Two... Farkon Labarin

9.8K 477 21
                                    


Assallamu Alaikum,'Yan Gidan Gwaiba is a story which has 50% reality of our day to day activities and 50% of fiction to make it more elaborate, interesting and fun, also not forgetting the educational aspect of it.
Please any resemblance to you, your household or your community is an honest coincidence. Allah ya bani ikon gamawa lafiya... Amin summa amin. #YGG

Kaduna......

Gwaiba Manor (Gidan Baffa Yusuf)

Nuwairah...

Today is just like any other day, karar alarm ɗina ya tadani karfe biyar daidai kamar yadda ya saba. Ban tashiba illa mistike idanuna tareda addu'an tashi daga barci.
Wani matsananci faɗuwar gaba na tashi dashi gashi kuma ya haddasa min ciwon kai, koda yake tun shigowar makon nan nake samun haka amma na yau yafi kowane rana. Na rasa inda zan saisaita tunanina na gane ainihin abinda ya sani haka.
Though abubuwa sunyi min yawa amma ina kyautata zaton baifi gama jarabawa na makaranta da zamuyi yau ba, sai kuma Doctor da zani wajen sa. Gashi kuma Baffa yace zamu fara aiki gadan gadan tunda mun gama school.

Saidai na tabbata zuwa wajen Doctor ne ke saka min wannan tashin hankalin followed by fara aiki wajen Baffa tareda Nawwarah. Cikin School babu wanda ya damu dani, kwata kwata banida k'awa ko k'wara ɗaya. Idan mutum yayi min magana ko murmushi toh lallai note ɗina zai ara Kokuma zan tayashi da assignments.
Makarantar mu na Désolé International University dake jihar Kaduna. Makarantan Wani ne daga France dayayi haɗaka da Mike Adenuga, ana koyarwa da turanci da kuma harshen French. Yaran masu hannu da shuni ke cikin makaranta so babu wanda ya lura cewa Babana ne Alhaji Yusuf Gwaiba.
Koda yake baza'a lura ba saboda yanda nake dressing, kullum ina cikin manya manyan kimono tareda kwabɗa kwanɗan tabaru na medicated a fuskana. Ga kuma karafai akan hakora na watau braces.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now