Six

5.3K 333 2
                                    

Monday 8:30am.....

Gwaiba Group, Maraban Jos....

Mermer Ibrahim.....

    Ranar dana fara ganinsa ya kasance ranar farko dana fara zuwa Gwaiba Group, watau main office ɗin company dake Maraban Jos, sunada sauran office a wasu garuruwa amma na Kaduna shi ne babba.
       Fari dogo ne, bazaka ce masa kyakkyawa ba amma babu muni a jikinsa. Faɗuwar gaba naji na rashin dalili sai kuma naji an cikani da ido watau ana kallona.
     Dagowa nayi ina waige waige inga wayake ɗanyen aikin nan, karab idona ya haɗe da nashi, bai cire nasa ba sai muka rinka kallon kallo. Sai daga baya ni na cire nawa.
     Nifa bazance banida kunya ba amma bana shayin yin wani abu, musamman ma wajen kallo da k’ure mutum. Toh fah sai dai kayi hakuri dani.
     Amma na rasa dalilin dana kasa nuna halina wajen bawan Allah nan.
    Kamar kullum sanye nake da riga da wando na jens tareda bakar doguwan jacket, kana na saka ɗankareriyan belt na Moschino a kuguna, saina ɗauki army green khaska ɗan k’arami. Abinda yasa na ɗauki gyalen saboda laushin sa.
     Jan Fashion earrings na saka tareda bracelet ɗinsu, sannan saina ɗauki jaka wanda shima ja ne.
      Ni mace ce mai san saka k’ananan kaya, idan za’a ɗirga kayana to na turawa zasu rinjaye na al’ada. Kuma idan zan saka ina haɗasu ne da takalmin sneakers, Hightop, Gladiators, Supra da sauran su kasancewar bana san barin kafana a waje.
       Saidai kuma idan na saka atampha sai na ɗauki flip flops (Flat shoes) nayi amfani dasu irin ranaku na juma’a amma ba kowanne ba.
       Ban ankara ba sai na ganshi tsaye a fuskata yana murmushi, haɗa rai nayi sai nace, “Ji wannan! Shi dawa kuma?” duk cikin raina saina juya kaina.
     “Kofar bazai buɗe ba idan baki je wancan ɗakin dake gefe ba kinyi registration” ya faɗa saboda ya lura ina ta dambe da kofar shiga main entrance ɗin.
       “Okay thanks” nace saina nufa wajen.
    Su kuma su Nawwarah tun wajen 8pm suka isa wajen, ita kadai ta tafi abinta saboda har yau bata sake ma Husna fuska ba.
    Nuwairah ce tace mata su tafi tare, babu yanda zatayi idan ba haka ba saidai ta dauki taxi which zai zubar mata mutuncinta ba kaɗan ba.
     Sun isa kuma sunyi duk wani registration daya kamata suyi sabida har an basu ID card ɗinsu kuma dama dashi zakayi amfani wajen buɗe kofa.
      Suna zazzaune a hawa na takwas cikin wani madaidaicin conference hall mai cin mutane 24, Nuwairah, Nawwarah, Asma’ul Husna, Mermer da wasu Maza guda biyu duk yau za’a fara Internship.
     Cikin ɗakin babu abinda ke tashi daga sanyin AC sai kuma kamshin turaruka daban daban saboda kowa ya kure a dakarsa ne. Mermer ce ma take tauna chewing-gum k’as k’as tana danna waya tana murmushi.
     Ita kuma Nawwarah kalle kalle takeyi na Hall din tana yatsina fuska alamar baiyi mata ba, yanda takeyi xaka zata ba ubanta keda wajen ba.
      Nuwairah koh duba wasu files takeyi dayake an basu Manual, a hankali take kokarin gane kan abinda ya k’unsa kafin supervisor ɗinsu ya zo.
      Husna kuwa YouTube ta shiga tana kallon Videos dinsu Emmanuella, babbaka dariya takeyi kyakyakya.
    Su kuma mazan anata gardama akan kwallo, Messi da Ronaldo wayafi iya kwallo, musu sukeyi kamar sun daɗe da sanin juna.
     Wani ne ya shigo cikin Office ɗin ya soma magana, sanye yake da wani koɗarɗiyan kwabɗeɗan suit wanda mutane biyunsa zasu shiga kuma yayi masu daidai.
     Gashi saiya saka wani siririn necktie, kana ganin shi kasan cewa babu gogewa a tareda shi. kansa sai shek’i yakeyi saboda ya aske komai tas. Ga kuma siririn medicated glass.

     “Good Morning everyone? Sunana Nawaz Adamu, kuma ina cikin Department na public relations ne. But yanzu zan zama supervisor dinku for now” yace
    “This is wonderful, the nerd is our Boss!” Mermer tace, dama ita tanasan kananan maganganu. Aiko nan take kowa ya bushe da dariya banda twins.
     Nuwairah saboda tasan bai dace ba, Nawwarah kuma saboda Mermer tayi joke ɗin. Thou ita bata fiye wangale baki ba cikin mutane saboda dai ita da raini basa haɗa hanya.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now