Nineteen

3.8K 267 7
                                    

Gwaiba Manor.....


Shikuma Deenie wajen Magrib ya soma jero ma Nawwarah kalaman soyayya ta text, dayake har yanzu bai bambanta suba yasha itace ya gani ɗazu.

Ita kuma ta yaba na yabawa babu yabo babu fallasa, dayaga yanda take amsawa saiya soma dariya saboda yan Mulkin sun motsa.

Sunyi alkawari idan ta dawo gida zata nemesa, kuma hakan akayi saboda tana isa ta kirasa kuwa. Baiyi 30mins ba sai gashi yazo, saidai kuma ba ita ya gani ba.

Nuwairah ce take zaune ta wajen Parking lot tana shan iska tareda amfani da Wi-Fi tunda yafi karfi a wajen.

Ganinta yayi a parking lot yasa baima tunanin kiranta ba, zuwa yayi ta baya saiya fito mata bazata.

"Na kamaki!"

"Innalillahi" ta faɗa a razane har ta kusan faɗar da Wayanta. Shi kuma murmushi yayi saboda dama haka yake son mace fragile da ɗan tsoro ba ta rinka jarumta ba.

Dagowa tayi suka haɗa ido sai sukayi murmushi, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa.

Da kansa ya zagaya ya buɗe mata kofa, saida ta shiga ta zauna ya rufe mata sannan ya zagawa shima. Saboda yan biki yasa bazai iya shiga cikin falo.

Kallonta yakeyi yana murmushi itama ta mayar masa saidai ya lura gira a sauke gabadaya yau. Gyara zama yayi saboda ya kalle fuskanta sosai.

Saiya Kunna wutar motan domin yaga haskensa abin tinkaho ita kuma saita kawar da fuskanta tana dariya kaɗan kaɗan.

"Rowar fuskanki zaki min?"

Saiya kara matsawa dab da ita domin yaga fuskanta amma tayi amfani da mayafinta domin ta rufe da kyau. Dariya takeyi wannan karon mai sauti shima ya biye mata.

"Baya damuna saboda dazun na ganki lokacin da akwai hasken rana"

"Eh ɗin" still bata bari ya ganta ba.

Juyawa yayi ta kujerar baya ya dauko wani leda ma ɗan karin kyau. Fito da flower yellow Tulips 12 strands yayi ya mika mita, ko yanda abin ke kamshi dole ya kara dankwan soyayya a zuciyar wanda yaba balle ita da ta riga ta kafa sonsa a ranta.

Saiya Fitoda karamin kwali wanda ya kunsa gold custom ring, a tsakiya an rubuta D&N watau Deenie da Nawwarah, amma dayake Nuwairah shima daga N ya fara babu wanda zai gane.

Zai rike mata hannu amma saita amsa ta saka da kanta saboda bata san maza na riketa balle ma wajen goman dare. Abin ya zauna ɗas a cikin yatsunta.

Zuciyar ta ya soma bugawa sosai, wani zafin sonsan ya kara shiganta. Dukda yana wajen bai hana zafin data keji ba kamar gawarshin wuta. Wani siririn hawaye ya soma fito mata daga idanu.

"Meyasa kake sona?" tace da siririn murya. Shiru yayi saboda baiyi tunanin zata mashi tambayar ba.

"Bangane ba?"

"It's simple, why do you like me?"

"Ni dai nasan cewa inasonki saboda yanda kike tunanin cewa idan kika haɗa rai ko fuska zai koreni daga rayuwar ki but bakisan na samu wajen zama bane."

"I love you saboda duk yanda kike nuna cewa you're not compassionate, emphatic, or caring but deep down saida na zauna dake na gane ba haka bane, you're actually sweet, kind and gentle"

"I love you because no matter how mean kike tunanin you're, to me i really find it sweet" yace ya mata wani irin kallo mara fassaruwa.

Shiru tayi batace komai ba saboda yanda jikinta ya mutu, bawai saboda kallon ba, ah ah saboda kap Nawwarah yayi describing. Saidai kuma tana kyautata zaton baisan Nawwarah ba balle yayi tunanin itace.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now