Thirty-five

4.6K 308 45
                                    

Bayan kwana biyu.....

   Zaria...

  Yaune daurin auren Mudassir Kabiru Gwaiba tareda amaryarsa abin alfaharinsa Hunaisa Musa. Murna wajensa baya misaltuwa tareda sauran Yan Gidan Gwaiba musamman ma Gwaggo Dija.
   Sai kaiwa da kamowa akeyi cikin annashuwa da jindadi, an ɗaura bisa sadaki dubu hamsin lak'adan ba ajalan ba.

   Ba'a yi kowane events ba saboda har yanzu tana famada PTSD(Post Traumatic Stress Disorder), ko kamu na gargajiya akayi na fesa nono da turare.
   Sam ba'a yi treating ɗinta kamar bazawara ba, dama aurenta na farko ba'a yi mata haka ba. Kuma tasha su Dilke da Halawa tayi kyau. Saidai kana ganinta kasan tana cikin damuwa, idanunta ya bala'in fitowa kuma gatada k'ashin wuya looking so malnourished.

    Tunda satin ya shigo ta shiga tashin hankali dayafi wanda take ciki, wanda yafi rabuwarta da Mudassir tun farkon lokaci. A lokacin tana ganin babu abu kuma da zai ɗaga mata hankali kamar shi, but lo and behold saiga wannan.
   Kwana kuka tashi kuka, Mommy ne watau Hajia Zainab take mata nasiha akan ta dauki kaddara kamar yadda kowane musulmi ya dace ya runguma mai kyau da mara kyau.

    Tana mata nasiha akan tayi hakuri akan kome ke damunta saboda kuka baya magani banda hassada wani cutar. To ta rage kashi kusan 40% da take yi da.
   Yanzu takanyi idan ita kadai ne a ɗaki. Dukda yanda Hunaisa ke basar da Mudassir bai hanashi ɗawainiya da ita ba. Sam baya jin haushin abinda takeyi ko ace sabon yanayinta.
   Ko shine aka ɗauke na wata shida tareda azabatarwa zai shiga hali fiye da nata, yasa yake mata bala'in uzuri. Indai Hunaisan daya sani ne to fah yasan soyayyar datake masa yafi wanda yake mata, shikam lokacin har mamakinta yakeyi.
   Tana warkewa komai zaizo masu sumul, hausawa sun riga sun gama magana da suka ce 'Mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romonta' kokuma wasu sukace 'Mahakurci mawadaci'

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now