Fifteen

3.8K 281 12
                                    

Hotel Seventeen...
   
    Numfashin Asma’ul Husna ya soma daukewa kamar mai ciwon Asthma, nan gaɓoɓin jikinta suka mutu tas, sake dailing number ɗin Ashafa tayi amma yaki connecting.
     “Wayyo Allah na bani na lalace” tace tareda faɗi kasa, kama gashin kanta tayi ta soma fizga kamar tayi hauka. Nawwarah ce ta tashi da sauri taje wajenta dukda daga barci take. Tallabota tayi tana mata magana, “Menene Husna? Wani ya mutu ne?”
     Bata amsata ba illa sumbatu birjik, “Wallahi baka isa ka guje niba, nida kai takalmin kaza ne
    Anan tasha jinin jikinta, ita kuma Husna tana kara karanta msg ɗin saita yanka wani mahaukacin ihu, anan ta gane cewa tashin hankalin da Husna ta shiga sanadin msg ɗin data karanta ne. Itama daukar wayar tayi kuma cikin ikon Allah tana shiga mgs sai tagani. Namiji kanin ajali, idan bai kasheka ba saiya nakasa ka.
     Salati tayi tareda sakin wayar a kasa, da badun pouch dake makale dashi ba da ya fashe saboda bugawa.
     Hawaye ya soma zubu mata tana tunanin yadda Husna ta cuce kanta, wannan abin kunyar dame yayi kama? Wai ace ango ya gudu ya bar amayarsa. Dukda bawai tana wani shiri da Husna bane amma ta tausaya mata, yanzu wannan abu daya faru ba ita kadai ya shafa ba har ilahirin yan gidan gwaiba.
  Rarrashinta Nawwarah ta rinka yi, ita ko sai sumbatu takeyi tana rapka ihu.
Su Nuwairah dake gefe suna kallo, sannan sauran masu barci suka tashi a firgice, kallonsu sukeyi suna so su gane meke faruwa.
   “Halan lafia ?” Mermer tace.
   “Dama number ɗin Ashafa ne baya shiga shine hankalinta ya tashiNawwarah ta amsa saboda koda wasa bazata gigin faɗa masu bakin zaren ba
    “Awwwn... Allah sarki! Kada ki damu komai zai daidaitaMermer tace.
   Ita kuma Nuwairah tace, “Anjima saiki sake trying”
    Matse ma Nawwarah hannu Husna tayi tana ajiyar zuciya, taji daɗi data rufa mata asiri. Dama wani abu sai dan uwanka, naka sai naka duk ɓacinsa.
      Hawaye keta gudu daga fuskan Husna, kwakwalwarta ya tsaya cak baya aiki. Zame jikinta Nawwarah tayi taje bayi ta daura alwala saboda dama bata yi subhi ba.
     Bayan ta idar saita mikar da Husna domin tana kyautata zaton batayi sallah ba. Husna ta shiga bayi tayi wankan tsarki tareda alwala.
      Daga nan tazo ta kabbara sallah, a wajen sujud tayita addu’a, daga sharrin mutum dana shedan.
    Wajen bakwai da rabi aka kawo masu breakfast, buffet ne babu abinda babu. An soya chips, plantain, doughnuts, pancakes da kuma caramel.
    Sannan ga kayan shayi, sap, fresh milk, oats da kuma hot chocolate. Saikuma su wainar kwai da kuma cabbage sauce.
     Daga Nawwarah har Husna basu ciba, sauran ne suka zage damtse suka narka abinci. Ita zulumin Husna ya zatayi da events ɗin yau tunda ango ya gudu.
    A yaune za’a yi mother’s day a Hamdala Hotel kuma jirgin karfe takwas na safe Ummanta zatabi da sauran mutanen Lagos.
    Gabanta duka uku uku yakeyi saboda Umma ta riga tayi warning ɗinta sosai kafin ta tafi akan lowering gaze ɗinta banda kwadayi. Amma tana zuwa tun ranar farko ta watsar da komai.
       Shikuma Ashafa murna fal ransa, zuwa yayi ya haɗa kayansa tas saiya saka a boot, driver ya tuka shi saboda Airport zaije.
      Bayan ya kulle gida saiya bama Maigadi keys sukayi sallama, “Oga yanzu sai yaushe kenan
    “Babu wata balle rana” Ashafa ya amsa. Ba Airport suka wuce ba direct. Malali yaje gidan kanin mahaifinsa.
    Anan yayi masa bayanin cewa bazai iya auren Asmau ba saboda wasu dalilai nashi, kuma yanzu haka Los Angeles zai koma.
      Kanin mahaifinsa yayi masa faɗa sosai kamar zai ara baki amma bai shiga cikin kunnen Ashafa ba.
    Shifa ya ɗauki alwashin idan sama da kasa zai hadu babu abinda zai sa ya aureta, haka aka gama masa faɗa ya tashi ya tafi. Bai tsaya ko’ina ba sai Airport.    
      Wannan shine ake cewa ribar kafa, wai kura taci karo da kwaɗo. Yazo business Nigeria kuma gashi ya kwasa garabasa wajen Husna.
     10am.....
    Lokacin su Umma sun isa da kuma sauran matan brothers ɗinta watau Ahmad, Abubakar da kuma Adamu. Sai kuma  sisters ɗinta su Aisha da Hadiza, kuma duka sunyi aure.
    Dama Husna ce Auta kuma akazo bikinta. Husna tana ganin Umma sai ɗari ɗari takeyi. Bayan sun gaisa saita bar wajen ta tafi chan balcony tana kokarin tunanin yanda zata gayama Umma an fasa komai.
    Wani dabara ya fado mata akan gwara taje ta faɗa ma Momee tunda tafi saukin kai, umma xata iya dukanta da girman ta.
       A daki taga Umma ta barbaza jewelleries akan gado tana kokarin zaban wanda zata saka anjima, dayake ita tayi sponsoring ɗin event ɗin.
     Hawaye ya zubo ma Husna, duk kunyar kanta takeyi. Ji takeyi kamar kowa yasan abinda tayi, a yanzu tayi dana sanin abinda tayi kuma tana kaico da hali irin nata.
      “Amarya da kanta, shigo ciki mana, kizo ki tayani zabeMomee tace da fara’anta. A sanyaye Husna ta karasa inda Momee take ta zauna, daga nan saita fashe da kuka wiwi.
     Mamaki Momee tayi sabida bataga dalilin dayasa Asmau ke kuka ba, “Asmau me akayi maki?”
    Sheshekar kuka takeyi sosai ta kasa magana, da kyar ta saisaita kanta kafin tace, “Momee ya gudu, yace bazai aureni ba”
     “Ban gane bazai aureki ba, wa kenan?” Momee tace a raxane.
   Anan cikin kuka Husna ta labarta ma Momee karya da gaskiya yadda dai baza’aga laifinta ba.
     Salati Momee tayi ta rasa ta inda zata fara magana, wannan shi ake kira babban tashin hankali. Bata ce komai ba illa zuwa inda ɗakin Umma take, sai ta ce ma sauran yan dakin su fita zasuyi magana.
    Ita dama Umma tun sanda Asmau tace zatayi aure gabanta ke fadi, sam sam ranta yaki kwanciya. Ko yanzu dataga Momee gabanta sai ras ras ras yakeyi.
  Momee ta zauna a gefen gado saita soma magana, “Hajia ina so ki sani cewa duk abinda ya faru da mutum daga Allah ne, aure lokaci ne kuma idan lokacinsa bai kaiba babu yanda za’a yi
       “Menene ya faru Maman Yan biyu?”
    Anan Momee ta labarta mata abinda Husna tace, hawaye ya soma zubo mata. Dama tasan za’a rina, wai an sace zanin mahaukaciya.
   Daga haɗuwa da mutum da sati biyu har kace zaka aureshi, jindadin ta daya shine bai bari ya aureta kafin ya saketa ba.
     Baban Husna aka kira aka gayamawa, tareda Baffa suka je gidan kanin mahaifin Ashafa domin suji daga bakinsa.
      Anan yayita basu hak’uri ya nuna rashin jin dadinsa a bayyane. Bayan sun bar gidan suna cikin mota sai Baffa yace  ma Baban Husna idan yanaso akwai wanda zai aureta nanda Friday.
    Godiya ya rinka yi sosai saboda an fitar dashi daga kunyar da yarsa ta sashi.
    Baffa ya kira Momee yace mata, “ku cigaba da biki, Husna ta samu mijidaga nan ya kashe wayar saiya danna wani number, bugu biyu aka dauka.
      “Alhaji Tahir Kurfi, kazo gidana yanzu ina san ganinka
Wannan kenan!!

Brooklyn, NY

Idonta a rufe sai addu’a takeyi, numfashin Hamza kawai takeji a jikinta, magana ta somayi kasa kasa duk a tsorace.
    “Dan Allah kada ka illanta min rayuwa, ban sanka ba kuma ina kyautata zaton banyi maka komai ba amma ina rokonka koma menene kake tunanin nayi kayi hakuri, wannan hukuncin daka ɗauka yayi min tsauri
     Ja da baya yayi kaɗan saiya soma kallon ta, mamakin ta kawai yakeyi, watau bata masan dalilin zamanta a gidansa ba? bata san cewa itace farin cikinsa ba bayan rasuwar iyayen sa? Bata san cewa ita kadai yake gani yaji daɗi ba? Bata san cewa duk wani fara’a da murmushi akanta yakeyi ba? Bata san cewa zuciyar sa bata bukatar tayi tarayya da komai ba face ita? Bata san duk abinda yakeyi yanzu dama wanda zaiyi a gaba saboda ita ne? Kuma bata san cewa laifinta bazai yafu ba!!!
     Tashi tsaye yayi yana girgiza kansa, lallai ta raina shi dayawa. Safa da marwa ya somayi cikin ɗakin hannu yana kan kugu, kuma yakan kalleta jefi jefi.
   Ita kuma tana daga zaune kafa a harde tana kuka, wannan shine ake cewa duniya tayi maka ɗaurin Tom Tom.
    Dawowa yayi ya zauna dab da ita, cikin ido ya kalleta saiya soma magana, “bari na faɗa maki abinda kika min, bari na gaya dalilin zamanki cikin gidan nan” daga nan saiya Tallabo mata gemu.
    “Hunaisa! Hunaisa!! Randa na fara ganinki kika sace min zuciyata, a ranar na kamu da ciwon sonki, ciwon da har yanzu yana addaba ta. Kece kawai zaki iya magance min wannan ciwo” ware idonta tayi sosai tana mamaki, dama santa yakeyi? Ita ko tunanin sanin sunarsa batayi ba balle wani abu daban.
     “Dan Allah Hunaisa ki fahimci ni, banyi niyyar cutar dake ba. But i don’t want to loose you, bari kiji bazan ma iya bane sabida zan shiga wani yanayi daban san shiba. Kece other half ɗina, kwanciyar raina kuma duk filin dake cikin zuciyana yanzu ya cika da soyayyarki
     “Shine ni ka rabani da wanda nake so kuma yake sona, how selfish are you?”
   “Akan so (Book ɗin habibtee Lubna Sufyan)  babu abinda ba zanyi ba, koma me zakice naji ɗin indai zuciyata zata samu abinda take so”
    Dariya Hunaisa tayi na takaici, “An gaya maka a haka ka sameni ne? Bari kaji ruhina yana tareda YaMudassir, kawai gangar jikina kake gani, kuma gwara na mutu danaso mutum irinka, mugu azzalumi kawai”
   Ranshi yayi mugum ɓaci amma tunda sulhu yake so ya hakura, “Hunaisa My love, karki ce haka, bakisan abinda Allah zaiyi nan gaba ba”
     “in sha Allah bazan faɗa sonka ba, Allah kuma ya kareni, Allah ya isa tsakani na dakai, kuma sai kaga karshen ka nan kusa” saita tashi ta dauki kwalba.
    Bugawa tayi akan bango ya fashe ratsa ratsa, cikin kuka ta soma magana, “Da na bari kayi abinda kake so akaina gwara na kasheka, nima kuma na kashe kaina kowa ya huta”
    “Ki ajiye kafin ranki ya ɓaci... Kinsan cewa wuta zaki shiga koh idan kikayi haka” maganar ta soma mata tasiri a jiki sai yayi sanɗa ya fisge kwalbar, ita kuma ya mareta.
   “bakida hankali ne? Idan wani abu ya faru dake kina ganin zan iya rayuwa ne?” daga nan ya turata kan gado ya nufeta. Ja baya tayi yana binta kamar yadda sukayi ɗazu.
    Hawaye ta somayi, “Da mugun abinda kake so kayi min ba gwara ka aureni ba...Tunda nasan cewa bazan kara ganin YaMudassir ba gashi niba fasika bace”
     Fuskanta yabi da kallo yayinda take magana, anya kuwa yaji abinda ta faɗa kuwa!
    “Da gaske kike?”
    “What do you think?’’ tace tareda balla masa harara, kallonta yayi yaga babu wasa, tashi yayi murna ransa.... Half bread is better than none... Wannan kenan!


#YGG

DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now