Forty-one

4.8K 298 64
                                    

    'Yan Gidan Gwaiba suna ganin ittifaƙi, daga shekara ɗaya daya wuce zuwa yanzu Allah ya jarabbace su da abubuwa da dama, abubuwan da basu taɓa tsammanin zai faru, saidai kana naka Allah yayi nasa.

    Sunyi ƙoƙari sun runguma kaddara kamar yadda kowane musulmi ya kamata ya ɗauka, walau me kyau ko mara kyau.

    Husna dai tana garƙe a hannun hukuma, kunyar datake kunya yau tasha dubunsa, gashi an kwace mata takalmi da ɗan kwali. Nan sanyi ya soma shiganta tunda tana jego.

    Su Sergent Jummai da Tanimu suka sakata a gaba sunata zagi, kowa a wajen tir da hali irin nata yake, bayan laifin kisa gashi har Adultery aka kamata dashi.

    Ita ma tana kaico da hali irin nata, banda kuka da nadama ƙarara babu abinda takeyi. Tabbas tasan cewa bata kyauta ba, tayi ma bariki mummunan fahimta.

   Bata gane abinda Hausawa sukace ba, 'Bariki lahiran makwaiɗaita, ka shiga kana dariya ka fita kana kuka' lallai Lubna ta nuna mata cewa ita yar duniya ce, tanata ingizata bata kyalleta ba saida taga kanta a hannun hukuma.

   Koda Momee tazo bata taɓuka wani abin kirki ba, kisa Husna tayi na manyan mutane. Koba Family dinsu ba, sauran al'umma dasuke mu'amala dasu zasu so a fitar masu da hakkinsu.

    Su kuma 'yan Human Rights Activists suka zo akan basa so a kashe Husna, kawai a bata life in prison ne.

   Momee dai tayi cuku cuku za' a shigar da ƙarar gobe saboda ta samu tudun dafawa, Momee ne kawai wanda taje dubata daga yan gidan gwaiba, kowa yayi nisanta da ita yanzu batada kowa sai ɓakin halinta.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now