Nine

4.7K 287 3
                                    


Washe gari...
Gwaiba Manor.....

     Asabar ne kuma kamar yadda al’adan gidan yake ranar gaba ɗaya ake cin breakfast, anan ne kowa zai kawo matsalar sa daga yaran gida zuwa masu aiki.
     Sannan ana abincin sadaka da ake kaiwa masallatai da kuma gidan almajirai. Daman Baffa ya ware mashi ne domin taimaikon marasa wadantan kudi.
      Yauma anyi Buffet ɗin abinci kala kala, babu irin cuisine ɗin da babu. Daga na gargajiya harna turawa.
      Babban Dinning aka jera komai saboda karamin bazai dauka ba. As usual ita Nuwairah bata bari iyayenta su fito cin abinci kafin taje ta gaida su.
     Takan bisu ɗakin kwanarsu suyi gaisuwa cikin mutunci tareda tambayarsu lafiyan su. Sannan ta wuce ɗakin kanne ta dubasu suma.
      Anan take tada wanda basuyi sallah ba, kuma babu fashi tana zuwa ɗakin Nawwarah itama dukda wulakanci data ke mata.   
    Yau tana shiga ɗakinta taga wuta a kashe alhalin ba ɗabi’anta bane kwana babu wuta a kunne. Haka take barci da wuta k’erere.
    Sallama tayi kamar yadda ya dace idan zaka shiga ɗakin mutum kayi saita kutsa ciki.
     Ba’a amsa mata ba koda yake tasan halinta, balle yadda jiya ta rinka watsa mata harara.
    Bayi ta wuce ta kunna mata heater ɗin ruwan zafi, dama ranaki kaɗan ne bata kunna mata. Ta fito daga bayi kenan sai taga ashe idon Nawwarah biyu saidai kuma kyarma data keyi cikin bargo.
    Da sauri ta karasa wajenta, “Nawwarah habibtee meke damunki?” saita tallabo mata jiki. Rau taji kamar garwashin wuta.
     Ita kuma Nawwarah ta shaka sosai amma babu yanda zatayi, kawai shiru tayi tana watsa mata harara.
    “Tashi kiyi wanka Please ko xaki ji dadin jikinki”
     “Malama Kyaleni”
    “Nope idan na barki kika mutu wa zai rinka musguna min kuma, im going to missing that alot”
    Abin ya bama Nawwarah haushi, watau clown ta mayar da ita bata ma jin haushin abinda take mata. Haka Nuwairah ta yashe mata bargo tareda janyo ta. Dolenta ta mike tunda batada karfi.
     Ruwan sanyi ta cika cikin bathtub saita taimake ta cire kaya. Daga nan saita rufe kofan taje kitchen ta dauko coffee pot tareda mug.
      Akan food trolley ta daura tareda sauran kayan shayi kamarsu sugar, zuma da madara. Haka ta dawo lokacin yayi daidai da fitowan ta daga banɗaki.
     Yanzu ta soma jin karfin jikinta sosai, aiko nan ta watsa ma Nuwairah harara, “Oya kinyi kokari saiki fitan mu daga ɗaki koh? Riyan ya isa haka!”
     Murmushi Nuwairah tayi wanda abin yana bama Nawwarah haushi. Dama the biggest way ka bama mutane haushi baifi ka murmusa bayan sun maka rashin mutunci ba, zaifi bakanta masu rai tunda burinsu su ɓata maka rai amma aka samu akasin haka.
      “Okay twinny na barki lafiya” daga nan saita fita.
 
10am....

   Kowa ya hallara za’ayi kalaci a dinning table, Nawaz shima yazo saboda Baffa ya umarce shi. Nawaz ya fara aiki a cikin Gwaiba Investment tun kafin ya tafi jami’a.
     Lokacin yana cikin lebirorin da suke dauko auduga daga gona kafin a sarrafa zuwa kaya. Daga nan sai ya zama driver mai tuka tractor. Aiki dai birjik yakeyi na cikin kamfanin domin taimakon kansa kafin wata rana suka hadu da Baffa Yusuf a inda har hira ta kaisu yace yanaso ya cigaba da makaranta.
      Sosai Baffa yaji dadin jin haka daga bakinsa bcs yayi mashi kamada kansa sanda yake yaro. Anan ne yayi ma VC na ABU magana Watau Mustapha Abdullahi tunda abokinsa ne akan yanada candidate idan za’a yi sabon ɗauka.
     Cikin ikon Allah Nawaz bai bada kunya ba a wajen Jamb saboda 220 ya buga, direct aka bashi course ɗin dayake buri watau Public Administration.
     Cikin shekaru hudu ya gama ya dawo Gwaiba Group gadan gadan, shi yanzu a matsayin Uba ya ɗauke Baffa ba Boss ba. Thou iyayensa sunada rai amma haka ya ɗauke Baffa.
      Kafin fara aikinsu Nuwairah, Nawaz ne ke tayashi wasu abubuwa haka yasa suka shaku. Yanzu ma haka ya kirashi ne domin yaji performance ɗin yaransa saboda yaji ko sun kai munzalin da za’a basu wani ɓangaren Gwaiba su lura dashi.
      Ana zazzaune banda Nawwarah, Baffa ne ya kalle Nuwairah yace mata, “Ke ina yar uwanki?” dama mutum bai isa ya kawo mashi wargi ba. Ko Nawwarah bata isa ta nuna kiyayyanta akan Nuwairah ba idan Baffa yana wajen.
     Yanzu saiya kwada mutum da mari, Momee ne tasan da rashin jituwan su. Fuska babu annuri Nuwairah tace, “Tana kwance ɗaki babu lafiya”
   “Subhanallahi!” Baffa yace saiya mike da sauri. Cikin seconds yakai ɗakinta tunda tana downstairs.
     Ko haka ma ce masa tayi hawa sama da sauka yana bata wahala, yace zai duba yaga ko za’a saka masu lift. Shi kawai ya kasa gane lalaci irin nata. Wai ace hawa stairs bazata iya ba.
      Sun shiga ɗakin tana cikin bargo tana kwance, “Nawwarah ance bakida lafia?”saiya dafa mata kai.
      “Eh Baffa, zazzabi ne”
    “Bari a kira Doctor ya dubaki”
    “Nagode Baffa amma nasha Anti maleria, in sha Allah zanji sauki”
    “Okay babu damuwa, bari na zan tafi Zaria anjima kaɗan. I will see you later”
    “Allah ya kiyaye hanya, a gaida su Gwaggo Dija”
    “Toh” daga nan saiya tafi.
    Duk abinda akeyi Momee na wajen cin abinci, Nuwairah ma haka da Husna. Shi dama haka Baffa yake, idan mutum yana ciwo ya rinka rawar jiki yana damuwa.
     Bayan an gama kalaci sai Baffa ya kebe da Nawaz ya tambayeshi akan yaranshi.
    Bai boye mashi komai ba, ya faɗa mashi Nuwairah tafi saukin kai kuma bata nuna kanta a matsayin Yar Gwaiba while Nawwarah kusan Kullum saita jaddada masu cewa kamfanin ubanta ne kuma tana gab da koransu.
     Godiya yayi masa daga nan sai Nawaz ya tafi, Baffa kiran Dr Jalaluddeen yayi a waya ya tambaya progress ɗin Nuwairah. “Muna cikin introductory part ne yanzu, sai next week zamu fara treatment” Deenie yace
     “Okay na gode sosai” Baffa ya amsa.

*****
Jirgin Hamza ya sauko a Nijeriya a kaduna Airport. Kai tsaye chatan taxi ya ɗauka zuwa Zariya inda gidansa yake.
    Dama a Sabon gari yake zama, shima Alhaji AbdulMumini yana Sabon garin amma ba layinsu daya ba.
    Mai gadi yayi mamakin ganinsa tunda satinsa daya da tafiya kuma shida zaiyi wata shida.
    “Sannu da zuwa Alhaji” Mallam Dauda yace saiya amsa kayan hannunsa. “Yauwa sannu”
    Daga nan sai Mallam Dauda yaje ya buɗe cikin gidan tunda an bar masa makullan gidan a hannunsa.. 
     Hamza yana shiga cikin gidan saiya wuce daki kai tsaye. Dama ya riga yayi sallah a kaduna kafin ya shiga mota.
   Lafiyan gado ya bi sanadiyar gajiyar da yayi sosai. Bashi ya farka ba sai washegari watau Asabar.
      Shima kiran sallah na kofar gidansu ya tadashi, addu’an tashi daga barci yayi saiya mike tsaye tareda mik’a. Bayi ya wuce ya kimsta tareda daura alwala.
     Masjid ya wuce, anan yayi rakatanil fijr sai ya soma karatun qurani. Dama shi yanada san addini sosai yasa ko gaban gidansa ya gina Masjid.
     Mugun halinsa guda ɗaya watau taimaka ma Oga Daddy wajen fashi da makami. Haka yayita karatu har aka tada ikama na sallar subhi.
     Bayan an idar bai bar wajen ba saida gari ya soma haske, addu’a yakeyi akan samun nasaran zuwansa. Ko Oga Daddy baisan da zuwansa ba, kuma zai gargade Mallam Dauda akan kada ya sanar da kowa zuwansa.
     Inta shine ya ganta yau to zai koma inda ya fito shikenan an wuce wajen.
    Kudi yaba Mallam Dauda yaje ya siyo mashi Indomie a wajen mai shayi kasancewa yana jin yunwa. Bayan yaci yayi nat saiya mike yayi wanka.
      Sweet pants ya saka da hooded shirt duka bakake sai kuma tennis shoes. Range ɗinsa wanda itama baka ce ya shige ya tafi Gaskiya inda yaga mai Blue Hijab.
      Kasancewar asabar kuma hanyar babu kowa, haka yayi Parking a daidai layin daya ganta.
     Ya fito daga motarsa baima san me zaiyi ba, nan take he felt so stupid travelling from America to see someone da baisan komai akai ba.
     “Hamza you can do better” yace ma kansa. Bai bar wajen ba illa nade hannusa akan kirji yana rarraba ido a hankali cikin layin.
    Yayi tsayuwan kusan awa daya amma banda motoci babu abinda ya gifta. Sai kawai ya soma pacing, ya kai gwauro yakai mari.
    Duk bai ishe shiba, tsaki yaketa zabgawa kuma hannusa yana kan kugunsa. Anan ya soma kwallo da abubuwa kamar su duwatsu, ledan pure water, totuwan masara, ledan Omo da sauran tarkacen dake yawo akan titi.
     Maigadi ne yaji hayaniya yayi yawa saiya fito yaji ko lafiya. Yana kyautata zaton yara ne sai ya fito da yar sandan sa domin ya kwade na kwadewa.
     Hamza yana cikin yanayinsa na frustration saiya ga dattijon dayaga Blue Hijab suna gaisuwa da.
    Da fara’arsa ya karasa ya duka har kasa, “Ina kwana Baba”
   “Lafiya lau samari, kai kake damun mu halan?” murmushi Hamza yayi yana sosa keya.
   “Afuwan Baba ban lura ba”
   “Babu damuwa”
  “Yauwa Baba inada tambaya idan bazaka damu ba”
    “Allah yasa na sani”
   “Dama juma’a data wuce wajen azahar kafin masallaci akwai wasu yanmata kun gaisa dasu haka”
    “banda abinka Saurayi, aini banda gadi toh gaisuwa da mutane yana cikin sana’ata”
    Murmushi Hamza yayi sai kuma yace, “Su biyu ne sun saka hijabi dogaye har kasa, da fara da wanda batada wani haske.”
    “Ai sai kace min Hunaisa da Munauwara kake nema, sune kawaye masu shiga iri daya”
    “Yauwa baba su nake nufi. Toh wanda batada Haske sosai nake nema, tanada hijabi mai kalan Omo”
    “Saurayi banda abinka ina zan san kalan kayan ta. Tanada hijabai sunfi goma daban daban... Gadai gidansu Munauwara chan sai kaje”
    Anan ya nuna mashi gida na uku a layin, murna fal ran Hamza dan saida ya dauko dattawa biyu masu daraja ya bashi watau dubu daya.
      Nan ya rinka maimaita sunar Munauwara a cikin ransa saboda duk zaton sa itace mai Blue Hijab. Yana isa sai ya buga gate din da confidence.
    Mai gadi ne ya fito sai suka gaisa, daga nan saiyace ayi mashi Iso da Munauwara. Harda karyan cewa tasan da isowarshi kuma wayanshi babu charge balle ya kirata.
       Munauwara tana zaune a falo tana kallon ‘Secret Love’ a Eva+ saiga Maigadi ya faɗa mata abinda Hamza yace. Mamaki sosai taji saboda bata jiran kowa.
     Kuma ma Sweety ɗinta tana Chatting dashi balle tace shine, dama Mamanta tana daki saita sungumi hijab ta fita ta duba.
    Zuciyar Hamza ke duka uku uku har hudu hudu sabida bai masan mai zaice ba.
    “Assallamu alaikum” yaji tayi masa magana, shi dama kansa yana kasa yana tunani baiga zuwanta ba.
     “Waalaikumus salam” ya amsa saiya daga. Nan take ya gane ba ita bane saboda wannan fara sol ce while Blue Hijab batada haske. Yanzu yana kyautata zaton Blue Hijab itace Hunaisa.
     Da fara’arsa suka gaisa saiya daga yace mata, “Dama Hunaisa nake nema amma gidansu ya shige min”
    Kallonsa tayi sau daya saita kawar kana tace, “Lafiya dai koh”
   “Lafiya lau, sai alheri”
    “Amma kasan cewa aurenta ranar Talata za’a fara events koh sabida juma’a za’a daura
   Ita abinda yasa ta faɗa masa haka tasan wasu dasan dagula lissafi bazasu tuna suna san yarinya ba sai an saka mata rana.
     Nan ya soma zufa na rashin dalili, shi kwata-kwata bai ma taba kawo zancen zatayi aure ba Kokuma kila ma matar aure ne.
   Anan ya gane sakarcinsa, ko sau daya bai taba tunanin marital status dinta ba. Saisaita kansa yayi yana murmushi saiyace, “Na sani mana, dama maganar hall na events nazo muyi magana akai”
    Murmushi Munauwara tayi saboda taji kunya sosai, “Allah sarki kayi hakuri bari na kira maka Hunaisan”
     Daga nan saita wuce next house which shine Gidan. Yana ganin ta tafi saiya shiga motarsa ya fice, kuna ransa yake masa wanda rabon daya shiga wannan tashin hankalin tun mutuwar iyayensa.
     Gudu yakeyi kamar babu gobe, direct gidan Abokinsa watau Last Don ya wuce dake Gyallesu.
    Su Hunaisa sun fito sukaga babu kowa a bakin gate, dama abinka da motar zamani ba kara gareshi ba balle kaji tashin sa.
    Hunaisa kallon Munauwara tayi sai tace, “Anji kunya April fool kike min... Al’adan Yahudawa da yan Nasara”
  “Wlh ba wasa nake maki ba. I swear na ganshi tsaye da bakin range da bakaken kaya”
   Dariya Hunaisa tayi saita ce, “Bakin mota da bakin kaya, watau the devil himself ne yazo wajena”
   “Dalla matsa it’s not funny”
    “Okay naji, bari naje mai dilke tana jirana”
  
Last Don yana ganin Hamza yasan babu lafiya, Hamza baima rufe motar ba ya fita daga ciki yaje falonsa ya kwanta ringine kan rug.
    A hankali ya soma magana, “Last don kana sona?”
    Cikin mamaki yace, “Eh mana you’re like my brother” da sauri Hamza ya tashi sai yayi masa kus kus cikin kunne.
   Ja da baya Last Don yayi yace “wallahi babu ruwana. Inaaa bazan iya ba”
     Idon Hamza yayi jazur yace, “Duk taimakon da nayi maka shine zaka juya min baya. Kome ya faru zan dauki laifin”
     “Haba Hamza please ka duba me kake so muyi, it’s very dangerous. Kuma idan Hunaisa ce na Gaskiya toh wallahi Yar Gwaiba ce kuma bazan iya messing da family dinnan ba”
    “Ai bance kayi ba, taimaka min zakayi nayi abina hankali kwance.... Please man i really need ur help... Dan Allah”
   Sai Hamza yayi kneel down tareda harde hannusa alamar roko. Anan Last Don ya karaya sabida Hamza bai fiye rokon alfarma ba. Shi mutum ne da baya san raini yasa sau da dama yafi sanyi abinsa shi kadai
    Idan ya sameka ba karami bane. Dafa ma Hamza shoulder yayi saiya ce, “Karka damu Man, i got ur back. Tashi mu fara planning strategies”
   Bayan sun gama komai sai Last Don yace, "Wow Oga Hamza kenan, kana sha'aninka... A ganka a kyale ka"      sai suka sha hannu suna dariya.
    Wannan kenan!




#YGG



DIMPLΣS ce

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now