Five

5.1K 353 9
                                    

Murtala Mohammad Airport, Lagos....

      Asma’ul Husna ta gama duk wani clearance daya kamata tayi, kawai yanzu tana last check point ne sai kuma shiga jirgi.
      Sannu a hankali shima tayi wannan saita shiga cikin jirgi, ta samu kujera ta daidai window ta zauna. Sauran mutane anata shigowa kowa na  zama tareda ajiye kayansa a drowar sama.
      Fitsari na rashin dalili ya kamata, anan ta mike ta tafi bayin cikin jirgin domin ta kama ruwa.
        Shikuma yana shiga cikin jirgin yaga an kusa cikawa, duk guri mai kyau watau wajen window an cika. K’yallara idonsa yayi sai yaga chan baya akwai empty seat.
     Dadi yaji ya kamashi saboda da zaiyi tafiyan kunci zuwa Kaduna, dama duk a gajiye yake kasancewar yanzu ya gama more than 10hrs journey.
     Isarsa Nigeria kenan daga Los Angeles, shine ya shiga wani jirgi kuma zuwa Kaduna. Casual riga ce a jikinsa mara nauyi, an rubuta ‘Keep Off’ akai. Sannan sai ya saka sweatpants tareda bakin tennis shoes.
      Gashin kansa kaca kaca, kuma idanunsa sunyi ja tareda kanana alamar gajiya da barci. Basai ya faɗa maka ba amma kana kallonsa kasan he is not in the mood for drama.
      Ita kuma tana gama kama ruwa sai taji sa’ida, kara gyara make-up ɗinta tayi saita koma wajen zamanta.
     Cin karo tayi da mutum saboda a tare zasu shiga seat ɗin, shi ya ganta yasa yake kokarin rige rige da ita. Aiko nan ya tureta ya shige sannan ya zauna akan kujerar.
    “Meye haka? Kana tafiya baka kallon gabanka?”kallonta yayi yana dariya cikin ransa, sai kuma yace mata “Sorry”
   “Okay, but wajen zamana ka zauna”
   Kallon left and right yayi cikin isgili alamar baiga komai wajen da zai nuna mashi seat ɗinta ne ba. Saiya ɗaga kafada tareda dauko roban ruwa ya fara sha.
     “Kaifa nike jira” tace a kule
   “Me zan maki?” ya amsa
  “Tashi zakayi min daga kujera tunda na riga zuwa, besides daga hanyar bayi kaga na fito
    “Ga waje ki zauna mana, ko dole sai nan wajen? Sai kace tsafi?”
   “Eh”
   “Gaskiya saidai kiyi hakuri”
    Zatayi magana sai wata hostess tace mata ta zauna an kusa tashi, kuma tana tareda wata dattijiwan mata, dole Husna ta zauna kusuda gwaskar daya zauna mata kan kujera.
      “Welcome to Eric Airlines, it’s the boarding time for flight 284, heading to kaduna from Lagos, Captain Baffa Malami wishes you a splendid flight” akayi announcing cikin jirgin

       Ran Husna idan yayi dubu toh ya ɓaci, Allah Allah takeyi su isa Kaduna ta rabu dashi. Earpiece ɗinta ta dauko saita saka karatun Al Quran. Shikuma makwabcinta saiya soma barci wajen 25mins haka saiya farka.
     Ita ya fara kallo kuma sai suka haɗa ido. Nan take ta zabga mashi harara saita ɗauke kanta, buga Candy Crush takeyi ne kasancewar tana level 635.
       Murmushi yayi saiya dauki ruwa ya kara sha, a ranta addu’a takeyi ya tashi wai zashi kama ruwa, toh wallahi zata koma wajensa. Shima wayarsa da dauko yana buga candy crush ɗin.
      Yanayi yana leka wayarta, batace komai ba shi keta abinsa. Sannan sai juye juye yakeyi acting all clumsy, abin ya kaimata hakon wuyanta sosai amma tayi burus dashi. Daga bisani yayi ajiyar zuciya saiya ce, “Ahhh this is getting boring, nifa ban saba inje waje ba’a min magana ba”
     Banza dashi tayi kamar bata jiba, kara maimaitawa yayi but still. “Okay I’m sorry, kawai nafison zama wajen window ne” harda bazata amsa ba saita fasa.
      “Akwai wanda ke right mind ɗinsa da zaice baisan zama wajen window?”
    “Chill mana! Hak’uri fah nake baki shine kuma kike min masifa” ya faɗa cikin sigar shagwaɓa.
   Ya bata dariya sosai amma ta dake, bai kara kulata ba kuma abin yayi mata dadi.
     Sun isa garin Kaduna garin gwamna. Da sauri ta tashi ta tafi, harda dan ture ture ta haɗa dashi,  ga schoolbag, sannan ga karamin akwati sai wani leda.
    Kafin ya tattara harta bace masa, haka ya tafi bai masan sunarta ba balle yasan inda taje zama. Koba komai zasuyita zumunci.
     Tana chan tana kokarin tare taxi sai wani arniyar mota baka tinted ta danno kai, daidai gabanta akayi parking.
    Ana winning glass sai taga sokon da suka zauna tare, dama sunar data saka mashi kenan cikin ranta.
     “Haba tafiya babu sallama, ai ba haka rayuwa yake ba”yace da fara'arsa.
    “Okay bye” saita juya kanta.
   “I said im sorry, please Kiyi hakuri mana”ya faɗa kuma kana ganin Nadamar cikin idonsa.
    “Ba fushi nakeyi ba, bansan kaba so banga dalilin da zan tsaya zance dakai ba... Please bye”
    “Toh kizo muje na rage maki hanya atleast, koda Kawo ne”
   “No, zan shiga taxi har gida”
   “Shikenan muje har gidan naku toh”
    “Ah ahn... Nace bana so” ta faɗa da ɗan karfi.
    “Kinada tsiwa” yace a sanyaye, sannan sai kuma ya soma magana a hankali, “Ki fahimce ni, kawai ina so nayi making amends ne bawai wani abu.... Im deeply sorry for my actions”
     Shiru sukayi na wajen seconds 30,itace tayi magana. “okay fito ka dauki kayana, saita bar kayan wajen tareda zuwa ta ɗayen ɓangaren.
    Dariya yayi saiya fito, driver shima ya fito da sauri amma ya hanashi. Shiya kai boot saiya koma ciki ya zauna.
     “Wani unguwa kike?”
    “Geneva Close zamu”
   A hankali ya sake kallonta saboda yasan Geneva gida uku ke cikinsa, its either Yar Gidan Gwaiba ce Kokuma Yar tsohon shugaban kasa.
     Sun isa wajen sai yaga an rubuta Welcome to Gwaiba Manor. Ita kuma saita fito waje, shima haka domin tayata da kayanta.
     Dama cikin mota babu wanda yace komai, harta soma tafiya saita tsaya, juyawa tayi saita ce, “Thanks” daga nan saita wuce.
    Murmushi yayi tareda harde hannunsa biyu akan kirjinsa, kawai kallonta yakeyi. Zuwa tayi wajen gate sai wani computer ya kunnu  yana mata tambaya.
    Dama mai gadi ke controlling ɗinsa ta ciki, tafara  faɗin sunanta gate ya soma budewa da kanshi kasancewar electric ne.
     “Im ASHAFA SAMBO by the way” taji muryan guy ɗin yayinda take wucewa ciki. Daga masa hannu tayi alamar bye saita wuce.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now