Thirty-nine

4K 302 43
                                    

   Barakallahu....
 
    Koda Nawaz yagama shan shayinsa saiya kama hanyar gidansu, tunanin kala kala yakeyi a hanya. Gashi da gangan bai bar ma Ama key ba. Tafiya yayi da abinsa sai tayi ta zama gidan Maman Eemad.

    Gwaggo kam tana shanya scolar tareda mita, sai faɗa takema Hassatu akan tayi sauri kafin tayi latti. Ita kuma Hassatu da gangan bataso taje irin wuya yayi kaurin nan.

    "Assalamu alaikum" Yace fuskansa da tsantsan damuwa.

   "Amin waalaikumus salam"

  "Gwaggo ina kwana"

   "lafia lau Dan Albarka, ya kwanan Ama?"

      "Lafia lau, daman maganar danazo muyi kenan"

     "Toh shikenan, bari na gama shanya"

  Wucewa hanyar ɗakinta yayi sai yaga Hassatu tanata jan jiki,"ke bazaki tafi makaranta ba sai ranki ya ɓaci" Yace da masifa

    Figar hijab ɗinta tayi ta wuce tana kumbura baki, shikam ya samo kujera ya zauna.

     Yana zaune wajen 10mins saiga Gwaggo ya shigo tana gyara haɓan zaminta. Zama itama tayi saita kalleshi.

   "ina jinka! Injin dai lafia?"

   "In lafia bah lafia" ya faɗa yana haɗe rai.

   "Toh ni duk ka ruɗani, Ama ne babu lafia koko naƙudan me yazo?"

   "Duk bashi bane, watan haihuwanta sai gobe ko jibi"

  "Toh menene kake wani sanya sanya?"

    Anan ya zayyana mata abinda Ama keyi, duk ɗiban albarkan datake masa, bai rufe komai ba harna safiyan nan"

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now