Forty-two

5.1K 325 46
                                    


   Haka Hunaisa taketa kuka Hamza yana jinta amma bai tsaya ba, asalima sarsarfa ya haɗa dashi ya shiga cikin motarsa.
   Mudassir na daga tsaye! Baisan me yake feeling ba, ko takaici kokuma jindadi? Saidai kuma yanzu ya samu amsar abinda yaketa tambayar kansa.
   Yasan dalilin dayasa Hunaisa ke masa ɗiban albarka, ta kuma raina sa. Ba komai ke damunta ba illa abinda ke damunsa, watau abinda yasa yake hak'uri da duk wani abu datake masa.
    So ke ɗawainiya da ita kuma yayi mata mummunan kamu, ita kuma tashi tayi ta shiga ɗaki, shap ta mance da wani Mudassir na gefen, saida ya tafi hankalinta ya dawo jikinta.
   Gaskiya Hamza ya faɗa itama ta sani, Mudassir mutum ne! Kuma da gaske ne he deserves better, toh yanzu ya zatayi? A bakin kofa ta jingina tana shesheƙar kuka.
   Shi kuma Mudassir idan zaice ransa bai ɓaci ba sanadiyar abinda tace yayi karya, kawai dannewa yakeyi saboda Allah yana tareda mai haƙuri.
     A hankali ya bita zuwa ɗakinta, ya murɗa sai yaji a garƙe. Magana ya somayi ƙasa ƙasa, "Dan Allah Hunaisa ki buɗe ina so muyi magana ne" saida tayi jinkiri kafin ta baɗe.
   Idanta jazur kamar garwashin wuta, tana ma dafe da kanta a lokacin. Kallo ɗaya tayi masa saita matsa masa ya shiga ciki, ita kuma tana daga bakin kofa.
    Tun kafin yayi magana tayi maza tace, "I'm Sorry Ya Mudassir" shikam mamaki ya soma saboda baisan afuwan me take nema.
    "Idan bakya so ki zauna dani naji na yarda zan sauwake maki" yace A sanyaye.
    "Ba haka bane, dan Allah kayi hakuri. Bansan meke damuna ba, it's so complicated" ta karasa tana kuka.
   Tashi yayi yaje inda take ya soma petting mata baya, wanda yaune rana ta farko daya wuce arm length away. Bata hanashi ba saboda tana bukatar a bata hak'uri.
    "Banaso nayi kamada mara zuciya ko wani abu, amma idan kin bani dama zamu magance komai tare, ni da ke" ɗago kai tayi ta kafa mashi ido. Babu haufi Mudassir is too good for her, balle ma yanda ta rinka masa ɗiban albarka kala kala kwanan nan.
   Amma idan yace zai bata second chance zata karɓa da hannu biyu, itama zatayi fixing mistakes ɗinta kamar yanda Hamza yakeso yayi nasa.
    Kwantawa tayi akan kafaɗar Mudassir tana kuka mai tsuma rai, shikam aiki lallashi ya soma. Yanzu ya samu amsar dayake nema, kuma ya gane cewa Hamza ya tafi da Hunaisa, saidai mai tunda he has his gal back bygones is bygones.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now