Thirteen

4.1K 270 15
                                    

Gwaiba Manor....

Ya jingina elbow ɗinsa akan murfin mota sai kuma tafin hannunsa yana wajen fuskanshi. Tunani kala kala yakeyi akan abinda tace.
Yayi zurfi cikin tunani kamar ma ya mance inda yake, kwatsam sai yaji ta fara shafa shi, daga wuya, fuska da kirjinsa. Da sauri ya rike mata hannaye yana salati.
"Husna bari mana, cikin gidanku fah kike"
"Gwara na nuna maka cewa babu wasa a tareda dani" daga nan saita soma zuge zip ɗin rigarta.
Da sauri ya tareta amma yana haka saita kwanta a jikinsa, sunyi shiru na wasu seconds a haka. Kowa da abinda yake ayyanawa.
Lubna ta riga ta jaddada mata cewa lallai jikinta yakeso amma yake kwana kwana, yasa duk wani hanya da zata bi dole tabi ta bashi.
Shikuma yana ayyana wannan abu cikin ransa, shifa sanda suka hadu da shirin aure yake santa. Saidai kuma ta canza kwata-kwata kuma ta bullo da wannan matsalar, idan baiyi wata wata ba zata iya mashi fyade.
A hankali ya zuge mata rigarta ya rufe inda ta fara buɗewa. Sai ya kuma rabata da kirjinsa kafin yayi abinda zaiyi dana sani.
Tallabo mata fuska yayi, ita kuma saita rufe idonta. "Buɗe idonki please" yace, a hankali ta soma buɗewa sai suka haɗa ido.
"Dan Allah inaso ki fahimce ni ba abinda nake nema wajenki ba kenan, tunda ban tambayeki ba ai bana so kenan"
"Watau kana nufin baka sona kenan?"
"Ina sanki yasa nayi respecting ɗinki... Please ki fahimce ni da kyau"
"idan kana sona ta abinda zaka nuna min kenan"
Dafa kansa yayi yana girgizawa, abin nan yayi mashi zuwan bazata. Bai taɓa tunanin zata iya bukatar wani abu haka daga wajensa ba.
Baice komai ba sai ya kalleta tareda lashe leɓansa, idan yace bayaso ya kasance tareda Husna ya yaudari kansa. Amma bata hanyar data ke bukata ba.
"ki bani dama na tura iyayena neman aurenki, sai ayi bikin mu nanda sati shida"
Bata amsa shiba, asalima bata kalleshiba saida ya sake maimaitawa.
"Toh meye banbancin abinda na tambayeka? Yanzu da bayan munyi aure ai abu ɗaya ne"
"Eh amma ni nafison na aureki kawai"
"ban yarda da kaiba, ji kwana biyun nan idan ban nemeka ba baka nemana" ta faɗa a shagwaɓe.
Tallabo mata fuska yayi, "Look at me please" saita kalleshi. "Kinga I'm sorry, nasan ban kyauta ba dana saka harkan aikina akan iyali na amma in sha Allah bazan sake ba"
"Okay zanma Daddyna magana" daga nan ta sake fuskanta. Yatsina fuska tayi data tuna batama masan aikin dayake yiba.
"Aikin me kakeyi?"
"ni Investment Banker ne" yace yana murmushi. Daga nan sai suka soma soyayya irin na yan zamani.

Shikuma Mallam Musa da full confidence yaje office ɗin Headmistress zai biya kudin makaranta.
Ya zauna sunyi gaisuwan mutunci sai ya saka hannu a aljihu amma yaji salam. Haka ya kara duba ɗayan amma babu komai.
Aljihun wandonsa ya duba shima baiga komai ba. Da sauri ya bar office din duk tsammanin sa yana cikin mota amma shima baiga komai ba.
Haka ya duba motan wajen driver's seat amma babu kudi, anan zufa ya karyo masa. Handkerchief ya dauko ya soma sharewa.
Jingina yayi saiya rasa inda ya zubar da kudin, gashi gari yayi zafi wannan ma bayan ya biya kudin haya shi ne ya samu ragowan.
Sai kawai ya tuna ya shiga bayi na BQ kafin fitarsu, da sauri ya shiga mota ya wuce Geneva close.
Yana isa ya fara duba bayin amma baiga komai ba, nan hankalinshi ya kara tashi. Dubu goma sha biyar babban kudi ne a wajensa.
Dama idan ya biya School fees yau gobe sai yaransa su koma makaranta bayan sati daya da suke zaune gida.
Ya bincika duk wani hanya daya bi amma baiga komai ba. Sam bai kawo cewa ko Nuwairah ta dauka ba tunda tafi karfin kudinsa nesa ba kuda ba.
Ita kuma Nuwairah sai wani sabon iyayi takeyi, gashi sai murmushi takeyi. Hakoranta wanda suke tartar sai nunawa sukeyi.
Gashi wushiryanta shima abin kallo ne, Momee saida ta jata Office ɗinta ta tambaye ta akan chan jin datayi.
"The Fairest, naga kin canza ne?"
"Eh Momee, nima na zama yar yayee"
Yake Momee tayi saboda tasan haka kurum mutum bazai canza ba saidai akwai wani abu dayayi sanadin hakan.
"Kin tabbata haka kike so kokuma akwai wani dalili da ban sani ba"
"Momee babu komai fah"
"Kinsan babu karya tsakani na dake koh baby"
Inda inda ta somayi sai tayi dana sanin abinda tayi, idan bata gaya ma mahaifiyarta gaskiya ba to waye zata gaya mawa.
"Dama wani ne" saita faɗa tana share hawaye. Dukda bata karasa ba Momee ta gane cewa soyayya Nuwairah ta fara.
"Nuwairah ki sani cewa kinada kyau yadda kike, bakiji ance beauty lies in the eyes of beholder, idan baiga kyanki yanda kike ba tofah he doesn't deserves you. You don't have to be outgoing, spontaneous or sociable... Be proud of who are no matter what, stop being insure akan sauran mutane, kowafa nada nasa insecurities ɗin amma yana dannewa... Please kada kiyi abinda zakiyi dana sani"
"Yau banma ganeki ba, kin canza kwata-kwata, kinayi kamar Nawwarah... You guys are 2 different people, please baby be yourself kinji"
Kafin Momee ta gama magana hawaye keta fito mata daga idanu, tabbas Momee tayi gaskiya. Yanada kyau mutum ya gode ma Allah yadda yake, kowa da yadda Allah yayi sa kuma babu mai canzawa.
"Okay Momee Nagode" daga nan sai aka kawo masu abinci, waina ne da miyan taushe wanda yasha nama da man shanu.
Sunci sunyi nat sai Nuwairah ta tashi zata tafi gida, Mallam Musa ta kira a waya yazo su tafi.
Koda ta kirasa yana Geneva, haka ta jirashi harya zo. Amma kuma ta lura akwai matsala a fuskanshi.
"Mallam Musa halan lafiya naga kamar ba kaiba"
"Kedai ki bari Hajia, wallahi na zubar da kudi na naira na dukan naira har dubu goma sha biyar.
Ras gabanta ya faɗi, ta tuna ita ta dauka, fuskanta sai yayi la'asar. Saidai kuma zaka sha tausayin sa takeyi, amma asali tausayin kanta takeyi.
Ina ita ina sace ma Mallam Musa kudi, mutumin dayake kokarin tallaba ma iyalan sa. Zuge zip ɗinta na jaka tayi saita fito da wallet ɗinta mai kyan gaske.
Dubu talatin dake ciki zata karbo dinki ta dauko ta bashi, tana kallon kudinsa data sace daga gefen cikin jakar amma bazata iya faɗa masa ba.
"Toh gashi kayi hakuri da wannan, Allah ya kare tsautsayi da asara"
"Haba Hajia ina ni ina daukan wannan kudin, ai sunyi yawa wallahi. Ki rage wasu dama na makaranta yarana ne"
"Haba ai kafi dubu talatin a wajena, kawai na baka sadaka ne"
"Toh nagode Allah ya kara budi" daga nan suka shiga cikin motar, gidan ya mayar da ita tunda batada kudin da zata wajen Tailor.
Dama ankon Hunaisa zata amsa amma kuma yanzu babu biki. Shikuma Mallam Musa ta sallame shi akan ya tafi sai kuma gobe. Godiya ya sake mata sannan ya tafi.
Babur ɗinsa na Yamaha ya hau ya tafi kasuwa watau Abubakar gumi central market, bakin dogo kai tsaye ya wuce. Kayan miya ya siya, robon dustbin ya taya na timatir saiya siya, tarugu da tartasai kuma a cikin roban custard.
Yana matsawa gaba saiya taya robon custard na dankalin turawa, anan ya siya tareda doya.
Dama sunada ragowan buhun masara dana shinkafa. Saiya wuce wajen masu nama, ya taya kilo na nama akace masa 1400 sai na kayan ciki 900. Anan ya yanke shawara gwara yajeda kayan cikin.
Haka yayi siyayya saboda yau koda na rana ɗaya ne suma miyansu yayi zaki.
Koda ya koma gida daga yaransa har matansa da kuma kanwarsa dake zawarci da yaranta biyu, ga kuma gyatumansa.
Kowa murna yakeyi ya shigo da leda bai dawo hannu yana dukan cinyarsa ba. Haka suka kama aiki gadan gadan.
Shinkafa da wake akayi da miya, sai aka aika makwabta aka siyo latas.
Naira saba'in ya bada yace ranar a siyo masu ledan pure water watau ranar babu shan ruwan rijiya wanda aka saka a randa. Ranar yanaso kowa yaji daɗi tareda shima Nuwairah da albarka.
Haka kuwa akayi, nan suka rinka santi kowa ya samu yanka ɗaya na kayan ciki, ga kuma latas da danyen tumatir an yanka sai ruwan pure water.
Shima for once ya shigo gari... Wannan kenan!

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now