Seventeen

4.5K 267 15
                                    

Friday.....
    
Brooklyn, NY

    Tun sanda Hunaisa tayi ma Hamza maganar aure ya soma gudunta. Abinda ke haɗasu kawai idan ya kaimata kwanan abinci ko makamancin haka.
   Aure ba abin wasa bane kuma shi bata haka yaso yayi aure ba. Shi yafison idan ya tashi aure ya aura wanda take sonshi kuma yake santa, dama ance kaso kuma a soka shine ribar aure.
    Aisha kafin ta rasu tasha jaddada mashi amfanin soyayya, soyayya mafari rayuwa ne. Duk da a lokacin bai fahimta abinda take faɗi ba sai yanzu.
    Sannan bama rashin soyayyar da Hunaisa ke masa ba zai hanashi aurenta. Shifa baya son duk wani abu da zaiyi distracting ɗinsa wajen gano wanda sukayi masa aika aika, ma’ana suka kashe kowa na cikin rayuwarsa.
     Idan ya gansu saiya tambaye su dalilin dayasa zasu raba yaron shekara sha bakwai da yan uwansa, sannan meyasa basu kashe shiba suka barshi a raye har ya faɗa cikin mugun hali.
    Da farko yana fashi da makami, yanzu ya zama kidnapper.
     Kuma shi bayason ya haihu, bawai bayason yara bane. Ah ah suna bala’in burgeshi musamman ma Suhail da Suhaila saida kuma irin sana’ar daya keyi bazai bashi damar tarawa ba.
    Bazai kyautu ace ya tara yara kuma shi dan fashi ne, idan iyayensa sukayi masa haka bazai taɓa yafe masu ba.
    On the other hand, tun bayan fitan Hamza a daki ranar dayaso yayi mata aika aika ta lura ya canza tsaf.
    Bayama iya kallonta kuma bashida wani kuzari, dukda bawai dama shi mai magana bane amma ta lura da cewa akwai damuwa fal cikin ransa.
    Wajen Isha ta idar da sallah, sai tayi Shafa’i tareda addu’a. Tana so taje ta tambayesa akan batun maganar su, tsoron sa take yi sosai kada yayi mata zuwan bazata cikin dare gashi babu aure.
   Saboda babu wanda ya taɓa abin kunya a Gidan Gwaiba ya raine shege kuma Baza’a fara daga kanta ba.
      Kuma sarai taji sanda yace mata shiba katako bane, dama idan akwai mace da kuma namiji to na ukun shedan ne.
    Babu karya amma tasan tanada kyau, batacika fari amma kuma ba baka bace chan chan. A shekara sha bakwai jikinta yaje daidai da shekarunta.
    Tanada tsawo dan madaidaici da gashi daidai misali. Abin dayafi burge mutane da ita shine creamy eyes ɗinta. Sau da dama shike attracting mutane suje wajenta.
    Mikewa tsaye tayi ta murɗa kofa, a garke tajishi kamar yadda dama ta saba. Bata bar murɗawa ba tayita dambe da kofa babu kakkautawa.
     Shikuma Hamza yana ta wajen ɓangaren da computers ɗinsa yake yana assignments. Ance suyi hacking camera ɗin Central Park sai suyi recording wani vital information.
    Tuntuni yaketa kallon wajen amma har yanzu wani abin azo a gani bai faru ba, yanayi yana hamma barci yanaso ya fizgeshi.
   Rashin sallah da baiyi ba shiya hanashi kifa kai a kan tebur ya hau yin barci. Tsam ya mike ya nufa bayi domin yayi alwala daga nan saiya fito da darduma ya kabbara sallah.
     Cikin kira’a mai daɗin sauraro na Abdullahi Abba ya wakanar da sallah shi, sannan sai yayi shafa’i da wutiri saboda barci yakeji.
    Yana cikin arzkar sai yaji Hunaisa tana dambe da kofa, da farko yaso ya shareta saboda ɗabi’anta kenan sanda suka zo sabo sabo.
    Baiyi saurin tashiba saida yayi addu’a ma’ishi sannan ya mike ya nufa inda take, dan mukullin ɗakin dake cikin aljihunsa ya ciro ya soma budewa.
    Ita kuma tana ganin ya fara budewa sai gabanta ya fara duka, yanzu bata masan ta inda zata soma magana ba.
    Kofan yana budewa suka haɗa ido saita soma ja da baya shi kuma yana kokarin shigowa. “Meye?” ya tambayeta
   Barin lebe ta somayi kafin daga  bisani tace, “daman daman... Daman tsoro nakeji, naga kamar wani abu ya gifta ta wurin window ɗina”
      “Sai kuma akace miki zuwa wajena kin tsira kenan koh? Baki sani ba ko wanda zai kubutar dake ne a wajen”
    Bata amsa shiba ta kafa mashi ido, shine yace bari yaje ya duba ya dawo. Kulle ɗakin yayi ya fita ya zagaye gidan tas baiga kowa ba, koda ya dawo baibi ta kanta ba yaje wajen computer dinsa ya zauna.
     Ganinta da yayi ba karamin tada mashi hankali ba yayi, ya saba ganinta da kayan jikinta amma yau kuma yaga gashinta, bawai bai taɓa gani bane. Kawai yau babu ihu ko wani mugun firgici a idonta sannan kuma akwai siririn murmushi wajen lebenta.
     Yana cikin kallon computer ɗinsa sai yaji ta sake murɗa kofa,a hasalce ya mike saboda wannan karon yaji haushi ba kaɗan ba.
    Ita kuma bata masan sunarsa balle ta kira yasa take murɗa kofa, kuma bataso tace masa ‘Kai’ ko ‘Ranka ya dade’
      Yana murɗawa ya soma mata masifa, “Malama nace maki babu kowa”
    “Ah ah ba wannan ba, dama akan maganar mu ta rannan nake so muyi”
   “Wani magana kenan”
   “wanda mukayi mana 2 days back”
   “Ki fito fili kiyi magana, saboda if it’s not important then i wont remember”
   Hadiye miyau mai zafi tayi saboda ta shaka, amma kuma jin haushi ba nata bane dole ta rinka binsa sau da kafa.
    “maganar aure nake nufi” ta faɗi a sanyaye harda guntun hawaye. Shiru yayi baice komai ba, asalima kare mata kallo yayi.
    Hunaisa kyakkyawa ce na bugun jarida, bawai tafi yan mata da yawa bane, ko kawarta daya gansu tare tafita kyau. Kawai she is unique ne yasa take burgeshi. Saidai kuma maganar auren yake taunawa, yasha idan yayi burus da ita ba za’a kuma zancen ba.
     Ashe wannan tafi maye iya maita.
    “Kinaso ne?” yace a sanyaye shima
   Da sauri ta ɗaga idonta ta kalleshi saita mayar kasa, ‘meyake nufi da ita ne’ wani zuciyar ta raya mata. Bata amsa shiba illa wasa da rigarta.
    “Ke nake jira, baki ce komai ba”
    “Me ma kace?” itama ta rama abinda yayi mata ɗazu.
    “Karma ki soma wasan nan dani, waye sa’anki” yace da masifa
   “Ni a ganina gwara auren koba komai zansan zaman dana keyi anan”
     “Okay gobe idan Allah ya kaimu zan zo da masu daura mana” bai jira amsarta ba ya soma rufe mata kofa, saura kaɗan kofan ya gama rufewa sai tace, “Kanada suna?”
   Shiru yayi saboda kwata kwata baiyi tunanin gaya mata sunarsa ba, “Hamza” yace.
Karap ya rufe kofar tareda saka mukulli.

****
   Jaɓi Road....
     Rayuwa ya canza ma Mermer yayi mata ɗaurin TomTom, Anty ta mayar mata da zaman gida zaman ukuba.
   Tun sanda ta dawo daga mother’s day bata sake fita ba, koda yaushe tana cikin aiki dayan bayan daya.
      Gashi kuma aikin duka na rashin dalili ne, rearranging ɗaki, kokuma tsintar tsakuwa cikin hatsi ko scolar.
   Ita Mermer abinda yasa takeyi saboda Anty tabar Daddy yana zuwa aiki. Ko saboda wannan zatayi, bataso takiyi ta hanashi zuwa yayi sanadin rasa komai nasa.
   Tun bata saba da aiki ba har ta soma sabawa, lokacin hannayenta jazur sukeyi kamar zasu fashe saboda tsabaragen aiki amma yanzu ya soma washewa.
    Shikuma Nawaz kullum saiya kirata yaji Lafianta, koda wasa bata taɓa tunanin gaya masa dalilin dayasa bata zuwa ba.
   “ganin dama” take cewa a matsayin rashin zuwanta. Saidai kuma yanzu batasan me zuciyar ta yake mata ba, tana yawaita tunanin shi Nawaz ba kaɗan ba.
  Har Allah Allah takeyi ya kirata, ita dai bata taɓa kiransa ba amma idan ya kira bata fasa daukawa. Dukda zata faɗa mashi babu daɗi san ranta.
   Tana kitchen ta gama jefa ɗan wake saboda Bilki tace shi take jin ci, ta dauraye hannu zata tafi daki tayi sallah kafin yayi tausa sai taga wani da Anty anata hira.
      Bata ko kallesu ba ta wuce hanyar ɗakinta, su kuma suka soma kallonta. “itace wannan?” yace yana Washe baki.
     Ita kuma Bilki hakima tana karkaɗa kafa ɗaya, saida ta gatsa kwakwa sannan tace, “Itace Makau”
     Shikuma Makau murna ransa saboda Kanwar baabansa tayi masa rana, a duniya bashida abinda zai saka mata dashi. Ko yan birni basu samu damar auren irin wannan tsukekiyan mace ba. Sai gashi cikin ruwan sanyi ya samu.
    Dama wani abu sai naka, saboda shi tallan kuka yakeyi a baro yana za gayawa anguwa anguwa da kasuwanni yana siyarwa. Wai yanzu shine zai zama angon Mermer, koda yake dama a dare ɗaya Allah kanyi bature.... Wannan kenan!

Gidan Gwaiba, Zaria.....
  Kowa da kowa ya hallara a gidan gwaiba saboda anan za’a daura ma Husna aure da angon ta Alhaji TK.
  Gwaggo Dija karamin tashin hankali ya kamata dataji cewa Ashafa ya gudu. Har ta fara sallami da Salati akan farin kafan yan gwaiba
   Wai ace da an saka ma yarinya aure sai wani abu ya faru, hankalinta yayi bala’in kwanciya dataji za’a ɗaura da TK.
    Su kuma dangin ango mutanen mutunci ne sosai, koda sukaje kamu basu nuna kamar badasu aka soma bikin ba. A lokacin ma kowa yasan cewa Husna bada Ashafa zata zauna ba illa TK.
   Saidai kuma ba’a yi wani tsegumi ba tunda shima yanada kumɓan susa.
    Dangin ango sun bada dubu dari na kamun amarya, mutanen arziki basu nuna tsiya ba cikin alamarinsu.
    Shima events ɗin anci ansha kuma an nare, kowa fatan Alheri yakema Husna da kuma zuri’a ɗayyiba.
    Ita kuma Hajja Zee da Tk ya gaya mata zaiyi aure bata yarda ba tasha irin wasan April fool ne. Anan ya fayyace mata komai akan an fasa aurar da Husna da Ashafa akan wasu dalilai yasa akace ya aureta.
    Anan ta barke da kuka wiwi,dukda Tk ya riga yayi mata alkawari bazai taɓa aure akan rashin haihuwa ba. Ya riga yace haihuwa nufi ne na Allah yana bama wanda yaso ya kuma hana wanda yaso.
     Idan bashida rabon samun yara koda mata dubu ya aura haka zai zauna babu komai. Haka Tk yayita bama Hajja Zee hakuri akan auren nan badan ya tozarta zaiyi ba.
    Kawai zai yishi saboda aure Raya sunnar Manzon Allah SAW ne, sannan kuma bazai iya musa ma Alhaji Yusuf Gwaiba ba.
   Anan ya bata dubu ɗari biyar ta kara jari a shagonta watau inda take sayarda kayan ɗinki. Babban shago ne wanda kowane Crystal da kuma stones zaka samu indai akwai shi a duniya.
    Sannan yace ta zaba kasar da zata tayi sati biyu, anan ta zaba China saboda koba komai zatayi siyayya na shagonta.
    Itadai addu’a takeyi Allah ya kareta daga zafin kishi da kuma aikin shedan, tasan wani abu shine zata ja girmanta. Dama girma baiwa ne kuma idan Allah ya baka ka gode masa.
    Ita kuma Lubie tana isowa daga South Africa taci karo da mummunar labari, kawai sanɗa tayida Husna suka tafi wani ultrascan clinic haka.
     Anan taketa ma Husna fada, “haba sai kace bakida hankali, bazaki wanke mahaifanki ba salan ki shiga da cikin Ashafa” sai anan Husna taga rashin hankalinta.
     Ita sam abin bai zo mata raiba saida Lubie tayi mata maganar, an gwada Husna kuma an gano akwai sperm a jikinta.
    Anan ido ya raina fata, da kanta tace ayi flushing komai tas, aikuwa hakan akayi.
   Sannan Lubie ta kaita wajen wata mai maganin mata aka haɗa mata Emergency, anyi cuwa cuwa yadda ya dace kuma an gargadeta akan kada ta yarda wani abu ya hadata da TK sai bayan sati daya saboda maganin ya amsa jikinta.
   Husna kawai gode ma Lubie takeyi saboda a duniya babu wanda yayi dacen kawar arziki kamar ita.
   Jikokin Gwaggo Dija suna zaune a falonta anata hira, yar gaban goshinta Nawwarah ke zaune daga gefenta ta rike mata hannu.
   Kowa yana mamakin yanda jininsu ya haɗu. A duniya Nawwarah batada wanda takeso bayan Iyayenta sai Gwaggo. Sannan kuma kanwarta Nafisa.
     Suna zaune su biyu sai kurmusu sukeyi bakajin komai sai sautin dariya yana tashi.
    Su kuma su Husna ana zaune a ɗakin yan mata, a gefenta Lubie ce suma suna kurmusu kadan kadan.
    Sannan sauran yan ɗakin akwai Nuwairah da kuma cousin ɗinta Hussaina yarinyar Hassanan Momee tunda dama Momee Yan biyu ce.
      Sannan Mufeeda, Kannen Hunaisa Suhaila da Safina. Sai kuma Umma hani da ummul khairi.
      Anata hira a chan tsakar gida duka yan uwa ana aikace aikace, kamar yadda kowa yasan yan zaria ta shan san faten tsaki, haka kuwa aka ɓarza rabin buhun masara.
     Sannan ga kwandan albasa mara lawashi da mai lawashi, suma su kabewa gasu manya manya sai ɓarewa akeyi. A gefe suma kayan miyane shake an ajiye.
   Nan yan uwa aka bazu anata hada hadan girki anata raha, wanda aka daɗe ba’a hadu ba ana catching up, su kuma abokan wasa(Yaran ɗan namiji dana Mace)  sai shammatan juna sukeyi anata dariya.
   Wasu kuma suna daga gefe suba hira ba suba aiki ba kawai sun shimfida tabarma wajen inuwa suna kallon kowa. Dama daga cikin abincin gidan faten kawai ne zasuyi da kansu.
    Sauran abincin kamarsu, shinkafa jollof da fried, tuwon shinkafa dana semovita etc duk anyi order daga wani kamfanin dafa abinci.
     Nawwarah ne tazo ko kallon su batayi ba balle ta gaishe su, zuwa tayi ta samu tsumma ta buɗe murfin tukunyan faten dake kan murhu. Dama Gwaggo ce tace mata ta debo mata idan yayi.
    Aiko anan ta kone, kowa nan ya bushe da dariya sosai. “maganin mara kunya kenan” Anty Zainabu maman Hunaisa tace.
    Ita kuma Nawwarah zumbura masu baki tayi ta wuce batace kala ba. Momee ne tazo wucewa taga suna dariya, anan aka faɗa mata abinda ya faru.
   Itama dariyar tayi tana tunanin wannan irin rashin hankali na Nawwarah, ta raina kowa bata ganin mutane da gashi.
   Ita kuma tana komawa ta faɗa jikin Gwaggo tana shagwaba, “kin wani aikeni gashi na kone sannan kuma abincin bai nuna ba”
    “Toh meyasa baki tambayesu ba kika buɗe tukunya kai tsaye?” Gwaggo tace tana dariya.  
     Bata amsa ba illa hura inda yaketa mata zugi. Anan wayanta ya soma ruri alamar ana kiranta.
     ‘Jalal’ kamar yadda tayi masa saving ya nuna dara dara. Bata dauka ba illa sakawa a silent. Bata san meyake so da ita ba. Ta riga ta faɗa mashi cewa tana zaria to kuma menene yake damunta dashi.
     Gwaggo ta lura da chanjin yanayinta saita soma mata magana, “Jikalle abin cikin kwan yafi cikin kwan daɗi, meya faru ne kika canza fuska? Halan mijina ke kiranki shine kike masa jan aji”
    Dariya Nawwarah tayi amma bata tanka ba, Gwaggo ce ta cigaba da magana, “Babu kyau wulakanci, idan yana sanki tsakani da Allah karki nuna masa halinki.. Kefa mace kuma wata rana zakiyi burin kema kiyi aure kamar Husna kema ki haifa, babu kyau wulakanci kinji Jikalle”
    “In sha Allah Gwaggo zan rage”
    “Ai yagewa zakiyi bama daina wa ba” Gwaggo tace tana dariya, sannan ta kai mata duka a baya, “Yar tselan uwa kawai” ta bita da ashar.
    Itama Nawwarah dariya tayi, tana jiran yanzu Jalal ya kirata taji meke tafe dashi. Ita baxata iya kiransa ba saboda bataso tayi amai ta lashe.
    Shikuma Deenie dama yazo gidan gwaiba ne yayi surprising Nawwarah amma taki daukar wayan, yaro ya samu yace mashi ya kirata.
   Dayake yara suna shakkanta saboda yanzu yanzu saita maka dan iskan duka, kuma idan uwarka tayi mata magana tayi mata rashin kunya.
  Dama Abdulrahman ne yaron Hajia Safiya babban yar gidan gwaiba. Baiyi wata wata ba yaje wajen Nuwairah ya faɗa mata tay bako a waje, idan taje akace ba ita bace saita kira yar uwanta.
     Ita kuma Nuwairah sanye take da anko na yinin biki, atamfa ne na Gwaiba wax mai kwalliyar furanni. Akwai sky blue, cream, golden da pink a cikin atampan.
     Tayi ɗaurin gwargwaro da raw silk wanda aka haɗa da atampha. Sannan tayi make up sosai, red lipstick ta saka saita saka eye-liner baki da blue mascara.
    Gashi kuma ɗinkin riga da shirt tayi na doguwan peplum har gwiwa da straight skirt.
   Koda Deenie ya hangeta zuciyarshi ta soma harbawa, soyayarta samun mazauni ya sakeyi cikin ransa.
    Tana waige waige tana neman wanda ke kiranta, baiyi saurin fitowa ba yana daga cikin mota yana kallonta, burgeshi takeyi sosai.
  Wining glass ɗin window yayi saiya ce, “Princess your Knight is here”
    Murmushi tayi masa sosai saboda gaskiya wannan ake cema good surprise, cikin rausaya ta zagaya ta dayan ɓangaren.
   Babu shakka Dr Deenie yana santa, kawai ta lura shi bai fiye san kiraye kiraye bane. Kuma idan suna session dinsu he is strictly professional, but aside that he is very sweet.
    sau biyu dayazo gidansu dataga ganshi he was very nice and sweet, kuma suna soyayya yanda ya dace.
    “Princess ɗina kinga nayi maki zuwan babu zata koh?”
  “Ah ah wallahi naji daɗin ganinka, i need it”
    “Okay mezan samu wajenki?”
    “Na baka zuciyata me kuma kake bukata” tace tana murmushi. Mamaki yakeyi idan tana abu, tanada split personality, yau tana sanshi gobe salam.
   “Banida bakin da zan gode maki, in sha Allah ba zakiyi dana sanin abinda kikayi ba, Princess i promise to love and cherish you till eternity”
     Murna takeyi wai yau hot, sexy and charming Dr Deenie yake faɗa mata irin wannan kalaman. Gode ma Allah kawai takeyi saboda shine yayi mata wannan hallarcin.
    Haka suka watsa ma juna kalmomin daya dace da zukantansu tareda daukar ma junansu alkawari sosai. Bashi yabar wajen ba saida aka kira sallah na juma’a watau na zuwan liman.
     Shi bawai yaso zuwa bane, asalima ko sallar safiya baiyi ba ranar. Nuwairah ce ta matsa mashi akan ya tafi saboda bataso yayi Missing huduba.
    Haka ya tafi tareda alkawari zuwa anjima idan suka dawo Kaduna. Shi kuma kai tsaye ya wuce Kaduna abinsa sallar ma an fasa...
    An Daura auren Asma’ul Husna da Angonta Tahir akan sadaki dubu dari, as expected mutane sun cika babu tantama. Kowa sai sanya alheri yakeyi.
    Wajen la’asar aka fara kai amarya gaban kowane babban gidan gwaiba domin yayi mata nasiha. Kamar yadda kowane amarya ke kuka haka itama tayi amma ita nata tanayi ne saboda bata san mijin da zata aura ba.
   Gwaggo Dija tayi mata faɗa sosai, sannan aka kaita wajen Ummanta. Itama tayi mata nasiha kuma tanayi tana hawaye. “karki bani kunya” abinda ta rinka jaddada mata kenan.
     Convey ɗin daukar Amarya ya iso, a cikin motar dangin uwan amarya da uba daya daya sai babban kawa watau Lubie ke ciki.
    Yanzu za’a kaita gidanta wanda daga ita sai halinta na arziki da shi kadai zai iya kwatanta.... Wannan kenan!








#YGG




DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now