Seven

5K 336 12
                                    

A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, su Nuwairah da Nawwarah suna aiki kullum babu fashi.
     Husna ma haka, kullum tana makale da Nuwairah wajen ta rage mata hanya tunda Nawwarah bata sake mata sosai ba, saidai kuma idan zata dawo Ashafa ke maidata gida.
    Shima ba gida suke zuwa direct ba, sai sunyi yawo cikin gari anci banza kamarsu kaji, shawarma, ice cream dasu pizza kafin dab da magrib ya maidata gida.
    Ya riga yace mata shifa santa yakeyi kuma babu maganar wasa a ciki, ita kuma a dadinta saboda wannan shine “Maraba gasarshe wai kura taga bak’ar jaki”
     Ta faɗa mashi kanin mahaifinta shine Alhaji Yusuf Gwaiba, shi kuma yaji dadin abin sosai saboda koba komai yanzu kwarya zata bi kwarya ne ba kaman yanda yake tsammanin kwarya zatabi akushi ba.
      Soyayya ya fara shiga cikin zukatan su, saidai kuma cikin kankanin lokacin ta fara nuna masa halinta kaɗan kaɗan kamar su banida kati turo min, kokuma yunwa nakeji muje ka kaini naci abinci.
      Shifa bai ɗauki abin da wani zuciya daban ba, yasani cewa a matsayinshi na namiji dole ya ɗauke ma budurwasa abubuwa kamar haka. Tunda ance ‘Any soup where sweet na money kill am’
        
   Shikuma Nawaz bashida aiki daya wuce na kallon Mermer, sau da dama tana kamashi kuma tayi masa magana irin na marasa kunya ‘Mallam lafia kake kallona?’ Kokuma ‘Ya da kallon kamar kaga abin tsoro’
     Dariya yakeyi sosai saboda duk abinda zatayi mashi bazai karya mashi zuciya akan kallonta dayake ba ko kuma neman abinda zai haɗashi da ita.
     Nawaz irin mutanen nanne da abin duniya bai damesu ba, baya daukar wani abu na yayee. Shigarsa ya bambanta da irin maza na shekarunsa, dukda shekarunsa 31 a duniya amma salon shigarsa kamar ɗan shekara saba’in.
     Gashi kuma yana san saka hula koda yaushe, wata rana ya saka K’ube da suit, wata sa’in hana sallah kokuma hular cowboy irin na Goodluck.
     Kamar kullum yauma kallon Mermer yakeyi, shi kansa yasan cewa bai dace yayi hulda da ita ba, ta mashi fintinkau ta ko ina amma hakan baya hanashi abinda ya kulla ransa.
    Yasan cewa sarai wannan yarinyar ba irin yan matan gargajiya daya saba gani bane da zaiyi mu’amala dasu saboda kwata-kwata halayyarsu ta bambanta, thou bawai yayi mata wani sani ba bayan na office da suke haɗuwa.
    Haka ya gama kallonta san ranshi saiya yanke shawara yaje yayi mata magana, koba komai yasan matsayin sa.
     “Assallamu alaikum”
  “Waalaikumus salam”
   “Malama Mermer, zan iya zama?” ya tambaya yayin dayake janyo kujera.
   Bata kalleshiba saita soma magana, “Bawai kana tambaya na bane, kuma kamfani bana ubana ba balle na hanaka zama”
    Dariya yayi mai dan sauti saiya ce, “Sorry, ni ba wannan ya kawo ni wajenki ba”
     “please idan bai jibanci aiki ba, ina rokon ka akan karka faɗa min”
     “Gaskiya ba maganar aiki bane, kuma ni bazan iya hakura ba”
     Dagowa tayi ta kafa mashi ido, kallon kaskanci take mashi sama da kasa, “ok ina jinka, faɗa muji”
     Kasa magana yayi saboda yanda ta cika mashi ido, farad ɗaya ya soma ɓarin lebe kamar ma ya mance da abinda ya kawo shi. Inda inda ya soma saita bushe da dariya, ita karin kanta tasan cewa idan ta ruda mutum ne toh wannan karamin abu ne wajen ta.
      “Please ka tafi ka bani waje, ina aiki ne idan baka lura ba”
     “Shikenan bani lambar wayanki?”
    Kallonsa takeyi cikin mamaki, mika masa hannu tayi alamar ya bata wayanshi. Shima yayi mamakin abun saboda duk xatonsa zasuyi Jani in jaka.
    Wani tsohuwar BB ce Bold 2 yake amfani dashi,  bata amsa ba saboda wayar ya tsufa duk numbobin ya goge. Kuma tana tsoron kafin ɗan kankare ya kamata idan ta rike.   
     Jero masa number ɗinta tayi saiya rubuta da kansa, daga nan saiya kirata. “Toh gashi sai kiyi saving koh?” yace da fara’arsa.
     “Iska na wahalar da mai kayan kara” tace a fili.

******

  Jalaluddeen bashida wani aiki saina kiran Nawwarah, sam bata sake mashi fuska. Ita yanzu batada lokacin wani namiji sabida zasuyi distracting ɗinta akan main goal ɗinta. Watau nuna cewa tafi Nuwairah.
     Shikuma tun sanda ya ɗaura idonsa akanta ya susuce, sam ba ɗabi’arsa bane bibiyar mace. Dayake yanada bala’in kyau mata ke kawo kansu gareshi.
     Amma banda Nawwarah, attitude ɗinta yana bala’in bashi mamaki, kwata kwata baya gabanta ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin.
     Duk wani karamin lokacin daya samu yana kokarin kiranta ko yayi mata text. Sau da dama yakan kirata a Skype amma sau biyu ta dauka shima bata wuce minti goma sha biyar.
      Yaje gidansu sau biyu, na farkon taki fitowa wai ba tasan  zuwan bazata, idan zai zo wajenta ya rinka sanar da ita kafin ranar. Babu irin magiyan da baiyi ba amma ta kyale shi.
      Na biyun ne ya rinka rokonta kafin ta yardar mashi, haka shima yana zaune a falo an kawo mashi lemu basu wani daɗe ba ta tashi ta barshi wajen.
      Saida tayi taku kamar biyar haka saita juya tace masa sai anjima. Shidai kawai kallonta yakeyi, yasan cewa mai hak’uri zai dafa dutse kuma yasha romonta.
      Chan cikin zuciyar sa yana tunanin kila abinda yake ma yana mata shike dawo masa ta wani ɓangaren tunda dama abinda kayi sai anyi maka.
  
Ita kuma Nuwairah yanzu ta fara gogewa, kwalliyarta yanzu ya rage bada takaici ba kamar da ba. Still takan saka manya manyan kaya amma yanzu tana haɗa colors suyi matching.
     Sannan tana saka takalma zafafa dukda basuda tsawo, kuma jakunkunarta abin kallo ne. Duk nata nada da bata dauka yanzu kasuwarsu sun iso kam.
     Gashi kullum da soyayyar Deenie take kwana tareda tashi dashi, tunaninsa takeyi babu kama hannun yaro, fatan ta kawai therapy session ɗinsu yakai ta ganshi ko zataji dama dama.
       Saidai kuma wannan halin nata yana nan babu inda yaje, satin gaba ɗaya tana kokarin gane dalilin dayasa take yi. Kawai abu ɗaya zata iya dangantawa dashi.
      Maybe Depression da yawan damuwa ke jawo mata, yanzu dai ta gane depression ne but menene ta saka cikin ranta haka?
       Ranar Thursday ana gobe zata koma wajen Dr Deenie, suna zaune a conference room ana Seminar akan wani sabon material da zasu rinka sarrafawa mai suna Scuba.
      Kowa ana zazzaune ana sauraro, bayan nan sai masu tambaya sukayi nasu, irin su Nuwairah, Nawaz, Momee etc.
        Itadai Nawwarah tayi jotting down komai kuma ta kunna recorder saboda kada komai ya ɓace mata, ita burinta baifi ta nuna cewa itace zakarar gwajin dafi cikin yan uwanta ba.
       Dama Nuwairah tana zaune gefen Mermer, ana lecture tanayi tana tunanin Deenie kawai saita lura da wani Tiara karami haka gefen Mermer data fito dashi daga Jakarta.
     Dama Mermer kan saka Tiara wata sa’in akan gyalenta, ita tanason abin a matsayinta na yar sarauta. To aciki ta fi san wannan saboda yanada rastin royal blue, silver metal sai kuma gold.
      Abin ya bala’in burge Nuwairah, a hankali ta rinka fakon idon mutane. Angama taro kowa ya tashi zai tafi sai tayi wuf ta dauke tareda turawa cikin jakarta. Dama yanzu ta kware sosai nan take saita dauke abinka a idon ka baka sani ba.
      Da sauri ta bar wajen, tana cikin tafiya sai Momee ta kirata a waya wai su hadu suyi lunch tare. Anan ta mance data dauki wani Tiara.
     Ita kuma Mermer bata tuna cewa Tiara ɗinta yana kan table ba, duk zatonta yana saman kanta. Hankali kwance ta tafi gida abinta.
      Saida ta kalle kanta a cikin mirror ɗin ɗakinta kafin taga wayam. Nan ta soma dube dube cikin jakarta amma babu shi babu dalilin sa.
      Da sauri ta koma wajen motarta ta yashe tas amma bata gani. Duk cikin Tiara ɗinta yafi tsada, mutane basu san cewa ba golden color bane face gold karin kanshi, sannan silver ɗin kuma azurfa ne.
      Nanfa ta birkace kamar bible ɗin Hausa, samun waje tayi gefen mirror tayi zaman dirshan. Shine abu na karshe da Mamanta ta siyan mata kafin rasuwar ta last year. Gashi tana bala’in sanshi.
      Yanda takesan abin dole a lura ya ɓace saboda flaunting ɗinsa anyhow data keyi. Kawai sai wani tunani ya faɗo mata akan mutanen office ɗinsu.
      Yanda Asma’ul Husna ke kallon abin har haushi taji, tanata yabonshi tana rikewa. “Tabbas ita ta dauka” wani zuciya ya raya saboda su Nuwairah sunada kudin siyan abinda sukaga dama.
     “Aiko zakici ubanki yar talakawa gobe idan Allah ya kaimu kuwa” ta faɗa a fili tareda mikewa, kawai tunanin irin rashin mutuncin da zata mata ne gobe idan Allah ya kaisu.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now