ANYI GUDUN GARA 23-24

254 18 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


*NA*
*AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 23-24*

_____________________________

Har ummee ta tambaye sa lafiya yace ba komai , tashi yayi ya hau sama ya dauro Alwala yana saukowa Farouk na shigowa gidan ,shi ma da sauri yayi Alwalar yabi bayan mahaifinsa, tare suka fito daga masallacin suka shigo gida tare , duk falo suka zauna suna tattaunawa akan wani business da Abba ke so farouk ya fara bayan sun gama tattaunawa ne ya gangaro akan maganar su 'yar Kullum wato zancen aure

Take gumi ya fara karyowa Farouk har dai da yaji Abba na cewa "idan baka samu wadda tama a garinnan ba kawai ka shirya kaje zamfara se ka wuce maradun a can cikin dangi ka zabo wadda ta ma ka aura"

Shiru yayi se can yace "Abbah ai na samu anan"

"To, to Alhamdulillah 'yar wane gida ce?"
Cewar Abba

Se farouk yace "ai bamu gama fahimtar juna bane "

Gani yayi Abbah ya tashi ya haye sama ya barshi a nan falon
Take yaji gabanshi na faduwa saboda ya kula Abbah fushi yayi da shi, tunda har ya tashi ya barshi zaune,tsoron shi daya kar Abbah ya aura masa duk wadda ya samu
Se gumi ke karyo masa

Jiki ba kwari ya tashi ya nufi dakinshi
_____________________________

Su ummah nata shirye shiryen bikin Ramla Wanda yanzu sati biyu ya rage ayi bikin Amma a can kwankiyal za'ayi daurin auren Dan ko yini duk a can za'ayi tunda abun ya zama tuwona mai na

Ammah Anty Ramla a nan kano za'a kai ta ,duk sun bada dinkunan su na cin biki anan kaduna yau ma sun shirya ita da Amal zasu je kasuwa daga can se su je karbar dinkunan su

Sun shiga kasuwar sunyo siyayyar da za suyi sun fito, se suka wuce shagon dinkin, da yake yana kusa da kasuwar ne

Sun shiga sun karbo suka fito , suka tsaya akan titin suna jiran abun hawa se ga wata mota tazo ta faka kusa da su mutumen ciki ne ya fito ya nufo su
Ai ko suna hada ido da Amal ta koma bayan Ramla ta rike Mata hannu ta dukar da Kai

Da murmushi akan fuskar shi ya karaso suka gai sa da Ramla ,se na ga ashe malamin makarantar su ne Dan bautar kasa

Yace "Amal Ina wuni"
Duk se taji kunya ganin ko gaida shi bata yi ba tace "malam Ina wuni "
Ya Amsa da "lafiya lau"

Ramla har ta tare Adaidaita ya ce mutumin ya wucewar sa yace ma Ramla "Aunty dan Allah zo na mayar daku gida"
Ya wani marairaice fuska kamar karamin yaro nason kuka

Ramla ita abun nashi dariya ya bata
Sannan ganin yadda Amal Tasha jinin jikinta ,dakuma malam din da tace ya tabbatar Mata da malamin su ne tace to mungode fa

Shi ya daukar Mata wasu ledojin suka isa yasa a mota baya Ramla ta bude ta shiga Tana kokarin rufewa Amal ta fada da sauri
Girgiza Kai kawai yayi danshi yanzu yarinyar dariya take bashi

Tunda ya tare hafsa ya tambaye ta dalilin gudun da kawarta ke yi duk ta ganshi, tako fada mishi dalilin

Suna tafe a motar shiru se can ya ce ma Ramla "Aunty sunana Ahmad Hashim, malamin su Amal

Tace "Allah sarki"

Dai dai sun kawo wurin danja ta tsayar da su juyowar da Amal zata yi suka hada ido da farouk yana cikin uniform dinsa ,motar shi ta tsaya a gefen tasu

Ai ko zaro idonta Tana kallon sa , take ya Mata wani mugun kallo tuni jikinta ya fara rawa ta juya ta kankame Ramla da sauri Ramla ta dube ta ganin irin razanar da tayi tace"ke lafiya?"

Se tayi shiru juyawa Ramla tayi ta kalli gefen da Amal din take dai dai an saki danja motoci duk suka fara tafiya ,ita dai bata ga komai ba ,girgiza Kai kawai tayi bata ce Mata komai ba har suka karaso

Aiko kamar jira take yayi parking ko takan kayansu bata yi ba ta tashi ta bude motar tayi cikin gida se dai shi Ahmad din ne ya fito ya taimaka ma aunty Ramla da fitowa da kayan nasu

Ramla nata zuba godiya har sunyi sallama ta juya zata shiga gida yace
"Am anty Ina da magana"

Dawo wa tayi Tana kallon sa ,Dan sosa Kai yayi sannan yace"bazan boye Miki ba tun ranar Dana fara ganin Amal Allah ya Dora min sonta kuma ni da gaske nake aurenta nake son yi se dai taki bani damar magana da ita ma , duk ta gani se gudu shiyasa nayi tunanin fada Miki ko Zaki taimaka min ki shawo kanta"

Shiru Ramla tayi Tana nazari se can tace"Malam Ahmad kayi hakuri kaga Amal yarinya ce ,ba yanzu za'a Mata aure ba sannan gidanmu ma ba'a barin mu fira ,da nace kafara zuwa, sannan Amal nasan yanzu samari basu ne a gabanta ba se dai karatu ,Ammah dai zanyi kokarin ganin ko gaisuwa ce ku na danyi "

Murmushi yayi yace nagode da kika fahimce ni kuma naji dadin bayanin da kika min..............✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now