Fourteen

4.7K 303 48
                                    

'Yan Gidan Gwaiba

   Wattpad @Aynarh_dimples

   Page Fourteen

 
  _*Let me use this medium to appreciate all your efforts towards me, u are a sister and a rare friend. Allah ya albarkace rayuwarki, yasa ki fi haka... This goes to the Charming Pha’eexah AKA Ummiejafar ❤ Ashafa yana gaisuwa #YGG*_

******

Bayan Wata Daya...
  
  Brooklyn, NY

      Hamza ya kama masu gida na 2 bedroom shida Hunaisa, wani karamin cottage ne ya samo masu a wani kurmin daji. Dukda wajen yanada nisa da shi karin kansa Brooklyn ɗin ballantana ace Manhattan inda yake zuwa makaranta.
      Idan zai tafi makaranta yakan kulleta a cikin gidan saiya tafi. Sau da dama tana san guduwa amma bata samun dama sai yau
     Yau cikin ikon Allah bai rufe gidan ba saboda cikin daji saije ya samo su itace, a haka ta runtuma a guje. Bawai tasan inda zata bane, amma zaman kan titi yafi mata zaman gidansa.
     Ita tasan cewa Hamza bai taba muzguna mata ba, koda yaushe yana kokarin faranta mata rai.
    Bayan sunje US, da kanshi ya siyan mata su kaya kamar riga, wando, skirt, gown, jackets saboda sanyi, safan hannu dana kafa, boots, kayan shafa, sabulun wanka, auduga na al’adanta, mayafi da sauran su.
     Kullum yana cikin mata hidama daban daban domin ya burgeta. Dukda murmushi da fara’a ba ɗabi’ansa bane amma yana kokarin sake fuskanshi idan yana mata magana. Bai taɓa daga mata murya ba ko makamancin haka.
      Yana kokarin faranta mata rai a koda yaushe, shifa burinsa ta rage tsanar sa koda bata dena ba gabadaya.
     Soyayyar ta kullum samun mazauni yake cikin zuciyarshi,  so mugun ciwo ne kuma yafi kowane cuta zafi, a yanzu Hamza ya yadda da wannan kalma.  
      Bai taɓa tunanin xai faɗa tarkon so haka ba farad ɗaya, gashi abinda yafi ciwo shine san maso wani yakeyi.
       Kullum yakan ji ta tana kuka a daki tana kiran sunar Mudassir, ko ba’a faɗa mashi ba yasan cewa shine wanda zai aureta. Saidai kuma babu karya yana ganin kokarinta, yanzu yanda yake jinta a ranshi dukda basu wani saba ba balle dadewa, idan wani yayi sanadiyar rabasu sai yayi kusan hauka.
     Ba kuma sai an faɗa ba amma yasan he is very selfish, abinda yayi bai kyauta ba kuma yasan bazai yafu ba, saidai fatan Allah yasa ta yafe masa yakeyi a koda yaushe.
        Duk wani aikin gidan shi keyi, saboda baiyi trusting ɗinta akan ta lura da wani abu ba. wanke wanke bayan kwana uku ko hudu yakeyi, shara kuma tun zuwansu sau biyar yayi. Bashida time kwata-kwata saboda wajen dayake zama yayi bayan gari balle a soma maganar karatunsa da uban assignment.
      Bayan kwana biyu biyu Oga Daddy yana kiransa yaji halinda yake ciki tareda tambayarsa ko yanada wani matsala, Bai taba gaya masa batun Hunaisa ba sabida bazai lamunta ba.
     Kuma ko a haka yana jaddada masa amfanin makaranta sabida yana nan yana shirya masu wani gagarumin Operation da zasuyi wanda kungiyar su bata taɓa irin sa ba, harta cikin Nigeria sai an tona.
    Toh ya amsa mashi dashi saboda baisan ya zaiyi da Hunaisa ba idan abin ya matso kai.
    Kamar koda yaushe idan ya kuskura yaje bayi koya tafi wani guri mara nisa bai kulle kofa ba takan kokarin guduwa, haka yau shima tayi, ta samu nasara tana gudu har kan titi, anan taji shi shiru, firgita tayi sosai idonta ya raina fata. Wannan shi ake cewa gaba rafi baya maciji.
   Dama Hamza ya saka alarm cikin gidan kuma yan kunne ta ya makala tracker bata sani ba, bai wani sha wahala ba ya kamota. Duk sanda take kokarin guduwa bai taɓa jin haushin abin ba kamar yau sabida gudun 3 kilomètres tayi.
    A rakube ya ganta a gefen bishiya tana rizgan kuka, idonta sun kumbura balle ma bata saka kwalli sai yayi kamada nama. Gashi duk kafanta ya fara gurjewa kasancewa bata saka takalminta ba.
    Yana isa wajen ya fincikota, baiyi wata wata ba ya sharara mata kyawawan mari guda biyu. Itama tasan tayi laifi saboda ko kallan idonsa ya koma kamar na mugaye.
   Ta tsorata tana ja ta baya baya saiya damketa wajen kwalla, rufe idonta tayi tsam hawaye suka cigaba da bin mata fuska.
    Murya yana rawa ta soma magana, “Dan Allah kayi hakuri, wallahi bazan kara ba”
    “Ba sai kin faɗa ba amma daga yau bazaki kara ba, kin raina ni saboda ina wasa dake koh?” ya faɗi saiya dauketa. A kafaɗarsa ya ajiyeta yana tafiya zuwa gidansu.
      Ita kuma kuka taketa yi gashi wajen kunnesa ne, “Malama zaki rufe min baki ko saina ajiye ki kan titin nan nayi maki ɗan iskan duka”
      Da hannu ta rufe bakinta ta toshe saboda bazata iya daina kuka haka ba. Haka tana saɓe a kafadarsa har suka kai Cottage ɗinsu.
   Bai direta ba sai kan gadon bedroom ɗinsa wanda bata taɓa shiga ba, dama shi tun sanda ya dauketa a naija da kuma ya taɓa ta da farkon zuwansu bai sake ba.
    Idonta kara budewa yayi dataga meke shirin faruwa da ita, rufe kofa taga yayi saiya wuce bedside fridge ɗinsa ya dauki wani irin lemun kwalba wanda bata san sunarsa ba.
      Sai kuma ya zaro wani kwaya a cikin aljihunsa, katin mai guda biyar ne saiya ɓalla guda biyu ya haɗeye. A kasalce ya soma magana saboda har handwork din bokan bature ya fara tasiri a cikinsa.
       “Ba kin raina niba, kinga na kyaleki koh? Halan ance maki ni katako ne? Toh yau sai na nuna maki ke karamar mara kunya ne” Saiya nufa gadon ya hau yana murmushin mugunta, ita kuma matsawa baya takeyi amma harya kai dab da ita.
      Dan Allah kayi hak’uri na ranste da Allah bazan kara kokarin gudu ba”
     “Ai daga yau bazaki kara ba, i will make sure of that” ya faɗa murya kasa kasa, kusancin su yakai hancinsa yana gugan nata.
   Hannunsa yasa ya fara shafa wajen gefen fuskanta yana lashe lebensa daya soma alamar bushewa. Anan ta kara kidimewa, zufa ne ya soma karyo mata ta wajen wuya, goshi, kafanta Infact duk ilahirin jikinta, kawai ta rasa me ke mata daɗi.
    Ras ras ras kirjinta ke bugawa kamar zai fashe, tashin hankali take ciki mara misaltuwa. Idan akace mata zata iya tsintar kanta a wannan yanayi zata musa amma sai gata tsundum ciki.
    Yau tasan babu mai kwatanta a hannunsa.... Wannan kenan!

******
Haka rayuwa ya canza ma Mermer farad ɗaya, Anty ta mallake gidan nan tsaf babu mai iya kataɓus saidai ita.
      Mermer ta dauki na annabawa tana zaune a ɗakin shargi na da, sauran kayanta da bai samu damar shiga ba sai ta kai BQ ta ajiye.
   Kwata-kwata ba’a dafa abinci da ita, wata rana ta tirke mai aiki ta dafa mata wata sa’in tayi Indomie da kanta Kokuma taje waje ta siya taci.
     Duk wanda ya ganta cikin kwanakin nan yasan tana cikin damuwa, musamman ma Nawaz kullum yana cikin tambayarta ko lafiya?
     Nawaz yanada kirki itama ta sani, kuma yana kyautata mata more than she deserves. Saidai kuma wani hanzari ba gudu ba. Yanada bala’in kauyanci
   Yanzu tayi kunnen doki da duk wani ba kauye, Anty ta nuna mata cewa iskancin dan kauye yafi nan dan birnin, yasa kwata kwata yanzu ya kara fice mata daga rai.
     Dukda bawai a kauye yake zama ba, amma halayyarsa bashida maraba wata sa’in da nasu koba kullum ba.
     Babu nacin da baiyi ba amma tayi burus dashi, haka take dizgashi a gaban koma waye idan ya kuskura yayi mata magana.
    Pouring anger ɗin Anty takeyi sosai akansa, shikuma ya nace. Ya riga ya dauki alkawari babu gudu babu ja da baya.
     Asma’ul Husna bride to be anata iyayi, sai feleke takeyi ta samu gabo wanda zai aureta.
    Sakin mata kudi yakeyi babu kama hannun yaro na shirin events. Ita tasan cewa zata ji dadi nan gaba amma to her surprise it came sooner than later.
      Ashafa dan garin Birnin Kebbi ne a wani gari da ake ce masa Dakin gari. Maihafinsa Alhaji Sambo Dakin gari yanada yara shida, biyar mata sai kuma namiji auta watau Ashafa.
       Yanzu haka duk sisters ɗinsa sunyi aure saura shi kadai dan auta, mahaifinsa tsohon Jakada ne na Nigeria a US, bayan ya bari bai dawo Nijeriya ba.
      Yanzu haka Ashafa shi kadai yake zama a tsohon gidansu na Kinsasha Road dake Unguwar Rimi na jahar Kaduna.
      Kanin Mahaifin Ashafa da wani limamin unguwarsu a chan Dakin gari suka kai gaisuwan Ashafa.
      Baffa Yusuf ne waliyin Asma’ul Husna sabida haka shiya jagoranci komai. Anan Alhaji Aminu Dakin gari ya bada sadakin Husna na dubu dari da hamsin, sannan kudin gaisuwan uba da uwa dubu hamsin.
      An kawo hunhun goro guda goma, da katan biyar na chewing-gum din Robbot irin na al’ada, sai kuma katon biyar na sweet domin a bama yan uwa da abokan arziki.
     Harta lefenta an kawo makon daya gabata, akwatuna guda goma ne shake da kaya na alfarma.
      Abin kamar almara wai Husna ta kusan mallakar abin begenta, saura yanzu kwana biyar daurin aurenta da masoyinta.
      Dukda ana wannan hadimar ana yin sa da tention ne, ɓacewan Hunaisa yana nan daram a zukatan su. Babu inda ba’a duba ba amma babu ita babu dalilin ta.
      Gashi har satin bikin Munauwara ya danno kai, dayeke Mommy ce besty ɗin maman Munauwara dole itace kan gaba wajen taga komai ya daidaita.
     Haka idan sun haɗu su biyu a daki sai suyi kuka ma’ishe saboda babu wanda ya kaisu kusanci da ita.
    Shima YaMudassir ya warware kamar bashi ba, harya koma aiki saidai kuma kamar shirme ne.
     Baya wani abin kirki idan yaje wajen, haka yake kafa kansa akan table yayita tunani. Laifin sa kawai yake gani saboda duk abinda ya faru da ita shi yaja.
      Da baice zasuyi video call ba da basu fita neman katin waya ba. Saidai kuma baya fasa azkar tunda Allah ne kawai gatansa.
     Kamar yanda Yan Gidan Gwaiba suka dauka lokacin bikin Hunaisa haka aka dauka lokacin nan.
    Nuwairah sune manya kullum cikin zirga zirga, Nawwarah kamar bata san ana yin wani abu a gidansu ba.
      Kawai ankonta ta karɓa takai wajen ɗinki, itama Mermer an bata nata. Husna abinda takeso kenan ace manya sun je bikinta.
      Events kala shida ta shirya, bridal shower, cultural day, mother’s day, kamu, picnic, dinner da kuma walima.
    Duka kuma tayi dinkin masu  gani na faɗa, farin bridal gown zata saka na dinner ɗinta wanda Carolina Harera ta dinka.
    Sai kuma abayan walima Silhouette Ng watau Xeemee tayishi. Sauran gowns ɗin manya manyan masu dinki sukayi.
     An kira Fati Mamza akan zatayi mata kwalliya, sai Stevereinz zai ɗauki hotuna.
    Wasu events ɗin za’ayi a Hamdalah hotel dake Kaduna, wasu hotel seventeen sai sauran a tsakar gidan gwaiba manor.
      Biki sukeyi irinna attajirai burin Husna, wannan bikin bama burin Husna ba har yanmata baki ɗaya.
    Lubie bata iso ba tukun saboda tana shakatawa tareda saurayinta Minister of Commerce a South Africa, zatayi missing wasu events baifi uku zata samu ba.
     Ran Husna baiso ba amma lubie tace bazata iya barin abinda ya kaita ba, itama yanzu tana fafutuka ya aureta ne.
     
   Ta ɓangaren Nuwairah kuma da Dr Deenie ta rasa gane kansa, tun sanda yace mata he loves her bai kara ba.
     Bawai ta koma kamaninta nada bane, ah ah har yanzu bata saka glass sai zatayi karatu, kuma hakoranta wasai babu karafai
      Shikuma daya tada ma Nawwarah batun zuwanta office ɗinsa saita zazzage mashi kwandon bala’i akan ya raina ta.
    Mamakin abin yayi sosai sai kuma ya tuna cewa mata basa son ana tuna masu conquest ɗinsu wata kila kunya taji 
    Rayuwarta yana daure mashi kai ba kaɗan ba, kamar tanada split personality ko wani abu.
     Sai kuma ya mayar da abin akan kila tana jin haushin rashin sakema Nuwairah fuska daya keyi ne, dama ta riga ta ja masa kunne.
      Toh anan saiya soma flirting kadan kadan da Nuwairah, ita kuma abin nema ya samu, matar makadi ta haifa ganga.
    Nan take ta shagala ta buɗe zuciyar ta sosai saboda soyayyar yasa samu matsuguni a ranta.
   Abin nata yakai data fara binsa a fb duk ta kwashe hotunan sa, ta mayar Wallpaper ɗinta da screen saver, harda wallpaper ɗin WhatsApp.
     An fara mata therapy, kuma cikin ikon Allah tunda angano abinda ke asalin damunta, duk dai bai wuce rashin jituwan su da yar uwanta ba wanda ya haddasa mata anxiety.
     Tana shan magani yadda ya dace, sai dai bazata gane ko ta fara daina wa ba kokuma halin ɓeran yana nan.
     Amma kuma bazaka rabata da tunani ba, idan batayi akan Nawwarah ba zatayi akan Deenie. Ta riga ta kullafa shine muradin ranta kuma rashin samunsa barazana ne a rayuwarta  baki ɗaya..... Wannan kenan!

      Mermer ta shirya tsaf daga aiki zata gida, shiri kawai zatayi saita tafi Hotel seventeen inda za’ayi bridal shower.
     Kayan pink wando ne skinny wanda aka yanka na yankawa saika haɗashi da farin customised riga wanda aka rubuta ASH (Ashafa Sambo Husna)
     Sannan saika daura farin turban, kamar Mermer da Nawwarah sun riga sunsan kansu a buɗe zai tsaya.
    Mermer dama ita kadai taje aiki, shima sha biyu ta tashi. Takai gida sai Ado ya buɗe mata ta shiga. Bayan tayi Parking saita wuce cikin gida.
     Anty ta gani a falon kasa tana kallo, tun daga nesa ta kejin babbaka dariyar ta. Tana isa taganta tana zaune a kasa duk ta buɗe kafa kamar tana shirin yin Bori.
     Gauda ne da tubani abinsu na kauye take ci, sai wani bakin leda daga gefenta ta ajiye. tana kallon wrestling sai dariya takeyi. Gata da kankamban san yi turanci kuma bata ma iya ba.
     Jennifer ma ta fita iyawa dukda tana cewa ‘I can spoke English’ da ‘Hw is you’ amma ta kece ma Bilkisu tsara.
      Haka ta wuce ta bata ko kalleta ba ta shiga daki, Jakarta ta ajiye akan gado saita cire takalminta. Kai tsaye fita tayi ta nufa kitchen domin tasha ruwan sanyi ko drink.
   Anan taga abin mamaki, an garke shi da katan kwaɗo wanda za’a iya rufe gate din gida dashi.
     Shima store gashi da nashi kwaɗan har biyu, da sama da wajen kasa.
    Abin yayi bala’in bata mamaki saboda bata taɓa ganin inda aka kulle fridge ba, ko a almara masu zuzuta karya.
     Falo ta koma wajan Bilkisu, inda tabarta nan ta ganta, saidai kuma ta buɗe bak’in ledar dake gefenta tana cin gyaɗa soyayya.
      Murzawa takeyi da hannunta biyu saita hura da bakinta. Haka yake barbazuwa kacha kacha a falon kuma ko a jinkinta.
   “Bilkisu ke kika kulle fridge da store?”
    “Eh nice” ta faɗa yayinda ta murza gyaɗa ta watsa bakinta.
    “Akan mene?”
    “saboda naga dama, kuma gidana ne... Kema idan kinji haushi ki fito da miji kiyi aure”
    “Toh bani makulli na ɗauki ruwan sanyi kishi nakeji”
    Kallon rainin arziki Bilkisu tayima Mermer, cikin masifa tace “Idan baki lura ba ban aminta dake cikin kitchen ɗina ke kadai ba, kuma yanzu banjin tashi balle muje na baki ruwa. Saboda haka ki kunna pampo ki sha, idan kuma kinfi karfi kisha na pampo toh saidai kishi ya kashe ki sai ki koje inda uwarki ta tafi”
     Abin ya bama Mermer haushi, idan Bilkisu zata yi iskancinta tayi da ita kawai amma karta haɗa da Mamanta.
     “Toh bari kiji wani abu Bilkisu, mutuwa dai na kan kowa, komai lokaci ne... Kuma idan kikayi hak’uri bani ba harke duk zamu wajen data ke”
     “Wannan keya shafa, karamar karuwa kawai... Kuma gantalin da kike zuwa na kusan maganinsa saboda bazan lamunta ba”
     Kafin Mermer ta amsa saiga Daddy ya shigo, “Assallamu alaikum” yace
     “Waalaikumus salam” suka amsa a tare.
    Yana tafiya dukda alamar gajiya a jikinsa, ita kuma Bilkisu ta Mike tsaye ta karkabe gyaɗan dake jikinta.
     Riga da skirt ta saka na show me your back, dayake yar kauye ce duk bra ɗinta yamafi rinjayan idonka.
    Da gudu ta karasa gunsa ta ɗare masa jiki, “Honey sannu da zuwa” saita sumbace sa. Yatsina fuksa Mermer tayi tareda kauda kai sabida abin ya bata kyama.
      “Yauwa uwargida ran gida, mu karasa wajen kujera saboda yau a gajiye nike”
    “Toh ni gaskiya bazan yarda ba, daga yau bazaka kara zuwa ba tunda haka ne abin”
      “Toh shikenan babu damuwa, abinda kike so shi za’a yi”
     A razane Mermer ta kalleshi, “Daddy me kake nufi da bazaka kara zuwa aiki ba?”
      “Mamanki tace bataso kuma hakan za’ayi”
  “Dan Allah Bilkisu karkiyi haka” Mermer tace yayinda kuka ya kubce mata.
    Bilkisu bata kulata ba, illa janyo Daddy jikinta ta fara masa salon masu aure, gwiwa babu kwari Mermer tabar wajen kafin taga abinda yafi karfin idonta.... Wannan kenan!..

       Kowa ya hallara a hotel Seventeen za’a fara bridal shower, Amarya farin offsholder ta saka na three quatre jumpsuit wanda yayi mata ɗas a jiki. Saita saka farin tutu tareda farin sash wanda aka rubuta, “Mrs Ashafa”
     Sannan kuma ta saka silver Tiara a saman kanta, sai kuma ta saka choker a wuyanta
      Su kuma su Nawwarah, Nuwairah, Mermer da sauran friends ɗinta duk suma sun saka Sash wanda akayi rubutu, ‘I’m Next, Then me, Engaged’ da dai sauran su.
       Anyi bidi’a yanda ya dace, Nawwarah ta bama Amarya kyautar Lingerie set uku na Victoria Secret.
     Ita kuma Mermer Night gowns ta bata tareda costume mask. Nuwairah kuma wasu soft Chiffon gowns guntaye ta bata.
      Sauran kawayenta sun bata su turaruka da kuma su inner wears.
      Anci su ice cream, chocolate, drinks dasu snacks. Abin yayima ma Husna armashi yadda ya dace.
    Wajen karfe tara Ashafa ya kirata yaji yadda komai yake kasancewa, “Sweety bakaga yadda komai yayi kyau ba, i wish u were here”  
        “Allah koh babyna?” ya faɗa murya kasa kasa.
       “Bakaga yadda aketa rawa ba, balle kuma dana gwada lingerie da Nawwarah ta bani... Wow baby Allah ya kaimu daren auren mu”
     Shiru yayi baice komai ba kamar bai jita ba, “Sweety lafia kayi shiru”
   “Baby missing ɗinki nakeyi, kawai inaso na ganki ne”
    “Sweety cikin daren nan?”
     “eh mana, Inace a wajen zaku kwana?”
    “eh anan ne”
   “Yauwa saiki san yadda zakiyi ki gudu koda na 30mins ne”
   “Anya Sweety bazamu bari gobe ba”
    “Haba Baby rowan kanki zaki min, don ina san ganinki koh? Babu damuwa kije tunda kina ganin shine yafi maki kyau”
   Ana ta kuma rude, “Sweety ba haka nake nufi ba, naga dare ne yayi”
   “Ai dama ke baki damu dani ba, idan sanki zai kasheni ne saidai na mutu amma ko a jikin ki”
     “Kayi hak’uri dan Allah”
    “Keh sai anjima barci zanyi”
    “Haba Sweety kar muyi haka dakai, naji kazo ɗin”
   “Wow baby kin tabbata”
   “Eh im sure”
 
35mins later...
    Ashafa ne yana Parking lot din Hotel seventeen yana jiran Husna, tun data ke zuwa yaji zuciyarsa yana bugawa sosai.
   Yau hakon daya haka zai cinma ruwa, a yau zai fansa duk wani abu dayayi mata. A yau zata biya wani shawarma dataci, wani ice cream data sha, wani ɗinki daya karbo mata.
    Bai masan ta iso ba saida tayi clicking hannunta a iska, Firgit ya dawo daga tunanin sa, “Sweety tunanin me kakeyi ?”
    “Baby banida wani sauran matsala tunda an bani ke a matsayin mata”
     Daga nan ta zagaya dayan ɓangaren ta shiga, murmushi suke ma juna wanda ke tareda sakon so da kauna.
    “Okay baby muje field trip mu dawo, na mance maki da wani zobe haka”
    “Okay Sweetie babu damuwa”tace babu wani tantama a ranta balle taji kyauta za’a bata.  
     Sannu a hankali har suka isa Kinshasa inda gidansa yake, zagayawa yayi ta ɓangaren ta ya buɗe mata kofa.
     “Fito muje koh” saiya mika mata hannu, bashi tayi sai suka tafi cikin gidan.
   Ba’a gidan zasu zauna ba, Kinkinau za’a kaita inda gidansa yake.
    Tsarin gidan iyayensa yayi mata kyau sosai, bai sake mata hannu ba saida ya kaita cikin bedroom ɗinsa.
     “Ki zauna mana” yace saiya nuna mata kan gado.
   Babu musu ta zauna, shi kuma yaje drawer ɗinsa ya fito da wani kwali dan karami, budewa yayi saiya fito da wani zobe mai kyan gaske.
    Gold ne aka haɗa da azurfa, da sauri ta mika masa hannunta ya saka mata. Yana sawa saiya soma shafa wajen yanayi yana kallonta.
    Daga nan saiya kai lebensa wajen, anan ta soma shan jinin jikinta.
   Janyo ta yayi ya runguma tsam, basai ya faɗa ba amma ta gane inda ya dosa. A hankali ta soma zame jikinta amma yaki barinta.
   “Baby inace ke kika ce kina sha’awan kasancewa tareda ni... Toh yanzu na kawo maki kaina sai yadda kikayi”
     “Dan Allah ka bari mana, an kusan ɗaura mana aure. Kaida bakinka kace kafin son muyi aure”
    “Toh yanzu nace ina so, meye matsalar ki? ... Nafa biya sadaki kuma yanzu you are automatically mine”
      “Da yau da ranar auren mu baby duk daya ne, kinaso nasha wahala ne kafin nan, wajena fa za’a kawo ki”
      Haka tareda taimakon sheɗan yayi mata tasiri ta bashi kanta a matsayinta na ‘ya mace.
  
6:30am....
    Lokacin ne Ashafa ya mayar da ita Hotel ɗinta, daren jiya ya kasance dare da bazai taɓa mancewa ba. Infact bashiba har ita kanta Husna.
      Tana tafiya suna daga ma juna hannu suna murmushi, sam bataji dana sanin abinda tayi ba sabida ai nanda kwana biyar zata aureshi.
     Tana ɓacewa daga haraban saiya tura mata text. Abin yana shiga wayanta bata karanta ba kawai taga sunarsa ne, murmushi tayi sosai saboda duk duniya babu wanda ya kaishi kulawa.
      Koda ta isa ɗakin kowa yana barci banda Nuwairah dake karatun Quran, murmushi tayi mata saita koma gefe ta zauna domin karanta msg din Ashafa.

     “Zuwaga hasken zuciyata....lol wallahi karya nakeyi. Bari na fara maki daga farko yadda zaki gane. Duk me kikaga ya faru dake ke kika jawo ma kanki, Na farko dai da muka hadu dake nasha shiriyata zaizo ta hanyar haduwarmu, amma kuma sai naga akasin haka. Abin duniya ya rufe maki ido, kwata kwata bakida kawaici da wadatar zuci... Kedai kawai a baki koda yaushe... Ni abin lokacin bai dameni ba saboda kudi ba matsalata bane, amma kuma ashe kin raina ni, ni kike kira gabo mai kudin banza. Sweetheart ki buɗe idonki da kyau, babu namiji wawa ko gabo, kowa yasan abinda yakeyi. Bakisan wani abu da maza ba zasuyi hakuri na tsawon lokaci har su cinma burinsu. Bayan na daina sake maki fuska shine kika kawo kanki wajena saboda kaskanci. Da farko naso na karɓa ɓukatan ki amma naga idan ban koya maki darasi ba kinci banza kenan. Yasa na kawo maganar aure, nayi hakan ne domin ki aminta dani, kinga kamar green snake under green grass, baka ganinsa saidai ya sareka bazata. Ko sau ɗaya bazan iya auren classless mace irinki ba, gashi kuma yau naci banza harda wofi. Koda yake ba banza naci ba kudina na karɓa tas a jikinki. Saidai kuma wani hanzari ba gudu ba, kwata kwata bakiyi ba, banji dadi ko sau ɗaya yasa kinga bazakiga laifina ba idan nace bazan iya aurenki ba.... Kada kiyi tunanin nemana saboda yau zan koma Los Angeles.... Ki ajiye lefen da sauran abubuwan dana baki saboda ban bukatar su dama kece matsiyaciya.... Ma’assalam”

       Tana karanta hawaye ke fito mata daga kumatu, dailing number ɗin Ashafa tayi amma yaki shiga saboda bayan text ya nuna ya shiga saiya karya sim card dinsa.... Wannan kenan!




#YGG





DIMPLΣS ce


'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now