ANYI GUDUN GARA7&8

335 21 1
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️

*NA*

*AISHA GALADIMA*

*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*




*PG 7-8*

_______________________________________

Umma ce tace "yarinya kina da aiki babba a gabanki kuwa"

Abba ne yace"nifa lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro, irin wannan tsoron Dan sanda da take yayi yawa fa"

"Ai kuwa dama ta bari ,saboda auren ta da sadiq tamkar anyi an gama ne, tunda kasan alkawarin da kayi da yaya lawal"

Abba shiru yayi be sake cewa komai ba yace "bari na koma kasuwa"

"Allah ya kiyaye" cewar ummah

Ya tashi ya wuce ummah kitchen ta wucewar ta

Ramla dakin nasu ta shiga har lokacin Amal kuka take se taji duk jikinta yayi sanyi Tana tausayin 'yar uwarta ,ta kuma ji firar da su Abba suka yi, tasan duk Amal taji labarin cewar zata auri yaya Sadiq, Allah dai yasan halin da zata shiga

Matsawa tayi kusa da'ita ta dago kanta ,ta sa hannu Tana goge mata hawayen da take yi.

"Haba lovely sis miye abun kuka da zaki zauna kina ta kuka irin haka, ai se ki janyowa kanki rashin lafiya"
Fadar Ramla

Ajiyar zuciya Amal ta sauke ta kalli 'yar uwar ta da idanun ta da sukayi jajir saboda kuka , tace
"Aunty kinsan fa bani son Dan sanda fa da masu bindigogi ,Amma shine su Abba zasu gayyatosu suzo gidan nan Allah dai yasan wadanda ze kashe idan yazo gidan nan ni na tsane shi tun kafin yazo gidannan, dama ya mutu a hanyar zuwa

Da sauri Ramla ta rufe mata Baki Tana fadar"Amal Ashe Baki da hankali yaya Sadiq din kike ma fatan mutuwa, Dan gidan kawu lawal ne fa na kano Wanda yake muna aikan kaya na sallah ko Azumi ,koma ba su ba har kayan kwaliyya da kyalekyali haka yake aiko Mana da su fa ,yaya Sadiq kuma shine babban yaronsa fa kuma shine yayan husna fa kike so ya mutu?"

Se Amal tayi kwalkwal da idanu tace " to wa yace shi ya zama Dan sanda?"

"To ba aikin sa bane, sannan ba su kashe mutane kamar yadda kike tunani fa se masu laifi suke kamawa
Dauke labulan dakin akayi "wake kashe mutane?"
Duk suka zare idanuwa 😳
Ummah ce ta dago labulen ,da sauri Ramla tace "labarin wani film muke "

se tace"to ku tashi ga Kiran sallar Azahar can Ana yi kuyi sallah"

Duk suka Mike suka fita

________________________________________

Se dare wurin dinner ya hadu da Abban nasa bayan sun kammala dinner ne yace yana da magana da shi, tsam ya Mike ya nufi dakinsa , shima farouk biyar bayansa yayi zuwa dakin
Da sallama ya shiga ya nemi kasan carpet ya zauna
Se da Abba yayi gyaran murya ya fara da "babana na Kira ka ne saboda akwai muhimmiyar da nake so nayi da kai, farouk ya Kara sunar da kansa kasa, " Alhamdulillah duk abunda uwaye ya ka mata Suma 'ya'yan su duk na maka, har an kai matsayin da ka mallaki duk abubuwan da ya kamata se dai Abu daya da har yanzu Banga Alamar kana da niyyar yi ba, shine aure tun Ina ma mahaifiyar ka magana akan ko taji kana zancen se ta cemin A'a , Dan haka Naga ya kamata nama magana da Kaina naji ta bakin ka"

Farouk ya dau kusan sakan 10 be ce komi ba se can yace " Abba Insha'Allah na kusa yi"

"Ka kusa yi yaushe?"
Cewar Abba
"Bada jimawa ba "
Farouk ya bashi Amsa

"To yayi zan ci gaba da tsumayen amsar taka , to ya wurin aikin naka ba dai wata matsala ko?"

"Eh Abba ba matsalar komai"
"To yayi Allah ya maka Albarka ta shi kaje"

"Amin nagode Abba"

Ya sa kai ya fita direct dakinsa ya wuce ya na shiga ya wuce bathroom se da ya watsa ruwa ya fito , ya sanya kayan Shan iska ya zube akan gado yana tunanin maganar da Abba ya mai ta aure

Tunani yake shi da ko budurwa ba yada ake ma zancan aure ba Wai beda 'yan mata masu hauka akansa ba , kawai dai wadda yake so ne be da ita a yanzu,

Kuma yasan halin mahaifin nasa tsayayyan mutum ne tunda har yayi masa maganar ya na nufin auren yake so yayi ,kuma matukar yayi wasa shi me iya aura masa duk wadda ta masa zeyi. Addu'arsa daya Allah ya taimake sa cikin masu son nashi ya bincika ko ze daidai ta da daya daga ciki kafin a masa auren dole😀😀

________________________________________

Tun safe ummah ta tashi ta tashi su Ramla su rika mata wasu kana nan ayyuka ita kuma ta shiga kitchen ta fara daura girkin tarbar Baki se kusan Sha daya na safe aka kammala komai har tsaftace gidan da komai , umma tace to kuje kuyi wanka ki shirya kafin su iso

Dakin su suka shige ,Ramla ta tube ta shiga wankan Amal kam zubewa tayi kan gado Tana fadar "wash! Allah duk bayana ciwo ma yake min duk na gaji tun safe mutum na tsaye "ta murguda Baki

Nace Koda ita da wa😃

Se kuma gabanta ya fadi da ta tuna bakin da za su zo
Fatan ta daya Allah yasa kar yaya Sadiq din ya biyo su
Tana nan kwance Ramla ta fito ita ma tashi tayi ta shiga wankan Tana fitowa ta tarar da Ramla har ta kimtsa ta sa Atamfar ta kallon ta tayi tace "Aunty Ramla kinyi kyau Masha'Allah"
Murmushi ta mata tace "na kai ki kyau autar Abba"
Ita ma dariya tayi tace "ai ban kai ki ba"
Tace "to naji yi sauri ki shirya bari naje waje "ok kawai ta ce mata
Zaunawa tayi kan stool din mirror na dakin tayi 'yan shafe shafen ta ,light make up tayi ta dauko wata doguwar rigar material Baki ta saka ,
Masha'Allah ta yi kyau sosai 👌🏻

Amal fara ce kyakyawar gaske duk mahaifiyar ta biyo kasancewar ta bafulatanar asali, ta na da dogon hanci da idanuwanta kamar na kyanwa da Dan karamin bakinta ,lips dinta sun kasance jajir da su , doguwa ce marar kiba , yanayin jikinta yanayin na fulani, se dai Allah ya hore mata manya manyan dukiyar fulani duk shekarun 16 idan ka dubi yana yin jikin se a dauka 'yar 20years ce
ba ta da kiba sosai , se dai baza'a kirata siririya Kai tsaye ba ,so tari idan bata buda Baki tayi magana ba wasu daukar suke bata jin hausa wannan kenan

Ita ma fitar tayi ta tarar Abba shima ya dawo an shimfida tabarma a tsakar gidan nasu da yayi fes da shi ta zauna itama

Tsayuwar motar da suka ji ne yasa su kayi shiru daga firar da suke , sallamar ummah ce da husna yasa da gudu su Ramla suka je suka rungume su , Suma se murmushi suke saki duk suka nufi tabarmar suka zauna ana ta gaisawa, har da kawu lawan aka zo Ruwa su Ramla suka fara gabatar musu

Abba ne yace "Ina dandana ban gan sa ba shi"?

Ai ko Amal ta yamutsa fuska

Kawu lawan yace"tare muke ai shi ya aje mu ya juya akwai wani meeting na 'yan sanda da suke da a garin nan yau shiyasa ai kaga munzo da wuri, yace da sun gama ze karaso nan"

Abba murmushi yayi yace "Allah sarki sadiq ba dai kokarin aiki ba, to Allah ya kawo shi lafiya"
Duk suka ce Ameen Amma banda Amal da Tasha jinin jikinta

Abinci suka ci duk suka gabatar da sallar Azahar sannan suka sake. Zama suna hirar yaushe gamo

Abba ne ya yafito Ramla da hannu tazo yace "je ki sake gyara dakinnan na zaure a can yayanku ze sauka har abinci nai da komai ku Kai masa kafin ya iso "

Tace to taja su Amal suka tayata daukar kwanukan abinci

Koda biyu na Rana tayi duk sun gama gyaran dakin se tashin kamshi yake
Suka juyo cikin gidan
Suna shigowa ummah na fitowa daga cikin da spoons da suka manta Amal ce gefenta ta Mika mata tace "ungo tai kikai kun manta da wannan ta wuce

Dan Jim Amal tayi ta na Dan kunkunin ta cikin Rai

Takun da ta jiyo daga zauren ne yasa ta dakata bata tafi fa ta tsaya gefen kitchen din

Yana tafe cikin takunsa na jaruman maza ya na sanye cikin uniform dinsa da suka masa matukar kyau yana rike da bindigar sa irin wadda suke ratayawa a kafada ya shigo da sallamarsa

Dago kan da Amal tayi caraf idanunsu suka sarke da juna wata irin kuwa ta kwalla!!! Tana zare ido da sauri uwayen suka taso suna nufo hanyar

Se nuna sa da hannu take Tana hawaye!
Shi kam mamakinta ne ya kamashi se ya fara takowa kusa da ita
Ai kuwa ta lumshe. ido ta zube a wurin.........................

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now