Thirty-One

4K 280 22
                                    

   Yana cikin raraba ido ya tantance meya faru dashi sai wayarsa watau handset ya soma ruri. Cikin azama ya mike amma ya sake kwantawa saboda Sara da kansa ke masa.
      Yanaji har wayan ya gama kuka, a karo na biyu wayar ya sake ruri. Wannan karon a natse ya mike yaje wajen. Saura kadan ya tsinke saiya dauka.
    “Hello Princess!” Yace dakyar.
     “Sweety ina ka ajiye wayarka?” tace a masifance
    Runtse ido yayi saboda hayaniya is the last thing da za’ayi mashi saboda jiya ya bala’in kwaluwa da barasa da sauran kayan maye kuma har yanzu bai gama sakinsa ba. Gashi uwa uba Nawwarah abu kaɗan saita yi korafi.
    “Ban kusa ne sorry”
   “Dama inaso kaje Zaria da wakilanka da wuri saboda a riga daura mana aure kafin sister ɗina”
     “shikenan Princess an gama”
     “I love you Sweety”
     Saita kashe, shi mamakinta ya tsaya yi. Wani zuciya tana raya mashi cewa Nawwarah tana kishi da sister ɗinta ne. Saidai kuma bazai yiwu ba, Nuwairah batada gogewa da wani zaiyi kishin abin ga kuma uwa uba sata kamar yar fashi.
      Tashi yayi ya saka kayansa saiya bar Club ɗin, Hotel room ɗinsa daya kama tun biki saboda an riga an yi jere a gidansa babu halin kwana chan.
     Wanka yayi sosai kafin yaji dama dama, wani zuciya ya raya mai atleast yayi sallar asuba dukda 12pm ne balle yaune auransa. Sai kuma wani ya raya masa gwara yaje yaci abinci tunda abinci yana gabada sallah.
       Shikuma Shehu Usman suna ajiye Nuwairah sai suka wuce Zaria direct. Dama a Emerald hotel sukayi lodging shida friends dinsa.
     Anan suka soma hirar bikin da sauran su, basu suka kwanta ba sai wajen 3:45am. Shehu kam idonsa biyu baiyi barci ba, yana jiran a kira sallah yayi saboda yasan halinsa idan ya kuskura ya kwanta zaiyi wajen bakwai a makare which bayaso at all.
      Sallar asuba yana cikin sallar da bayasan missing koda bashida lafiya zaiyi a gida.
       Wajen 10am Mama ta kaimasu kalaci, wasu guys sun farka wasu kuma suna barci harda su Shehu. Babu wanda ya tadashi saboda kowa yasan halinsa. Idan yana barci koma menene ka kyale shi idan ba haka ba yanzu zaku hau sama ku faɗo.
        As expected Nuwairah tabi duk ta tadasu akan su tashi suyi sallah, idan kaki tashi kuwa ta kwara maka ruwa. Ta shiga ɗakin Nawwarah taga wasu sun tashi amma banda sister ɗinta. Dama ita yanzu kar tasan kar ne da ita, aiko nan ta sheka mata ruwa a jiki.
     A firgici ta tashi tana zare ido, aiko nan taga Nuwairah fuska a tamke babu wasa, “Dan Ubanki ni tsaran kine?”
    “Inafa zaki zama tsarana, Arniya kanwar Kim Kardashian kowa yana kallon gabas ke kin wani kalle yamma, wlh koda yaune last day da zamu zauna gari ɗaya sai kinyi sallah”
     Daga nan Nuwairah ta bar ɗakin, ita kuma Nawwarah haushi takeji ace mata Arniya kanwar Kim Kardashian, dama Momee ke ce mata haka idan an kira sallah tana nan tana kallon Keeping up with the Kardashians.
    Ita duk rintsi sai tayi Sallah batama iya barci sai tayi,, koda daga azahar ne zuwa isha sai tayi take iya barci.
       Wajen 8am suka koma gida, anan jikinsu duk yayi la’asar. Daga yau zasu bar gidan nan gadan gadan.
   Musamman ma Nawwarah sai wani ɗaci takeji a ranta ga kuma kirjinta yayi mata shegen nauyi kamar zai fashe. Mood swings take samu na rashin dalili, ita ya kamata ta samo wani fulfilment a ranta zata aura Deenie abin kaunar ta amma sam ta rasa samun farin ciki taji zuciyarta washar.
    Koda yake dama tanajin cewa ana samun cold feet a ranar aure kamar mutum ya fasa.
    Haka tayita sanya sanya har Momee tayi mata magana, anan tayi murmushi saita ce kawai zatayi Missing ɗinta ne,
   “Banda abinki ina Umaru Gwandu ina nan, da zamanin dane ai a kafa za’a je ballema zamu rinka haɗuwa jefi jefi a office”
     “Hakane Momee, please inaso ki yafe min duk abinda nayi maki wanda na sani da wanda ban sani ba” saita rungume Momee tana kuka. Itama Momee matse hawaye takeyin, “Na yafe maki babyna”
     Suna cikin haka ne sai Nuwairah tazo ta faɗa musu motoci suna jira za’a tafi Zaria ɗaurin aure. Itama nan ta shiga kuka.
   A duniya ba haka taso ba, tafison suna shiri sosai kafin su yi aure. Momee ce tace Nawwarah ta bada hakuri akan ɗiban albarka datake ma sister ɗinta. Harda bazata yiba sai tace “I’m sorry akan duk abinda nayi maki, i hope zaki yafe min kuma Allah ya baki zaman lafiya da YaShehu”
      “Babu komai twinny ni ban rike komai a raina ba” daga nan sukayi hugging juna.
   Momee taji dadi sosai dukda hakurin Nawwarah bai kai ciki ba amma tasan Nuwairah zataji daɗin jinsa sosai.

2:30 pm

      Motaci ne marasa kirguwa a Tudun Jukun dake garin Zaria, kowa ya hallara za’a daura auren yan gidan Gwaiba. An tashi daga sallar Juma’a shine kowa yazo nan.
    Masu kakaaki, sarewa, algaita suna busawa, masu kuma ganguna suna bugawa.
   Maroka bila adadin suna nan suna wasa angwaye da iyayensu. Baffa Yusuf yaga kara sosai saboda yanda mutane suka halarci daurin auren.
   Ayarin Deenie watau mutanen Gwaram suma sunzo, anyi ma Baban Deenie shima kara sosai saboda malamai sosai sun je. Yan siyasa da dama daga senators da yan Reps suma sun ma Abban Shehu kara.
      Deenie Navy blue Brocade ya saka wanda akayi masa ɗinki da bakin zare. Shikuma Shehu Farin Materials ya saka na alfarma.
       Kamar yadda Nawwarah ta bukata, aurenta aka fara daurawa, tanaji a loudspeaker ance, “An ɗaura Auren Nawwarah Yusuf Gwaiba tareda angonta Jalaluddeen Habibu Gwaram” ana ta soma shewa tana ɗaga kafada.
بَارَكَ اللَّهُ لَكَ، وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَمَعَ بَيْنَكُمَا فِي خَيْرٍ
Baarakallaahu laka, wa baaraka 'alayka, wa jama'a baynakumaa fee khayrin” Nuwairah tace ma Nawwarah
   Shashasha maimakon kiyi addu’a, kin wani soma fito kamar bamagujiya, Gwaggo Dija tace. Daga nan sai aka ɗaura auren, “Nuwairah Yusuf Gwaiba da Shehu Usman Abubakar Gwaiba”
     Anan aka rinka shela akan cewa “Hohoho ɗan gidan gwaiba ya auri yar gidan gwaiba” haba anan Maroka suka rinka buga ganga suna saka baiti akan haka.
      Yan jarida da dama sunzo kamarsu, Daily Trust, New Nigerian Newspaper, Vanguard, The Times etc. Sannan masu gidan TV kamar su AIT, NTA, TVC, Liberty, Ditv, Arewa 24 etc.
    Camera daban daban sai tashi yakeyi, kowa sai zuwa yakeyi ana masa interview saboda ya nuna cewa yaje. Ko Nawaz yaje bikin amm bai bari an daukeshi ba.
      Wajen karfe hudu akace amare su shirya zasu tafi, anan dukansu suka daburce. Kuka sukeyi sosai, Hunaisa taje bikin amma batace ma kowa kala ba.
     Kallonsu takeyi tana mamaki, musamman Nawwarah wanda za’a kaita gidan wanda takeso, ita yanzu she will give up anything Kawai domin ta kasance da Hamza.
      Anty Zainabu maman Hunaisa ne ta shiga tayi masu Tas sai suka natsu, ana ne kowa ya canza kaya zuwa Atampha dinkin riga da plain zani kamar yadda al’ada yake. 
      Falon Gwaggo aka fara kaisu, anan ta soma basu tarihin zamanin su nada, yanda suka kwana a gadon Bono da kuma amfani dasu itace da rijiya ba irin yanzu ba komai cikin sauki ne.
    “Yi nayi bari na bari, ku rufa ma maxajenku asiri, kowace mace itama da nata sirrin dama kuma mai daki ita tasan inda ya huje” anan ta fashe da kuka, su kam dama tunda suka zauna abinda sukeyi kenan.
     Ana akace ma Momee tayi masu fada, batace komai ba illa kuka, saida Baffa yace tayi magana mana ita ake jira, “Ni banida abinda zance sai Allah yayi maku albarka kuma kada ku bani kunya dan Allah, banaso ayi dani a gari”
     Baffa ne yayi gyara murya, “Da farko banida abinda zance sai Nagode ma Allah daya nuna mana wannan rana, sai kuma na biyu inaso ku sani cewa aure ba abin wasa bane, neman aljanna zakuyi kuma bazaku sameshi da sauki ba”
    “Dole akwai wasu challenges da zaku fuskanta wanda yake cikin kowane aure, tarbiyan da muka baku shine zai taimake ku wajen over coming komai”
    Ajiyar zuciya yayi tukun saiya cigaba, “Nuwairah”
   “Na’am Baffa”
   “Kece babba kuma koda akayi maki auren nan saboda biyayya kika yarda ba ke kikace kin sanshi ba, saboda haka inaso ki cigaba da biyayyar nan har gidan mijinki”
     “Nawwarah”
      “Na’am Baffa”
   “Kince kina san Jalaluddeen, to gashi an baki shi, inaso ki bishi sauda kafa. Duk me ya biyo baya babu ruwan kowa. Duk me zaki gani a gidanshi ki barma cikin ki, ki rinka rufa masa asiri.”
      “Ni yanzu babu abinda zance sai Allah ya saka maku da alheri, ya kuma baku zuria’a ɗayyaba wanda zasu taimaka addinin musulunci”
      Anan yayi addu’a sosai sai sauran dangi aka rinka masu nasiha, daga su Umman Husna, Maman Shehu, Kawu Kabiru baban Mudassir, Mommyn Hunaisa etc.
      Anty Hassana ce ta shiga mota daya da Nawwarah sai Anty Zainab sune zasu kaita Kaduna, ita kuma Umma da Hajia Safiya zasu Abuja.
   Baffa yace kada kowa ya kwana a gidan amare, yan Abuja zasu gidansu Shehu na Abj su kwana a chan sai kashegari su tafi.
     Yan Kaduna kenan zasu kwana a Gwaiba Manor.

8pm....
  Kowace amarya tana zaune a ɗakin mijinta, Nuwairah tayi Sallah ta sake gyara kwalliyarta tana jiran Shehu, itama Nawwarah tayi tana jiran nata angon.
   Nuwairah zulumi takeyi sosai saboda batasan irin zaman dasuyi ba.
    Shikuma bayan ɗaurin aure yaje yayi ma mahaifiyarsa sallama, anan ta turke shi tana kuka, rokonsa tayi alfarma akan ya rike Nuwairah da amana babu musgunawa.
     Jikinsa yayi bala’in sanyi yadda yaga tana kuka kuma hawayenta yana cikin abinda ke ɗaga mashi hankali, dandai respecting ɗin Nuwairah zai iya. Saidai yana da rules a gidansa kuma idan tabi to zasu bala’in shiri.
    Su Deenie suna zaune shida su Triplet dasu Tunde da Chike, sallar Magrib aka kira sai Su Abdul suka tashi. Kallon Deenie sukayi alamar su tashi suje Masjid.
    Kauda kai yayi kamar bai gane ba, Andulrazaq ne ya bushe da dariya, “Gaskiya Man ka rinka sallah koda sau daya ne a rana,”
   “babu ruwanka ai Inayi ranar Eid”
   “burauba” Abdulbasiq yace yana dariya.
    “Gaskiya mun barma su Chike kai, kuje chan ku karata chan”
    “Chai! Ogini Wetin? Bamaso, Munsan irinsu ko sun dawo Christianity ba suje Church ba” Chike yace yana dariya saboda yanajin hausa kaɗan kaɗan.
    “Toh alaramma saika koma chan daji ka fara bori ko bautar gumaka tunda musulmai da kirista sunce basaso”
    Anan guys suka fashe da dariya, dole Deenie ya tashi ya bisu masjid yayi sallah wanda ya mance rabon dasu haɗu for a long time.
    Halinsu ɗaya dasu Triplet koma Ace sun fishi iya bariki saidai suna sallah da azumi.... Wannan kenan!




#YGG




DIMPLΣS ce
 

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now