Thirty-six

4K 272 35
                                    


    Kaduna, Umaru Gwandu Road....

  
     Saida Nawwarah tasha kukanta ma'ishi sannan ta mik'e tsaye, tunanin da suke fito mata sunfi dubu. Tama kasa saisaita tunaninta waje ɗaya balle ta gano bakin zaren. Komai yayi mata bakin kirin babu haske.

    A duniya ba'a taɓa raina mata wayyo ba kamar wannan! Koda yake chan kasan ranta tasan cewa laifinta ne. Tsanar datake ma Nuwairah shiya rufe mata kuma she wants to win ta kowane hali yasa batayi wani bincike kansa ba.

    Balle uwa uba ya fita daga gidan malamai, wannan perfect disguise ne mashi yanda babu mai zarginsa.

   Wani zuciya ya raya kawai ta rabu da Deenie tun kafin aje ko'ina, moreover ita yarinyar Billionaire ne kafin ta gama Idda maza zasuyi layin aurenta, aiko nan ta sake samun karfin gwiwa "Amma wannan karon da proper bincike" wani siririn murya ya faɗa.

     Ta yanke shawara dole tabar Deenie, because as the day goes by, their is more bad news wajensa maimakon good news. Tattara masa takardunsa tayi sannan ta gyara masa gadon kamar niyyarta na farko.

   Tanayi tana tunanin zuci, bawai rashin makaranta ke damunta ba. A'a, karyan daya shirga ma mutane ne abin haushi. Allah ya riga ya tsara duniya kuma ba kowa bane zaiyi karatun boko.

   Wasu kam sunyi kudi bata hanyar boko ba, mutane da dama sun samu arziki basuyi adabin bature ba. Kowa da hanyar abincinsa, wasu boko wasu kasuwanci.

    Saidai kuma wani hanzari ba gadu ba, wai fisabilillahi ace aikin asibiti shine yakeyi na bogi, salan yaje ya salwantar da rayuwar wani saboda ganganci.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now