Twenty-eight

4.2K 275 22
                                    

Brooklyn, NY

    Kwance tashi babu wuya wajen Allah, ana satin da Hamza zai koma gida. Saidai shi kadai yasan suna gamawa zai koma.
     Itama tasan zai gama karatu amma batasan suna gamawa zasu tafi ba. Shi kam Oga Daddy yana nan ya hada mashi party akan dawowa da zaiyi.
   Duka boys dinshi su 28 zasu hallara, kuma an nema yan mata birjik. Akalla kowane namiji zai ware da mata biyu or more a daren party.
   Kuma an siya kayan maye kamarsu giya, k’wayoyi tareda hodar ibliss. Yaran Oga Daddy daga kabilu daban daban ne har yan Ghana akwai.
      Komai dai an tara masu yanda zasu hole kafin big day ɗinsu da zasuyi arziki ya iso.
    Shikam Hamza sunata zuba soyayya da Hunaisa, yanzu ta riga ta sake dashi sosai. Tana iya tsayawa babu mayafi ko dan kwali a gabansa. Shima kullum cikin neman faranta mata rai yakeyi, tare suke dafa abinci idan yana nan dasu scholar.
       Saura kwana uku su tafi kuma harya siyan masu tickets, dayake daya biya kudin gida harda na furnitures ya bada yasa yanzu kawai kayan sawansu zasu dauka .
    Shi kadai yake shirye shirye ita Hunaisa batasan bakin zarenba. Koda ya dawo tayi maza ta karbi jakansa. Shikam dukda a rufe yake yana zulumin ya buɗe ta gani.
    Har Yanzu ya kasa summoning courage dazai faɗa mata zasu Naija. Yasan tanaji zata birkice masa kuma abinda bayaso kenan.
   Haka zaita wanata har ranar koma me zai faru ya faru. “kaje kayi wanka ka dawo lokacin na gama komai” tace masa
    “Toh sannu da aikiya amsa saiya nufa hanyar dakinsa, har cikin ransa yana jin haushin yanda yake mata karya, but saidai kuma he can’t help it tunda bashida wani zabi.
    Yayi wanka ya saka grey jallabiya mai hood, Sallar isha yayi da shafa’i da wutri. Ya fito falo yana kamshi saidai bai tarad da Hunaisa ba.
      Ita kuma tana daki itama wankar tayi saita saka Tan top da jens, ita ta riga ta sake dashi kuma bataga dalilin da zata rinka boye masa jikinta ba,balle mijinta ne na sunna.
       Sallar itama tayi ta fito lokacin yana zaune akan couch yana kallon ESPN, a tare sukayi murmushi. “Zo na zuba maka” tace. Shikuma babu musu ya tashi suka nufa dinning.
     Ta zuba mashi macaroni da sauce sai kaza datayi micro waving. Ta zauna zata fara cin nata sai yayi karab ya kwace cokalin, “Ni zanyi feeding matana
   Tana murmushi ta sakar mashi cokalin, saiya matsa da kujerar sa dab da nata. Kusancin su yakai yana jin saukar numfashinta.
   Da tasan haka zai faru da ita da tun farko bata yarda ba, haka ya rinka bata har ta cinye. Shima nan ya noke kafada yana zumbura baki wai saita bashi.
    Dariya tayi sosai saboda kamar karamin yaro, haka ta hakura tana bashi. Wata sa’in yayi kamar zai tauna cokalin harda hannunta.
   Da kanshi yayi wanke wanke ita kuma tana zaune tana kallonsa, da badin circumstance ɗin da suka hadu ba datace she is the luckiest gal alive.
   Snapping fingers ɗinsa yayi a fuskarta ya dawo da ita daga tunani, “tunanin me kikeyi ?”
   “Tunaninka nakeyi” ta faɗa a ranta. Amma a fili murmushi tayi.
   “Koda yake nasan me kike tunani, ba kinga fine fresh boy no pimples only dimples ba kin wani rude” ya faɗa yana kanne ido.
   Dariya tayi ta saukar da kanta, yana abinsa kamar Merlin inba haka ba ta ina zai san abinda ke ranta.
   Jan hannunta yayi suka wuce falo, film ɗin Fault in our stars yayi masu haya a Netflix. A kujera daya suka zauna tunda couch ɗin yanada faɗi.
   Haka suke kallo ko ace take kallo, dayake ita bata kallon film sosai yasa bata taɓa ganin film ɗinba dukda tsufansa.
   Love life ɗin Hazel Grace da Augustus Waters yayi bala’in burgeta, saidai kuma kafin karshen idonta kamar kankana sai kuka takeyi. Zuciyarta ya soma harbi, sannan kuma ga kusanci dake tsakaninta da Hamza.
   Tsigan jikinta yayi bala’in tashi, a ranta tana ayyana kokarin Hazel bayan mutuwar saurayinta, dukda kawai tana zaune da Hamza ne amma duk wani rabuwa dasu samo yanzu zai bala’in taɓata.
   Shikam abin mamaki ya bashi daya lura kuka takeyi, soyayarta kara samun waje yayi a zuciyarsa.
    Janyota jikinsa yayi yana buga mata baya a hankula, a haka ya rinka watsa mata kalamai masu kwantar da rai.
   Ranar ma a ɗakinsa yace zata kwana saboda bai yarda akan bazata sake kuka ba, ita kuma ta jaddada masa cewa dama idan tana kallo haka take amma bai saurareta ba.
     Haka ta hakura suka kwanta ɗaki daya cikin shinfida ɗaya a wannan daren.

4:00am...
   Hamza ne ya fara mikewa tsaye, murna fal ransa yau ya kasance da abin begensa gashi kuma ya sameta a matsayinta na ‘ya mace.
   Bashida bakidan zai gode mata akan karamcin datayi masa, kawai fatan alheri yake mata. Bayinsa ya wuce yayi wanka tareda daura alwala.
   Zuwa yayi ya kabbara sallah yayi nafila, gode ma Allah yayi sosai har aka kira sallar farko. Anan ya mike yaje inda Hunaisa ke kwance.
    Itama taji sanda ya tashi amma kunyansa bazai bari ta mike ba, gefen fuskanta yazo ya durkusa. Tana jin mutum a wajen sai wani fiki fiki da ido takeyi.
    Anan ya bushe dariya saboda ya lura idanta biyu. “Baby barcin ya isa haka” ya faɗa tareda cire mata gashin da suka fara zubo mata.
   “Nika fita tukun” tace idonta a rufe. Babu musu ya tashi yayi hanyar kofa, tunda tanasan privacy ɗinta gwara ya bata.
   Bayan ya fita ta tashi ta zauna, mamakin komai takeyi. Yanzu shikenan ta zama cikarkiyar matan aure, yanzu shikenan YaMudassir yayi mata nisa.
      saida ta gyara mashi gado tareda arranging ɗakin sama sama,sannan ta shiga bayi, bathtub ta shiga tayi wanka sai ta jero alwala. Koda ta fito daga bayi taga clean outfit da kuma hijab akan gado watau Hamza ya kawo. Murmushi tayi saita soma sakawa.
   Shi kam yasan yanzu kunyansa takeyi amma dole ta daina, gashi jibi zasu koma gida. Yanaso cikin yau da gobe su saba sosai.
     Bayan tayi Sallah tana cikin arzkar, sai gashi ya shigo. Murmushi tayi saita cigaba. Saida tayi maishe sannan ta tashi.
   Drape gown baby pink color ya kawo mata watau wanda ta saka kenan, anan ta sake kwanta masa cikin rai, “Baby how are you?”
   “lafiata lau” ta amsa.
Komawa ɗakinta tayi wai zata kwanta, bai hanata ba yace zai duba wasu files. Ya lura yanzu gudunsa takeyi.
   Ita kam tana zuwa ɗaki tunanin sa takeyi, duk yanda taso ta daina amma ta kasa. Wani guntun hawaye ya soma gangaro mata data lura ta fara sanshi kuma bata san yanda haka ya faru  ba.
   Tausayin YaMudassir tayi saboda wannan shine tsantsan betrayal. Ta fara san mugun daya sanadin rabuwar su kuma ya masu iyaka da rayuwar da suke buri tun shekaru da dama da suka wuce.
    Amma saidai zuciya bata san wannan ba, Love comes in the most unexpected ways bazaka san lokacin daza ka fara ba.
   Haka tayita mirginawa ga kuma ciwon san dake addabarta. Wannan ya ninka wanda takema YaMudassir sau dubu, yanzu har wani zafi zafi takeji a ranta.
     Hamza yaje yayi masu toasting bread saiya haɗa da pourched eggs tareda oats. A tray ya saka saiya wuce ɗakinta.
      Tura kofa yayi tareda sallama, ciki ciki ta amsa saboda yanda ranta ya jagule. A kan gado ya dire masu abinci saiya hau da kyau, “Bismillahyace saiya soma cin nasa.
    Murmushi tayi saboda tasan yanaso ya bata space ɗinta amma kuma ya kasa, haka ta saka hannu sukaci saidai ba sosai taci ba.
   Suna cikin ci ne sai sukaji karar mota, kuma basu taɓa jin haka ba.
    Sam ya mance za’a iya leke ta Window, falo ya nufa. Ita kam window ta nufa.
     Mutane biyu ta gani maza sun nufa kofa, Shikam Hamza yana isa bakin kofa sai yayi ido biyu da worst nightmare dinsa.
     Oga Daddy da Last Don tsaye in flesh ba mafarki ba.
   Ware hannu Oga Daddy yayi saiya ce, “Boy ka girmasai suka runguma juna. Dama zumudin ya kusan yin arziki ne yasa yace gwara yaje ya dawo da Hamza da kansa tareda ganin gari da kyau.
   Koda yake daga Russia yake yaje order ɗin bindigogi sabbi yan yayee wanda zasuyi amfani dashi akan duk wanda ya kawo masu wargi. Dama duk duniya ansan Russia sun kware a haɗa makamai.
   Hamza mutuwar tsaye yayi, tabbas ya gaya ma Oga Daddy address dinsa amma baiyi tunanin zaizo ba, koda zaizo atleast zai masa waya ba zuwan bazata ba.
    Kallon Last Don yayi irin kallon tuhuma meyasa bakaga gaya mun ba, shi kuma Last Don daga kafada yayi tareda nuna Oga da hannu irin shi na kema aiki ba kaiba.
    Hunaisa ta saka mayafi ta fito falo, anan kowa ya mayar da hankalinsa kanta.
   “Boy Waye wannan?”
   Rawar baki Hamza ya soma yi, Oga Daddy ne ya dafa mashi kafada, “Karka damu na gane, aika ba katako bane, dole ka samo babe da zaku hole, Nima anjima ita zatayi min tausaya faɗa yana kyallara ido.
    Sun shiga cikin falon sai Hamza yace ma Oga suje ɗaki suyi magana, ita Hunaisa Ikon Allah take gani. Ta rasa meyasa Hamza ke hulda da mutanen nan. Koda yake deep down tasan Hamza is not really a good guy.
    Oga Daddy ya kasance irin bakin kirin, dogo mai tulelen ciki. Ga kuma eye balls ɗinsa kamar zasu fito daga  eye socket dinsu saboda girma.
      Sak yake da Segun Arinze na Nigerian English Films, kila Segun yafi shi armashi da fasali. Suna shiga daki sai Hamza ya rufe kofa.
    “Boy faɗa min dalilin dayasa ka kawo ni cikin daki da bazaka iya min magana a gaban Whore ɗin chan ba da Last Don”
    “Matata ceya faɗa fuska a murtuke kamar hadari.
    Su kuma Hunaisa da Last Don anan kallon kallo,  ta gane shi sarai saboda shine suka ɗauko ta da Hamza kuma yace zai bindigeta idan bata natsu ba.
     Harara ya watsa mata wanda shima ta mayar masa. Haushin ta yake ji sosai. Sanadin ta ne best friend dinsa yayi losing focus baya ji baya gani.
   Gashi kuma bayaso ya nastu su samu dukiya, zama tayi ta wajen dining ta kafa mashi ido kur.
   Zufa yake ke to ma Alhaji AbdulMumini, “ban gane ba Boy? Meye ma’anar matarka? Kana nufin zaman dadiro Kokuma matar sunna?”
   “Matana ta sunna”
    “Yar gidan waye
Yarinyar Major Musa amma mahaifiyarta Yar Gidan Gwaiba ce
     “Whatttt!” Oga yace da karfin tsiya saiya haska mashi mari
     “Boy are you out of your damn mind? Yusuf Gwaiba zamu yashe shine kakeso ka ɓata mana harka, why are you sleeping with the enemy?”
   Gaban Hamza ya sake tashi fiye da nada, yasan yanzu babu mai kwatar Hunaisa a hannunsa saiya kashe ta.
     “Boy kayi hakuri, amma dole na kashe ta kafin ta kawo min matsala
  Dukawa kasa yayi ya rike ma Daddy kafa, kuka yakeyi wiwi yana neman alfarma, “Dan Allah karka kashe min ita, wallahi itace rayuwata
   “ Dole ta mutu boy saboda i need ur head straight ”
    “I promise you Daddy bazan baka matsala ba”
    “Okay bazan kashe ta ba sabida kada ta mutu na rasa gane kanka. Amma dole kayi min alkawari guda biyu.”
   “ko me kakeso zanyi” yace yana kuka.
    “Na farko zaka saketa, na biyu zakayi alkawari bazata taɓa nemanta ba. Idan kuma ba haka ba zan kashe ta kuma na kashe ka” Yace yana zare ido
     Babu wasa a idon Daddy, yasan Daddy is a patient man. Zai iya kashe su a banza ya nemo wanda zai sake training irinna Hamza sannan ayi operation ɗin
   “Okay Daddy naji na amince”
   “Boy Koda wasa ka nemeta zan kashe ku baki ɗaya kowa ma ya huta.” Haka Hamza ya tashi ya rubuta takarda.
    Daddy ne ke gaya masa abinda zai rubuta, daga nan yace ya tattara kayansa.
   Hunaisa taga sun daɗe saita sha jinin jikinta, Shikam Last Don Gwaska ya hakince kamar falon gidansu yana kallo.
   Hamza ne da Oga suka fito daga daki, jakar Hamza a hannun Oga sai kuma wani Empty a hannun Hamza,. Wajen computer dinsa yaje ya tattara books dinsa na school dasu laptop da iPad.
    Hunaisa batace Jack Robinson ba saiga Hamza ya fita ko kallonta baiyi ba, shi dama ya riga ya dauki alwashin idan rabuwa tazo to fah saidai shi ya tafi. Ya gaji da ana tafiya a barsa.
   Yasa ko kallon idonta baiyi ba, abin yana masa kuna amma ya gwammace da haka da ace mata Goodbye, anan ta fara kiran sunarsa, ‘Hamza tafiya zakayi ka barni’
     Kuka ta barke dashi saita mike tsaye ta soma tafiya hanyar kofa, “i thought you Said  you love me, please ka tsaya karka tafi ka barni” yana kkua mai tsuma rai.
    Last Don ne tareta ya damke hannunta, “Ina kike tunanin zaki, ki gode ma Allah Oga baice na rakaki lahira ba”
     Kuka takeyi sosai sai Last Don ya fizge kallabinta ya kulleta da kujerar dinning. Oga shima ya fita sai Last Don kawai.
      Anan ya soma goge gidan saboda ya cire duk wani thumb print nashi, Oga, da Hamza kafin FBI suyi ram dasu.
    Hamza bayan mota ya shiga, kuka yakeyi wiwi kamar karamin yaro harda majina, a yau yayi dana sanin haɗuwarsu da Oga. A yau yasan cewa babu alheri kwata-kwata tareda Oga kuma ya ɗauki alwashin saiya dauka fansa duk daren dadewa. Yasan rabuwar su zatazo amma baisan ta haka bane.
      Oga Daddy shikuma gaba ya zauna, yana jin yanda Hamza ke kuka sai haushi yake ji, dana sanin rashin kashe Hunaisa yayi. Yaso ya kasheta sai yaga ya Hamza zaiyi ko shima zai hadiye raine ya bita.
     Hamza yana jin kukan Hunaisa daga cikin gidan, ita kam tashin hankali take gani. Ta rasa dalilin da Hamza ya yaudare zuciyarta bayan baya Santa.  Wai ace yaki kallon idonta balle suyi sallama, ashe jikinta yakeso kuma tunda ya samu dole ya gujeta.
     “Gashi ya sake ki, idan mun kai Airport zamuyi anonymous call akan kina nan” Last Don yace tareda ajiye mata takarda a jikinta.
   Gabanta ya fadi da taji harda saki, da karfin tsiya wanda Hamza zai ji tace, Hamza Allah ya isa tsakani na dakai, bazan taɓa yafe maka ba”
     Kamar saukar mashi yaji kalamanta, runtse ido yayi har suka bar haraban gidan.... Wannan kenan!






#YGG






DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now