ANYI GUDUN GARA 53-54

309 24 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)




*PG 53-54*


________________________________

Sannan ya dawo hayyacinsa, juyowa yayi Yana kallonsa
Shima kallon sa yake kafin yace "Nas Wai me kake kallo Ina ta magana kayi shiru, murmushi yayi yace masa "ba komai"

Yasmin janta tayi suka samu kujeri suka zauna ba jimawa aka tashi walimar janta tayi suka shiga cikin gidan nasu

Tunda Akayi Addu'a,Nasir yake baza Ido yaga ta inda Amal zata bullo masa be gani ba ,tuno cewa yaga Yasmin ta tarbeta ya tabbatar masa da kawarta ce Dan haka a gaggauce ya sallami Abokansa Yana fatan Allah yasa Amal Bata wuce ba

Suna shiga cikin gidan dakin Yasmin suka shiga Nan Amal ta dauko kyautar da ta sawo ta Bata Nan ta shiga yi Mata godiya,taji dadi sosai da kyautar kawar tata,Abinci da snacks ta kawo Mata ,duk da tace ta koshi Ammah se da Yasmin ta matsa Mata Akan se taci,
Kadan ta tsakura ,se ga Kiran Al'amin ya shigo wayarta,dagawa tayi yace Mata Yana waje

Nan take Yasmin tace ta bari tazo dakin mahaifiyar ta taje ta hado Mata kayan walima har jaka biyu,ta Bata tace daya na Yaya Al'amin ne godiya ta Mata suka fito tare

Sun fito filin gate din kenan Nasir ya hango su da sauri ya karaso wurin Yasmin Tayi saurin cewa "Amal ga yayana ,yaya Nasir shine ake ma walima Nan Amal ta gaidasa da masa fatan Alkhairi Akan karatunsa godiya ya Mata ,yace "ko wucewa Zaki yi?"

Tace  "eh"

"Ok bari na dauko mota na kaiki"

Ita dai Yasmin mamakin Yaya Nasir ya kamata ganin irin kallon Yasmin din da yake da Kuma cewar da yayi Bari yazo kaita shida keda Baki

Amal din ce tace"A'a Yaya anzo dauka ta ma "

Ta mishi sallama suka ci gaba da tafiya Ammah se da ya biyo bayansu suna fitowa Al'amin ne ya fito yana cewa

"Da yanzu Zan sake kiranki naji ki shiru"
Murmushi ta masa tace "ka ga wadda ta tsaidani Nan "
Tana nuna Yasmin

Se yanzu Al'amin ya kula da Nasir ma ,gaisawa suka yi suka musu sallama

Suka shiga mota suka nufi gida

Suna wucewa Nasir ke cema Yasmin
"Wanene yazo daukarta?"

"Yayanta ne"
Ta bashi Amsa
Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi gida ita ko se mamakin sa take can Kuma tayi murmushi ta juya cikin gida

Ana magariba suka Isa gida Al'amin massalaci ya wuce ita Kuma ta shiga gida,Tana shiga Bata isko ummee falon ba,aje kayan walimar tayi a kujera ta shiga cikin dakinta sallah tayi bayan ta gama ,ta dauko wayarta data manta da ita a gida Miss call biyar taga an mata da wata number ta kasashen waje Nan tayi tunanin ko farouk ne ,Dan haka se ta sake kiransa ba'a daga ba har ta tsinke ,jiki a sanyaye ta aje wayar ta cire hijabi kenan taji karar wayar ,dauka tayi ta zauna bakin gado ta daga wayar tace"Assalamu Alaikum"

Daga dayan bangaren ya Amsa murya a cunkushe zata gaida sa katseta yayi da cewa

"kina Ina ,Ina ta Kira Baki dauka"

Cewa tayi "bani Nan na je wurin walima"

"Kin fita da izinin wa kenan" yace

Shiru tayi ta rasa abun cewa se can tace "na fadawa ummee"

"Ni me yasa Baki kirani kin fada min ba,wato yawo kike zuwa ko?"

Shiru tayi jin fadan da ya soma Mata kafin tace "yi hakuri"

Kit taji ya kashe wayarsa ,shiru tayi Tana kallon wayar kamar zata ganshi a ciki,to ita Bata ga abun fada anan ba ,da har yake ta fada a waya,da yake cewa yawo take zuwa ai ba ta ma zuwa ko Ina da ya wuce makaranta ko gidansu ba ta je ba tunda ya tafi

To ita gaskiya Bata son a ta Mata fada barin ma nashi da bayada dalili ,bangarar da wayar tayi ta tashi ta fita daga dakin zuwa falo

A  haka Rayuwa ta ci gaba da tafiya Wanda a yanzu idan ba ka ma Amal farin sani ba ,ka ganta a yanzu bazaka gane ta ba ,komai nata ya canja tunda daga cikar data Kara da Kuma dabi'u da yawa da ta canja, sannan ga ilimin boko da ya ratsata,

Ummee har wurin koyon kwalliyar zamani da girki ta sakata ,yanzu Amal anzama irin 'yan matannan da ake Kira first class ita kanta ummee a yanzu ta tabbatar da danta ba karamin Dace yayi ba.


A bangaren farouk kuwa watanni takwas da ze yi a Cairo gani yake kamar shekara takwas ze yi , ba karamin kewar gida yayi ba mussaman matar sa Amal da yake kwana da ita a Ranshi duk da har yanzu ba wata wayar kirki suke yi ba , sannan Babu wani sabon Abu a tsakanin su

So tari Amal takan danyi tunanin farouk a ranta kadan ba sosai ba ,saboda har yanzu maganar da yayi da ze tafi Bata bace Mata akai ba, A yanzu ma yadda take ji ko ya dawo duk zaman da yake so suyi shi zasu yi ,saboda Amal din da ya sani da ba ita ce a yanzu ba

A yanzu haka jarrabawar kare secondary suke ita da kawarta Yasmin ,se dai har yanzu bata fadawa Yasmin cewar Tana da aure ba,ga Kuma Yaya Nasir da ya taso ta a gaba duk ya ganta ,ze ci gaba da kallonta ne har ta bace duk da be fadi ba ,ita tagano kamar sonta yake Dan haka ta rage zuwa gidansu Yasmin din sosai .

Ba dadewa suka gama jarabawar su ,sati daya tsakani aka bugo waya anty Ramla ta haihu ,Dan Alokacin tafiyar farouk wata takwas cif se dai har lokacin be dawo ba

Nan Amal ta shiga dokin haihuwar Anty Ramla,Rana daya suka shirya ita da ummee suka je kano ,Al'amin ne ya kaisu, ummee dai ta dawo Amal Kam kirjin biki se anyi suna zata dawo

Al'amin nata tsokanar ta Yana cewa"ummee kice ta dauko mayafinta ta mu wuce gida"

Amal se marairaice wa take , ummee dai murmushi tayi tace ma Al'amin "naki na ce din ka wuce mu tafi kar muyi dare a hanya "

Fita sukayi Amal ta rakosu har wurin mota Tana ta ma ummee godiya,har se data ga tafiyar su

Koda ta dawo gida Anty Ramla kallonta tayi tace "kanwata miye sirrin kodai soja yayi ajiya ne"

Rufe fuska tayi

Ramla dariya tayi kafin tace "Amal gaskiya ummee mutumiyar kirki ce Kinga abun arzikin data kawo ma baby Tana nuna wata jaka cike da kayan baby data kawo

Amal cewa tayi "ai Anty banta ba ganin mace me mutunci irin ummee ba Nan ta shiga Bata labarin irin yadda take kula da ita ,da abubuwa da yawa data ke koya Mata kamar ba surukar ta ba

Nan Anty Ramla ta shiga sa ma  ummee Albarka Nan take cewa"yaushe mijin naki ze dawo?"

Tabe Baki tayi tace "nima ban sani ba"

Wani mugun kallo Ramla ke bin Amal din dashi kafin tace "Baki sani ba fa kika ce?"

"Eh " tace ,tashi ma tayi ta bar Ramla sake da Baki Tana kallonta har ta shiga bedroom dinta

A haka sukayi kwana biyu ana jego ,baby Masha'Allah dashi yaron duk Yaya Sadiq ya biyo ,Ramla na ta son su kebi tayi magana da Amal din Dan ta kula yanzu kanta har wani rawa yake Mata,se dai Baki da akeyi a gidan akai akai ke hanata mata magana

Wata tsohuwa ummansu Sadiq ta turo ita ke kula da Anty Ramla,husna ma tuni ta dawo gidan da zama

Ana saura kwana ukku biki suka je kasuwa suka sayo Abubuwan da za'a ba 'yan biki daga Nan Amal ta bayar da wani dinkin lace dinta da zata saka ranar biki

Tafe yake Akan matattakalar jirgi Yana saukowa se da ya sauko ya ja numfashi Yana shakar iskar kasarsa ,ji yake kamar yayi wasu shekaru ba'a Nigeria ba,ya Kara wani irin kyau na mussaman fatar Nan har wani sheki take.............✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now