Thirty-four

4.1K 324 56
                                    


Assalama Alaikum, I Ainau Mardiyah AKA Yarinya Mai Dimples wish to extend a sincere apology for my long unexplained silence. I hope we can move on from this and have an awesome journey through the remaining updates, just bear in mind y’all endless love, care and support is well appreciated. For comments, observations and recommendations messages me.... Thanks once again.

******
    Haka Hamza yayita gudu babu kama hannun yaro. Thou gudu ba matsalar sa bane tunda he is an athlete Kuma kowane safiyan Allah Sai yayi koda Push up ne.
      Yana yi kuma yana jin karar bindiga daban daban yana tashi. Sanin kansa ne Oga Daddy sai yayi kokarin nuna ma Yan sanda zafin nama.
     Yayi wajen 20mins yana sharara gudu East. Abinka da dare yana kuma k’olulun daji. “tim” ya fadi kasa tareda k’undunbala.
   Ashe wani marmaran dutse ke wajen kuma bai ganiba. Nan take ya turguda kafansa na hagu. Idanunsa sunyi bala’in ja saboda azaba kawai daurewa yakeyi.
   Wajen faduwa saiya fadi akan wayarsa ya fasa screen ruku ruku beyond repairal. Daga kwance ya soma jan jikinsa saboda yabar daji balle lokacin damuna ne duk ciyayi.
     Amma ina... Zafin kafar ya hanashi cigabawa, nan ya soma karkarwa yana ɓarin leɓe. Gashi baiso ya cire takalmin kafin wani abun ya sare shi.
    Nan ya kwanta ciki daji, cikin dare tareda adduan neman agaji. Yana haka kenan saiga Faash latest recruit ɗin Oga shima ya biyo ta hanyar yana neman tsira, anan suka soma kallon kallo.
      Sukam su Oga Daddy sun tsufa a police headquarters dake Independence Way na jihar Kaduna. Rarraba ido yakeyi ko zaiga Hamza amma babu shi. Hakikan gaskiya yaron yana bashi tausayi sabida yasha wuyan duniya.
   Babu haufi yanzu ya samu sauki tunda yana kyautata zaton sune wanda aka fara kashewa. Saidai kuma harara ke tashj tsakanin Oga da Last Don sabida Oga yana ganin laifin Last ne da basuyi surrender ba.
    Shikam Last yana jin haushin Bad luck din Oga ne sabida baya binsu opération amma yau yilo daga zuwansu dashi har anyi ram dasu.
Kamar yanda ka’ida yake mutum zai bada duk wani personal belongings dinsa haka suma suka yi. Sun bada duk wayar su da kuma wani agogo ko zobe dake hannunsu.
  Sannan sun bada hula, jackets da kuma boot's dinsu. Nan aka gwamusta su cikin wani Cell dan madaidaici. Su ashirin suka fita operation amma tara kawai suke garke yanzu. Wasu sun mutu, wasu gadon asibiti sabida raunukan da suka samu. Wasu kuma kamar Hamza an fantsama daji.
   Koda Baffa yaji wannan mummunar labari hankalinsa ba karamin tashi yayi ba. Da kansa yaje police station domin a soma komai cikin idonsa. Shima Chief Security ɗinsa yana wajen. Anan ne yayi confessing da cewa an kawo tsegumi akan za ayi sata wajen azahar amma ya banzantar da abin.
  Aiko nan IG yace shima a sakashi a Cell sabida yayi serving as accomplice, koba'a ɗaure shiba dole yau yayi kwanar cell.
    Daga nan gobe zai rinka ɗaukar small information da mahimmanci. Haka yayita kuka amma babu wanda ya saurare shi.
   Shikam Alhaji Abdulmumini ana fito dashi daga cikin cell domin Baffa yace yana so yaga shugaban yan ta'adda.
   "Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un shine abinda Baffa yace, shikam Alhaji Abdulmumini sunkuyar dakai yayi alamar rashin gaskiya. Ashe tare suka tashi da Baffa a tudun jukun.
   Ya girma Baffa da kusan shekaru bakwai amma dasu Baffa yake yawo lokacin da suna k'anana. Shi Alhaji Abdulmumini ya kasance irin dolaye dinnan ne. Duk tsaransa sun tafi sakandire amma yana chan yana repeating yana canza makarantu. Gashi katon banza bai kama girman sa. Yayita shiririta kenan, sannan ya sakama Baffa ido a komai sabida Baffa ya kece masa tsara.
    Ko Langa sukeyi ya rinka saka ma Baffa kafa kenan yana faduwa, in short dai da gangan yayi planning yashe Yan Gidan Gwaiba sabida bakin ciki da hassada.
   Kunyar duniya ya kama Alhaji Abdulmumini sabida yanda ya tsaya gaban Baffa a wulakance. "Audu!" Baffa yace a sanyaye, idan ransa yayi dubu toya ɓaci. Tausayin Oga yakeyi tun da dama Hausawa sunce mai Hassada bakin cikin sa ne karshen sa, gashi kam babban ishara wajen Oga.
   "Audu a duniya mena tsare maka? Tun muna yara ka samin ido. Bagasu Saminu ba dasu Bello. Duk baka damu dasu ba saini komai ka gani nawa kana so. Haba Audu!!!"
   "Aikin banza, kana tunanin kaci wannan fadar ne? Toh bakada bokan daya isa ya zaunar dani a gidan yari. Gobe gobe zan fita" Audu ya faɗa yana yake baki.
   Baffa bai amsa shiba illa kallon IG, "First thing gobe ina so ayi trying ɗinsa dashi da yaran sa duka, su nawa ne?"
   "16 harda wanda ke clinic" wani Copral ya amsa.
  Kallonsu Oga yayi cikin mamaki saboda mutane 20 suka fita operation. Gashi baisan suwa ke asibiti ba.
    "Okay Sir ga documents ɗin Statements kayi signing, gobe gobe zasu wuce prison idan Allah ya kaimu" IG yace ma Baffa.
   "Nagode sosai Allah ya saka da alheri" Baffa yace daga nan ya yi signing sai ya tafi. Ko kallon Audu bai yi ba. "Karyan ka dangin tsiya jikan talakawa, wlh gobe gobe zan fita" Oga yayita surutai.
   Copral ne ya daka masa tsawa tareda ingiza keyarsa zuwa Cell... Wannan kenan.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now