Thirty-seven

4.1K 277 27
                                    


    Zaria, Hanwa GRA.....

    Tana shiga ɗaki ta banko kofa, "Dam" kakeji mai karar gaske. Shikam har yanzu mamaki yakeyi wai Hunaisan daya sani ne take masa ɗiban albarka haka.

    Girgiza kansa yayi saiya wuce ɓangaren ɗakinsa, anan yayi wanka tareda alwala domin Asr ya danno kai. 'Kulululu' cikinsa ya soma kiran ciroma.
   Wani Navy color jallabiya ya zura saiya wuce kitchen, anan yaga komai a mazauninsa, abin kuwa ya bala'in burgeshi.

     Dayake ya iya abinci nan yayi blending kayan miya saiya soya, taliya yayi masu na jollof dinta dan su samu su ɓasga kafin yunwa ya rakasu lahira.

     Ya ɗaura a wuta kenan saiya wuce Masjid tunda har an tada Ikama, amma da yake tsallaken gidansu sai samu kafin ruku'u.

    Abinka da gas ashe ya cika wutan, ita kuma tazo kitchen domin ta dauki koda fruits ne takai bakin salatin ta, abinci ta gani a kan wuta yana barar raka.

   Ko kallon wajen batayi banda aikin gabanta, watau yanka su kankana da abarba, haka tayi tas zata wuce taji ya soma kamawa, ko ajikinta banda wani tafiya na tak'ama data keyi tana wani juya jiki kamar reshen bishiya.

        Koda ya dawo aguje harda tuntuɓe, k'auri konewa yayi masa marhaba tun daga gate, anan  yaga abinci ya k'one kurmus kitchen sai k'auri yakeyi.

    Dan ruɗewa hannunsa yasa dan ya sauke, anan kuma ya k'one hannu. Zafi mara misaltuwa yaji wanda saida ya huta tukun kafin ya nema tsumma ya sauke.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now