ANYI GUDUN GARA 43-44

283 16 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*

'''Follow me on #wattpad @Ayshagaladima666'''



_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

'''Ban manta daku Ba'''

*JATTAKO NOVELS GROUP 2*

*ALHUBBUL AAMAH FANS GROUP*

'''comments din ku na sani nishadi'''


*PG43-44*

____________________________

Daga wa tayi cikin zumudi se taji muryar yaya Sadiq ce gaisawa sukayi har Yana tsokanarta Yana cewa"kanwata ya Amarci?"

Rufe Ido tayi kamar Yana ganin ta tace "Yaya bana so"

Dariya yayi ya  Mika ma Ramla wayar da kamar ta kwato a hannunsa tunda taji Amal ce ta dauki wayar,ai ko Tana karba ta barshi Nan tsaye ta  nufi bedroom,kallonta kawai yayi ya girgiza Kai ya nemi daya daga cikin kujerin falon ya zauna.

Tana shiga dakin ta Kara wayar a kunnenta tace "Amal"
Daga can bangaren tace "Aunty Ramla ya kike nayi kewar ki" se kuka ta sakar Mata ,daurewa kawai Ramla tayi itama ,saboda tayi kewar kanwarta ga Kuma auren da aka Mata na bazata

Da taji batada niyar yin shiru tace"Kinga in kuka Zaki yi bari na kashe wayar"

Ai da sauri tace "na Dena " Nan suka gaisa ,  Amal tace "Aunty kin San Wai mijin da aka aura min sojane?"
"Eh na sani ,Kinga yadda Allah ya kaddara Miki ko shiyasa ko yaushe nake fada Miki ki fidda wannan shirmen da kike na kin masu kaki,gashi yanzu da ubangiji ya tashi se y hada ki da shi"
Kuka Amal din ta fara ,se kuma taji ta bata tausayi ita tasan wacece Amal

Sauke ajiyar zuciya tayi tace"yanzu abunda nake so dake ki kwantar da hankalinki Kuma ki cire ma kanki tsoron da kika saka ,duk kin kayi sallah kiyi Addu'a Allah ya cire Miki wannan tsoron,Dan in ya San kina wannan shirmen ban San me ze faru ba"

Se kuma tayi shiru taga Tana Shirin ballo wasu ruwan,karku manta Ramla tasan farouk ne ya taba Marin Amal,sannan har gaida shi tayi kwanaki ya share ta

Amal ta katse Mata tunani da tace "Aunty yace se ya harbeni da bindiga ma " Tana me ci gaba da sheshekar kukanta

Har se da Ramla ta katseta da cewa "me kika masa ne?"

Nan ta kwashe yadda suka yi ta fada Mata,ai ko Ramla dariya kamar ta karta ,shiru kawai tayi Dan kar Amal din taji haushi

Nan dai ta bata shawarwari masu matukar Amfani ,sannan tace duk abunda farouk din ya sata ta dinga masa,sannan tace ta diba Jakarta da ta ratayo Ashe kowacensu ciki aka saka Mata sadakinta,tace tayi kokari tayi waya yadda zasu dinga magana tace to Aunty nagode sukayi sallama

Tana son ta fita ta bashi wayarsa Tana tsoro,Kiran wayar Akayi taga ansa kakus akan wayar ba shiri ta fito falon Yana zaune Yana cin Abinci a take away kasa Akan carpet karar wayarsa ya ji juyowa yayi  Yana kallon ta a darare ta iso ta Mika masa wayar karba yayi yace "zauna"

Daga wayar yayi ya Kara a kunne yayi sallama daga can bangaren aka amsa ,sannan taci gaba da cewa "Habubakar yanzu ka kyauta kenan daga aure har ka manta Dani ,duk da nima daga baya nasan da maganar auren,to yanzu dai gani na shirya kazo ka kawo Ni Naga Amarya"

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now