Sixteen

7.4K 268 37
                                    

Jabi Road....
     Koda Mermer ta isa gida wajen tara da rabi na safe, Ado ya buɗe mata gate ta shiga ciki tayi Parking.
    Janyo akwatinta tayi, dama da kit ne dame bin masa, sannan kuma sai ledojin souvenirs. Tana tafe babu komai a ranta har takai wajen kofan shiga ciki.
     Ta saka hannu ta murɗa amma tajishi a garke, saita karayi kuma shima tajishi haka. Juyawa tayi ta kalle gefen da Ado yake, tana so tayi mashi alamar yazo tareda hannunta amma ta lura ya shafa’a yana sauraren Radio baima kallon inda take.
     Sai a lokacin ta kalle garage da kyau taga motar Daddy yana nan watau babu inda yaje, ajiye kayan hannunta tayi a bakin kofa saita tafi wajen da Ado yake.
    “Su Daddy basa nanne?” ta tambaya tanaso ta tabbatar, “Suna nan ranki ya daɗe” Ado ya amsa a ladabce.
      Nan fuskan Mermer ya canza kala, ‘Kenan Bilkisu da gaske takeyi akan rashin barin Daddy ya fita
    Da kyar ta iya juyawa ta koma bakin kofa, wannan karon bugawa takeyi kamar zata karya kofan amma babu wanda ya buɗe.
    Ita kuma Bilkisu sun gama breakfast da Daddy  suna hira sukaji bugun kofan Mermer, Daddy ya nuna alamar zai tashi yaje saita taɓe fuska, dole ya hakura ya zauna sukayi burus da Mermer.
      Daɗin abin akwai rear door ta kitchen, aiko cikin ikon Allah tana murdawa saiya buɗe, taji daɗi sosai saita koma ta wajan kofar falo ta kwaso kayanta ta shiga ciki.
      “Daddy ina kwana?” tace tareda rinsinawa, a zaune ta gansu kan three seater, Bilki ta mimike kafa yana matsa mata, ita kuma, ‘Wash washh wash’ take cewa tareda fikifiki da idanu alamar tana jin dadi.
      “Yauwa Yar albarka har kin dawo kenan?” Daddy ya amsa da fara’arsa. Bilki ce ta dago tana yatsina fuska tareda tabe baki.
       “Har kin dawo daga gidan magajiyan kenan, kostomomi nawa kika samu?” Mermer bata amsa taba illa wucewa daki abinta, ita kuma Bilki tayi tsaki saita cigaba da jindadin abinda Daddy ke mata.
    Bayan Mermer ta shiga daki ta ajiye kayanta, batama adana ba yadda ya dace saboda ganin Daddy a gida ya bala’in ɗaga mata hankali.
    Fita tayi ta koma falon, zuwa tayi dab da wajen da suke zaune. Dafa kujerar tayi saita soma magana, ita kuma Bilki mamaki takeyi akan zuwan Mermer wajen su.
    “Dan Allah Bilki meyesa bakiso Daddy yaje aiki? Kinsan cewa idan baijeba za’a iya korarsa koh? Kuma duka wannan kudin da kike ganin munada shi zai kare idan wasu baya shigowa” banza da ita Bilki tayi tana zumbura baki.
       “Yanzu me kike so ne ayi maki, fadan ki dani ne ba Daddy ba”
     “kwarai kuwa, yasa idan Kinaso ya fara zuwa aiki toh saidai ke ki bar naki” Bilki tace a fusace. Shi kuma Daddy yanata matsa mata kafa bai ce komai. Anty Bilki ta riga ta mayar dashi lusari, ya riga yanzu ya zama hoto ko mai aiki da remote.
     Mutumi dattijo mai kwarjini amma yanzu kamar soko yake, yaro ma yafishi kaifin tunani. Ita kuma Mermer wasu zafafan hawaye suka soma zuban mata.
    Cikin kuka tace, “Yanzu kina ganin abinda kikeyi Allah zai barki kenan, bamu zalunce kiba ko sau ɗaya amma kike mana haka”
      “Dalla Malama ki rufe min baki, kin tambaya abinda nake so kuma na faɗa maki” Anty tace tareda nuna mata hannu. Saida Mermer tayi dogon tunani kafin ta dago jajayen idonta kamar garwashi tace, “Shikenan bazan kara zuwa aiki ba, indai akan mahaifina ne, zan iya komai. Kuma inaso ki fada mashi cewa idan yaje yayi abinda ya dace”
    “Toh wannan kuma bai shafeki ba”
  Daga nan Mermer ta tashi tsaye, shafa bayan Daddy tayi cikin kulawa sai tayi masa murmushi. Shima ya mayar mata saita tafi. Kana ganin yanayin Daddy sai kaji tausayin shi ainun.
     Data koma daki kan gado ta faɗa saita ɗauki wani babin kukan, saida tayi ma ishi wanda barci ne ma yayi gaba da ita. Bata farka ba sai wajen 2pm.
     Bayi ta nufa tayi alwala, saida tayi nafila kafin tayi Zuhur, duka kuma idan tana sujjud tana rokon Allah akan mafita.
   Ita kuma Anty Bilki wajen sha biyun rana ta tashi, bayi ta wuce saita kama ruwa. Daga nan kuma sai tayi tsarkin gabanta a wani jan karamin baho kamar yanda takeyi kullum.
     “Tsanani” sunar malamin ta ko ace bokanta, shine ya faɗa mata kowane sha biyun rana tayi tsarki saita ba Daddy ruwan yasha, ko yana nan idan kuma baya nan saita ajiye masa. Toh ta haka ne zata mallake shi.
     Haka kuwa akayi, tanada jug ɗinta data ke juya ruwan saita saka a bedside fridge ɗin ɗakinta. Toh wannan ruwan Daddy kesha koda yaushe.
       Dama kafin ta samu ta shiga gidan saida ta tashi tsaye, tayi artabu sosai saboda Daddy shima a tsaye yake da addu’a, farcen Daddy akace ta samu, yadda kuma akayi ta samu shine ta biya wani mai gyaran farce akan ya rinka zuwa wajen Masallacin dake layinsu musamman da magrib.
     Kullum yana zuwa wajen, akwai masu yanke farce daga gefen wajen amma Daddy bai taɓa yiba, wani rana haka da tsautsayi ya gifta ya bada, toh mutumin bai zubar ba ya kaima Anty.
    Wannan abu anyi wata uku kafin akaci nasara, dama harda gashin kansa wanda bai mata wahala ba, a hairbrush dinsa tayi sanda dakinsa ta cire.
    Shidai boka Tsanani ya kasance kazamin boka, bazaka iya kallonsa sau biyu ba. Duk gashin fuska bursusu ga kuma jajayen hakora. Sannan dakinsa yana dankarin wari kamar akwai gawa a ciki. Ga kuma yanan giza gixai kamar zai taɓa maka kai, idan ma ka cika tsawo saika duka.
      Duk abinka baka iya hadiye miyau a ɗakin, gashi kuma ka rinka numfashi sama sama kenan kamar mai Asthma saboda ɗoyin wajen.
       A chan kauyen da Bilki tayi auren farko yake, kuma ya shahara sosai tunda yasan bakin aikinsa. dama shi ya taimaketa lokacin ta samu galaba wajen musguna ma kishiyoyinta.
   Bama cikin garin yakeba saika tafi chan k’urmusun jeji ka wuce wasu kuguna guda uku sannan zakaga wani bukka da akayi masa jan fenti.
     Idan mutum yaje kafin ya shiga ɗakin saika cire takalmi kafa ɗaya kamar yadda Manzon Allah SAW ya hana, sannan sai mutum ya ce, “Rahama ya nisance shi” toh daga nan Tsanani zai baka damar shiga.
    Idan ka kuskura kayi sallama saiya gotar maka da baki harka koma gida sai chan dare zaka dawo daidai, har kaje ka gama abinda yakai ka a tsorace zakayi. Idan dai kayi imani dashi toh fah aikinsa kamar yankan wuka yake... Wannan kenan!
     Da Mermer ta idar da sallah saita soma make up tunda wajen 3 za’a fara event ɗin Thou tasan cewa za’a yi African time yakai kusan biyar.
    Ankon French lace ne Turquoise blue tareda Peach head. Dinkin peplum gown tayi na Princess cut, kuma daga kasa wajen 15” yana shara kasa.
      Tayi kyau ainun abinta ta dauki peach clocth saita saka takalmi hills shima haka. Ta fito lokacin Bilki ta gama shan rake, wani kwarara gyatsa tayi ‘Gaaaa’zak gyama, gashi dukta bata ɗakin sannan kuma wani ya makale mata a hakora.
    Bakin ledar da aka siyo a ciki ta tsinka saita fara sakuce hakoranta dashi, koda Mermer ta ganta ta maza ta kawar da kai saboda kyama.
    “kizo kije ki wanke min kayan cikin da zanyi abinci” Anty tace ma Mermer. Ita kuma juyawa tayi tana kokarin tattara tunaninta waje ɗaya, halan Bilki bataga biki zata ba, bacin haka ma ai tanada mai aiki.
     “Bakiga biki nikeda shi bane?”
   “keya shafa, nidai kije ki wanke min kayan ciki”
    “Mai aikin ki fa?”
   “na aiketa kasuwa, inama ruwanki? Watau ban isa na sakaki aiki bane kome?”
     “Ni gaskiya biki zani” tace da sigar kuka.
   “Dan ubanki babu inda zaki yau sai kinyi abinda nace” Bilki tace saita dumfaro inda Mermer take. Cin kwallarta tayi ta soma fizganta gashi dama ginin kauye ce akwai karfi kamar namiji, ita kuma Mermer bataso tayi kokawa kafin kayanta ya barke.
    Bata saketa ba saida takaita bakin kitchen, “dan uwarki ki wanke min tas inba haka ba babu inda zaki.... Karamar karuwa kawai ko ubanki bai isa balle ke haihuwar titi”
  Kuka Mermer ta soma yi, haka ta dauko apron ta saka. Kayan cikin bata taɓa ganin irinsa ba, bala’in wari kana gani yafi awa uku a ajiye. Gashi kuma da uban yawa.
    Haka kitchen ɗin yaketa doyi, gashi ruwan naman sai tsalle yakeyi daya bayan daya yana taɓa mata jiki. Wajen 4:15 ta gama, dama taso tayi sallah a chan amma kawai  tayi abinta a gida tareda dauraye hannayenta da kyau.
     Aikuwa turare yayi aikinsa sabida karni kawai takeji yana tashi daga jikinta.
     Gwaiba Manor...

     Umma ta kira Husna tace mata Babanta ya samu mata miji, gabanta ya rinka faɗi saboda batasan kuma inda za’a jefata ba.
    Haka ta tashi ta tafi ɗakinta, kuka ta cigaba dashi wanda ya zame mata abinci na ranar, idanunta sunyi sumtuma suntuma jajazur. Har muryanta ya soma dishewa.
    Koda Nawwarah tazo dubata saita sanar da ita yadda ake ciki, fatan alheri kawai tayi mata saita koma ɗakinta. Yanzu hankalinta ya soma kwanciya kadan kadan tunda an samu tudun dafawa.
      Make up artist sunzo su chaba ma Husna kwalliya, tasha foundation sosai kamar ba ita ba.
     Purple lips akayi mata da smoky eyes, sannan gown ɗinta golden ne saita haɗa da golden veil. Gashi kuma yana jan kasa sosai saboda sai an dauka
     Tana sanye da dream gown ɗinta amma batasan wa zata aura ba. Komai ma a sanyaye takeyi kamar mara lafiya, idan ka ganta saita baka tausayi.
    Nuwairah itama tayi kyau sosai, make-up artist tayi mata kwalliya kuma ta fito matuka kamar ba ita ba.
   Dayake mother’s day ne babu Ango da ayarinsa, itama Husna taji daɗin ba event din da za’a mata kwakwafi bane akan inda angonta yaje.
    Hall din na Hamdala Hotel ya hadu iya haɗuwa, masu decorations sunyi namijin kokari. Peach da fari akayi amfani dashi a wajen sai kuma su Crystal masu kyau wanda aka jera a ceiling da kuma wanda aka haɗa da flower vessel.
    Abinci kuwa Buffet akayi na serve yourself, da za’a shigo aka saka wakar Nura Imam na ‘ Lokacin ki ne yayi amarya yar amana, toh kije zauna da miji aure ibada ne’nan hall aka soma tafi da ihu saboda kidan ya zauna. Nawwarah ce to soma shiga tana tafiya cikin kasaita, gashi kuma gira ya haɗe tamau.
     Sai ga Nuwairah itama ba tayan baya ba, sannan sai Mermer kafin Amarya, sauran kawayen daga bayan ta suke biye. Stevereinz ya soma sana’ar sa na daukar hoto.
   Idan kaga yadda mutane suka cika zaka sha bare ne ke wajen amma 75% Yan Gidan Gwaiba ne, kana ganin Husna kasan yar dangi ce kuma yar so babu abinda ta rasa(Ni kuma Ainau’n mama  nace sai wadatar zuci)
     Taro yayi taro anci, ansha, kuma an tika rawa, barnar naira da kuma haska hotuna, Husna ma ta dan saki jikinta kaɗan....
      Su kuma su Baffa bayan kowa ya tafi Mother’s day sai Alhaji Tahir Kurfi yazo.
    Magidanci ne mai kimanin shekara Arba’in da takwas, yanada madaidaicin tsawo da kuma jiki, ba baki bane amma kuma bashida wani haske.
    Hakoran sa guda biyu na sama dana kasa sun fita amma dayake ana zamanin cigaba yaje an masa na roba babu mai ganewa.
      Yanada Mata ɗaya Hajia Zainab, saidai kuma shekarunsa 21 da aure amma basuda yara. Babu Asibitin da ba’a jeba amma ɗa yaki zuwa, toh sun dangana sun mayar ma Allah komai.
       Alhaji Tahir Kurfi Kokuma ace Alhaji TK asalin bakatsine ne amma a kaduna suka tashi. Shi petroleum geologist ne kuma yanzu haka shine Shugaba a Mobil dake round about ɗin wajen Lugard hall na jihar Kaduna.
      Kuma gidansa bashida wani nisa da Lugard hall. Yazo ya zauna a falon Baffa anyi gaisuwan mutunci, Baffa da kansa yaje ya dauko masu ruwan sanyi tunda harda su Anty Madina akaje.
     Baffa ya dauki shi a matsayin Amini sabida kusan sa’ansa ne, amma dayake arziki na kara manyanta shi TK a matsayin uban gidansa yake kallonsa.
    Duk abinda Baffa yace yanayi saboda karamcin daya masa a da, Baffa ne ya cika masa kudin daya mallake gidan Mai ɗinsa.
    “Alhaji Tahir, kaga na sammace ka koh?”
     “ai babu damuwa” Alhaji TK ya amsa a ladabce.
    “Dan Allah alafrma nake nema wajenka, idan babu damuwa inaso ka auri yar wajen gidana nanda juma’a”
   Shiru Alhaji TK yayi na wasu dakikai kafin yace, “wacce Nuwairah ko Nawwarah?”
   Murmushi Baffa yayi saiya gyara zama, “Asmau yar wajen wana, ka ganshi nan”sai Baffa ya nuna Baban Husna. Murmushi Alhaji Tk yayi saiya sinna kai.
     “amma kasan dai akwai matsala a gidana koh?” yace a hankali. Baffa ne ya chapka, “Ai Allah ke bada haihuwa ba wani ba”
     “Toh shikenan na amince  Allah kuma ya sanya alheri”
   “Amin summa amin” Baba yace. Daga nan Baffa ya bada kudin sadakin Husna kuma aka gama wani magana na gyaran daki, lefe da sauran su. Within hours har sun mance da wani Ashafa, saidai Husna!

*****

Brooklyn, NY

Wanene Hamza Aliyu Kirya?

   Hamza ya kasance basakkwace ne, saidai kuma bai taɓa zuwa ba sanadiyar haka baisan kowa daga cikin danginsa ba ta uwa da kuma uba.
     Marigayi Barrister Aliyu Kirya SAN, shine ya haifeshi tareda elder sister ɗinsa Aisha wanda itama Barrister ce.
     A Lagos aka haifesu kuma anan duka sukayi karatu, zaune suke a Mushin wani shahararren anguwa a chan birnin ikko.
      Mahaifiyar Hamza ta rasu yana shekara uku kacal a duniya kuma lokacin Aisha tana shekara tara, koda mahaifinsu ya aura wasu matan babu wanda ta haihu, rashin jituwa ke shiga tsakanin su harya sake su.
    A koda yaushe idan suna wannan abu watau fada, Hamza ya kan shiga chan kuryan ɗaki yayita kuka, ‘Ni bazan taba aure ba saboda gaskiya ni bana son faɗa’ haka yake faɗi kullum tun yana shekara bakwai.
      Ba sai an faɗa ba amma hayaniya ba ɗabi’ansa bane, baya shiga cikin yara ayita wasan banza kamarsu boxing, wrestling, somersaulting da sauran wasan yara maza.
       Kullum yana bakin computer yanaso ya gano yadda ake amfani da wani abu abu Kokuma idan wani sabon Vedio game ya fito ya buga a Online. Shidai barshi a daki kullum.
      Aisha itace ta zame masa uwa, ta maye masa gurbin mahaifiyarsu da suka rasa wanda ba zai iya tuna wani abu daya shiga tsakanin suba saboda kuruciya.
      Koda yaushe takan faɗa mashi idan ya tashi aure ita zata zaɓan mashi fara, doguwa, mai gashi, wanda ta iya abinci etc da zai aura. Anan sai yayita dariya har ya mance da fadan gidansu.
        Tana cewa duk wanda zata aureshi saita kama kafa sosai wajenta Kokuma a fasa, Aisha ita ke jaddada masa cewa akwai true love a duniya ba kamar yadda mahaifinsu da sauran matansa keyi ba.
     Ita take faɗa mashi love comes in the most unexpected ways kuma sanda zai fara bama zai sani ba. Shidai yana shakkun haka yasa ya riga ya rufe zuciyarsa sannan dan mukullin ya wurga chan kasan teku.
     Aisha tana jaddada masa cewa komai lokaci ne kuma idan lokacin faruwan soyayyar sa yayi bama za’a ji bakinsa ba.
    Labarinsa ya faru lokacin yana shekara goma sha bakwai ne, kuma a lokacin Aisha tayi aure, itama barrister ce kuma ta aure barrister dan uwanta. Sunada yara biyu, suhail da suhaila. wata rana baban shi ya shiga haɗakan business da wasu mutane haka.
      Dama Lagos city dat never sleep ne kuma yana cike da yan damfara sosai musamman yan yahoo yahoo da sauran su.
    Ashe mutanen ma cuta ne, dama shi Babansu yana so yayi retire daga aikin gwamnati shine yake so ya fara business inda kudi zai rinka shigo masa.
    Ya saka miliyan Ashirin da biyar na kudinsa, to anan mutanen suka yashe shi tas. Dayake shi lawyer ne yasan amfanin barin evidence. To saiya fara processing yanda za’a kamasu. 
    Ya saka evidence a flash drive saiya ba ma mijin Aisha watau Mohd tunda office ɗinsu daya kuma ya aminta dashi. Yana cikin processing evidence sai yan damfara suka je gidansu suka kashe su tas. Daga Daddyn Hamza har matansa.
     Toh a lokacin Hamza yana boarding school, King’s College Lagos. Kuma suna SS3 lokacin ana Waec.
     Tashin hankali ba kaɗan ba Hamza ya shiga saboda rashin mahaifinsa, amma dole ya dauki dangana ya koma wajen Aisha. Sam basu kawo cewa masu damafara bane sukayi haka, duk zaton su random theft ne.
    Waec ya fito kuma Hamza ya fita da fying colours, A guda uku sai B sauran. Anan Aisha ta samo mashi addmision a Harvard domin ya karanta Soft ware Engineering. Toh dama ta bashi wasu takardu haka da flash dinda Daddy ya bata ya ajiye mata a chan saboda tsaro. Ko sau daya bai taɓa buɗe file ɗinba.
     Bayan tafiyansa da sati shida sai wanda suka kashe Daddy sukabi Aisha da mijinta suka kashe shima sabida sun lura har lokacin case din bai mutu ba.
     A hargitse Hamza ya dawo Nigeria, yaci kuka ya gode Allah. Toh yan fashin sunbi Hamza su kashe sabida basa son kowa daya san maganar ya rayu.
     Dama ana tara gagarumin case ne bana Daddy kawai ba har wajen mutane goma sha tara suma anyi masu haka. Kuma Daddy duk yabi ya samo su a matsayin shedu.
     Hamza yana gidan Aisha ya harde kafa da gwiwa yana kuka, yanzu bashida kowa a duniya. Sai wani mutumi yazo a matsayin private investigator.
    Wannan ne sanadin Haduwar Shi da Alhaji AbdulMumini, shine akayi hiring ya kashe family din Hamza kuma yazo ya kashe Hamza amma sai yaron ya burgeshi.
    Toh anan ya ɗauke shi a matsayin yaro tunda bashida yara, dama case din ya kawo Oga Daddy Lagos kuma sun kashe kowa kamar yanda suka fada ma wanda suke kira aikin.
     Alhaji AbdulMumini yanasan potential ɗin Hamza kuma saiya barshi ya koma Harvard ya cigaba da karatu, bai dawo ba sai bayan ya gama komai.
    Yana cikin tattara kayansa ne sai yaga flash drive din da Aisha ta bashi, yana ganin abinda ke ciki ranshi yayi bala’in baci kuma ya dauki alwashin saiya dauki fansa akan duk wanda keda hannu akan wannan aika aikan.
    Aikuwa faduwa yazo daidai da zama saboda yana dawowa ya gane Oga Daddy dan fashi ne kuma yanada resources da zaiyi amfani dashi wajen daukar fansa.
     Bai taɓa binsu operation ba illa yana daga daki yana hacking abubuwa kamar su blueprints da sauran su. Yanzu shekara biyar kenan da fara aiki tareda Oga Daddy.
     Ko sau daya bai taɓa kawo ma Oga Daddy maganar daukan fansa ba, wannan sirrinsa ne...
    Shidai Hamza dogo ne baki, bashida jiki sosai komai daidai. Idan ka kalle fuskansa babu yawan fara’a ko saboda bakin cikin dake damunsa.
   Kyakyawane babu musu, gashi kuma sajensa taje daidai da dogon fuskarsa. Sai kuma dimples dinsa da ɓangaren dama, tunda bawai yana yawan magana bane so ba kasafai kake gani ba. Yanada san buga kwallon kafa, akan kirashi da Messi musamman Last Don.
     Shi dai Hamza ya kasance yana san addini da kuma kare hakkinsa, baya wasa da sallah kuma baya kaunar mai yin haka. Duk abinsa sai yayi sallah kuma yana yin azumin Monday’s and Thursdays jefi jefi...
    Shi yanzu yana tunanin ya aureshi da Hunaisa zai kasance, dama bawai fyade zaiyi mata ba, yayi niyyar tsorata ne kuma ta tsoratu.
    Yasan cewa dukda bawai yana jin dadin abinda sukeyi da Oga Daddy bane amma dole Allah ya kamashi da hakkin mutane.
    Gaskiya shi baya tunanin zai iya auren Hunaisa saboda yasan hakkin aure kafin yaje lahira kaya yayi mashi yawa... Wannan kenan!



#YGG




DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now