Forty

4.1K 280 44
                                    

    Saida Husna taji sun daina motsi kafin tayi amfani da key ta buɗe, yanda ta gansu a ƙanƙame ya bala'in ɗaga mata hankali.

   Riƙe da juna ta gansu wuta ya cisu, hannun TK rataye a bayan na Hajja kuma duk a ɗurkushe. Nan ta soma kururuwa tana ihu wai ala dole taimako take nema.

    Rugawa tayi BQ inda su masu aiki suke tana neman agaji wuta yaci gidan, nanfa suka dunguma akazo kashe wuta.

   Labarta masu karya tayi, ce masu tayi wuta ne ya soma cin sasan su Hajja, shine ta samo ta fita. Sukam sunzo fita sai kofa ya rufe. Tayi juyin duniya amma ta kasa budewa.

    Anan tace masu cikin ruɗewa ta mance ba ita kaɗai ke gidan ba, kowa ya yarda da ita saboda yanda jikinta ke ɓari kuma tanata kuka. Kisa ba abinda zaka danganta shi da mutum bane balle kace itace, balle ma sau da dama wuta na cinye mutum ya bar wasu.

    Haka aka kira ambulance cikin daren suka kawo masu agaji, kafin kace kwabo duk gari an ɗauka gidan TK mai gidan Mai ya ƙone, kuma tareda matarsa suka mutu, babu wanda ya zargi Husna saboda taci bulus. Yanzu dai sun mutu sun bar mata duniya sai ta zauna tayi ta gadinsa.

    Momee tashin hankali ya kamata dataji, bama ita kaɗai ba harda ilahirin Yan Gidan Gwaiba baki ɗaya, dayake Husna yar gari ce, harda ɗakinta ta cinna ma wuta.

   Bata tsira da komai ba illa ranta da kuma 100k ɗinda TK ya bata kan ya mutu. Haka Momee ta takarta ta suka tafi Gwaiba Manor, anan zatayi takaba harta sake samun miji.   

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now