Ten

4.8K 398 9
                                    

Gwaiba Manor....

   Sai wajen la’asar sakaliya Jalal yaje gidansu Nawwarah. Yayi mamakin ganin text ɗinta saboda bai wani daɗe da tafiya ba ta bukace ganinsa.
      Kawai abin yana nufin ya fara tasiri acikin zuciyarta ne kurum. Kananan kaya ya saka marasa nauyi, rigar T-shirts da grey jens na Balmain ya saka.
     Sai ya saka palms din Zara, hular baseball ya sa sannan ya makala tabaransa na Versace.
    Shi duk meyasa yana mashi kyau a matsayinshi na kyakkyawa, pinks lips ɗinnan rau kamar yasha lipstick. Yana tafe yana takama kuma duk inda ya gifta shi ake kallo musamman ma wajen Traffic da yayi winning window kasa.
     Anan ya tafi da idon masu kallonsa, kuma dama gashida da kwarjini nanda nan saiya cika maka ido.
      Yana zaune a falon kasa yana jiranta, yau Tv a kunne yake amma ba Manara ba. Wannan karon BBC lifestyle ne kuma ana wani Health program akan illolin shan barasa.
    Nan zuciyar sa ya lalace saboda ya lura kamar kullum ba’a ake masa idan yana cikin falon.
    Pinky ce ta fito sanye da doguwan riga sakarka, fuskanta payau babu kwalliya. Yanzu batada maraba da Nuwairah, shida farko Jalal ya zata Nuwairah ce.
    “Nuwairah ko Nawwarah?” ya tambaya fuska a tamke. Harara Nawwarah ta watsa mashi kafin tayi tsaki, gaisuwan ma an fasa.
     Zama tayi akan kujera bata kalleshiba, ita batada karfin masifa data zazzaga mashi rashin mutunci. Dama abinda yasa ta fito saboda ita tayi masa text jiya da haka zai gama zamansa ya ware.
      Aunty Madina ce ta kawo mashi Chi exotic da samosa, daga nan bayan ta ajiye saita kalle Nawwarah, “Hajia Nawwarah idan kin gama Hajia Babba tana neman ki
    Anan Jalal ya soma washe bakinsa, dama dab yake da soma bala’i. Duk daukarsa Nuwairah ce ta dauki wayar sister ɗinta tayi masa text.
      Ita kuma Nawwarah kasa gaya mashi abinda yasa tace yazo tayi, “Banida Lafia” ta faɗa a sanyaye.
    Sake kallonta yayi sai yaga ta bambanta da jiya, gaskiya ciwo bai karbeta ba kwata-kwata.
    “Sannu sweetie Allah ya kara sauki
    “Amin, thanks”
Daga nan basu ce komai ba, shi ya soma girban samosa ita kuma tana duba waya jefi jefi. Dama haka suke tadin, balle ita ba mai magana bane.
     Zaka iya tsintar kalma nawa tayi cikin hira banda ‘uhmkoUhm uhmNuwairah itama haka take amma tafi magana. Nawwarah ko saboda wulakanci bazata ce komai ba.
   Yaci ya nare sai Nawwarah ta soma magana, “Kada ka mance da maganar mu akan Nuwairah
   “In sha Allah” yace yana murmushi, itama murmushi tayi amma ko hakori daya bai fito ba. Irin na Big gals masu dariya baka ganin hakoran su.
     Yau har motansa ta rakashi which is very rare, yaji daɗi sosai kuma a ranshi yanata cewa dama ta cigaba da ciwon tunda ciwo yana sata tayi kirki.
     Yana cikin tafiya harya kai wajen gate saiga Mallam Musa da Nuwairah suna dawowa daga anguwa.
     Dama ita appointment tayi booking akan a cire mata braces ɗin hakoranta. Cikin ikon Allah an cire babu wani matsala sai dai ciwon kai data ke fama dashi.
      Gashi kuma bakinta yana mata salap kamar ba nata ba kasancewar bata saba jinsa haka ba. An bata Antibiotics sosai wanda zata rinka sha da kuma kuskure bakin dashi.
     Wani ta gani ya gifta kamar DR Deenie a cikin gidansu, “Mallam Musa tsaya” tace saita soma waige waige amma tuni ya wuce.
    “Mu tafi kawai” tace saita jingina da window ɗin motar kana ta rufe ido tana numfashi da sauri da sauri.
    Sannu a hankali ta koma ɗakinta, drawer ɗinta na magunguna watau First aid box dake bayi ta ajiye wanda ta shigo dasu.
    Zuwa tayi ta tsaya gaban madubi sosai tana kare ma kanta kallo, bude bakinta tayi saita ganshi washar. Daɗi ne ya kamata sosai koba komai mutane zasu daina kyankyaminta.
    Idan ta wuce tanajin ana kiranta da ‘Mai hakoran karfeKokuma ‘Vampire’ kuma ta tabbata shiyasa Deenie baya wani kallonta.
    Indai akan soyayya ne toh ta ɗauki alwashin zatayi komai har ta samu biyan bukatar ta. Tabaran idonta ta cire shima, bawai bata gani kwata-kwata bane, kawai sabo tayi dashi.
   Yanzu kawai zata rinka sawa idan zatayi karatu Kokuma rubutu ne. .. Wannan kenan!
 
  Asma’ul Husna abinta sai girma yakeyi wajen Ashafa, Gwaiba Wax guda biyar ta loda daga store ta bashi ya kaima Tailor.
   Sam bai damu ba, infact yanajin dadin yanda ta sake dashi cikin kankanin lokaci. Koba komai shi yake dauke mata ba wani katon banza chan daban ba.
    ‘My Woman My Everything’ yake yawan cewa, yana respecting ɗinta sosai itama tasan da haka.
      Yanzu yana jiran su ɗan saba sosai sai yayi mata maganar aure, which bashida buri dayafi ya mallaketa a matsayin matarsa na sunna.
    Ai baima san irin soyayyar da zai nuna mata ba, yanda zaiyi treating ɗinta sai sauran mata sunyi kishi da ita, daga masu aure har yanmata.
      Yauma yazo ya ɗauke ta saboda zai kaita Saloon, Exclusive beauty and Spa na Isa Kaita sukaje. Tayi kwalliya kamar babu gobe kuma shima haka.
     Kana ganinsu sai sun baka sha’awa sosai. Haka ya rakata har ciki yayi masu bayanin abinda zasu mata.
      Daga gyaran gashi, pedicure and manicure, spa, lalle etc. Bayan nan sai ya biya 15k kana ya tafi yana kewar babyn sa.
      Duk yan wajen ta burgesu, dama abinda takeso kenan taje waje ta yaki yan mata.

   1: 45mins later....
  Ashafa ne ya kira Husna, tana yauki sanye da towel ana mata spa bcs har an gama mata relaxing gashi.
     “My woman my everything, gani a downstairs na dawo”
   Langwabe murya tayi sai tace, “Baby ba’a gama bafa
    “Kai har yanzu! Gaskiya mata abubuwan ku yanada yawa
  “toh ai danku akeyi
    “Eh kuma da wannan kuma, babu matsala ina jiranki har ki fito
    “Haba Baby ba yanzu zan fito ba”
    “Karki damu, zan jira ki bcs u  worth more”
     “Okay saina fitosai kawai tayi masa kiss a waya kana ta kawar da sauri tana dariya.
   Ta shafa’a ta mance saita soma magana da mai Saloon ɗin, “Wallahi tsuntsu daga sama gasarshe na samu harda guntun yaji
     “Dan Allah!” Mai Saloon tace
    “Wallahi kuwa, kinaji na koh... Kudin banza gareshi, yanda kikasan gaɓo haka yake. Ni ina ruwana zan kwakuleshi da kyau san raina
    “Aiko ni abinda zanyi kenandaga nan sukayi shewa.
     Duk abinda suka fada a kunnen Ashafa, yaji tas. “Mai kudin banza.... Gaɓo!” yayita nanatawa.
    Jikinsa yayi bala’in la’asar yama rasa meke masa daɗi, kashe wayar yayi ya dafa kanshi akan steering.
    Haka ya jirata ta fito, tayi kyau sosai. Ya fito ya buɗe mata kofa kamar yanda ya saba, fuskanshi babu yabo babu fallasa harta shiga ciki, a hankali yake magana zuciyar sa yana masa wani irin ɗaciAfuwan baby bari na mayar da ke gida saboda kaina yana ciwo
     “Allah sarki, sorry kaji koh
    “Uhm hum’ yace daga nan bai kuma cewa komai ba.
      Ita kuma bata lura da changin yanayi ba, duk zatanta kansa ne dake sara.... Wannan kenan!

      ******

Zaria...
Amma Man ka tabbata abinda kake so kenan?” Last Don yace da damuwa karara fuskanshi
    Da Confidence Hamza ya soma magana, “Eh mana, na riga nayi making up mind ɗina
   “Please kayi tunanin da kyau, i want you to be very sure”
   “Look Last Don bana san shiririta! Nace maka abinda nake so kenan! Haba mana!  Ta ina kake tunanin zan iya samun Hunaisa idan ba ta haka ba?” ya faɗa cikin masifa.
      “My mind is set!” Hamza ya kara faɗi saiya wuce bayi dake kallon inda suke.
      Last Don tunanin abinda Hamza yakeso yakeyi, abokinsa yanaso ya buga dangerous game kuma yana nuna kamar baisan mai zai biyo baya ba. Kawai kamar yadda ya bukata zaiyi.
     Zai taimake shi amma zai goge duk abinda zai nuna shima yanada sa hannu. Sam bazai iya shiga filin yaki da Yan Gidan Gwaiba ba.
      Last Don ya dauki wayarsa ya soma kira mutane kala kala, koda Hamza ya fito ya zauna akan one seater ya canza channel baiko kalle Last Don ba.
     Tashar Discovery ya kunna yana kallon yadda mu’amulan Zaki a cikin Pride ɗinsu. Haka suka zauna shi Last Don sai waya yake da kuma text. Daga bisani saiya ce, “Man munsamu good and bad news, Wanne kake so na fara isar maka dashi
    Jiki na rawa Hamza ya juyo saiya ya kura ma Last Don ido, “Gaya min good news mana”
   “Okay the good news is zaka samu biyan bukata yadda ya dace, infact fiye ma.... Amma bad news ɗin...” daga nan saiya yi shiru baice komai ba.
     Throw pillows Hamza ya wurga mashi, “Haba faɗa min mana, ka barni cikin suspense”
    “Okay komai zai daidaita ranar Monday ne” last don yace a sanyaye.
    “Shit!” Hamza yace yana hura iska mai zafi. Shi yaso komai ya faru yau ne amma ana ce masa nanda kwana biyu.
    Dafa mashi kafada Last Don yayi sai yace, “Don’t worry, komai zai daidaita
    “Ba komai na gode
Anan Last Don ya cigaba da wayanshi akan sun amince a fara plan ɗin gadan gadan.
    Kwance Hamza yayi murna fal ranshi babu wani abu dake damunsa, da farko baisan meyake so wajen Hunaisa ba amma yanzu yasani tsab.
     
   Hamza da Last Don sun kasance aminan juna, asalin sunar sa Tijjani kuma duk a cikin masu ma Oga Daddy aiki Hamza yafi aminta da Last Don.
    Last Don shine head ɗin operation watau masu fita fashi da makami cikin tsakar dare. Ya kware sosai a tare hanya kuma da shiga gidan attajirai.
     Yanzu haka yayi heading operation 57 kuma yan sanda basuda leads akai, dama Hamza shike masu hacking da sauran su.
    Wani abu kuma akan Last Don shine yanada connection, shi yana aiki da banki ne da rana saboda haka bazaka zargeshi ba.
    Kuma gashida gemu irinna ustazai, wandon sa a sama kamar yanda Manzo SAW ya wajabta ma maza. Shima kamar Hamza yake baya wasa da sallah.
  
   4:30pm...
  Sun dawo daga Masjid ana tafe ana danna counter, dama hannayensu baya rasa irin wannan abun.
   Kitchen Hamza ya shiga ya dafa masu Indomie wanda aka saka sardines da kwai.
    Sun kora da kwalba biyu biyu na coka cola sun kayi gyatsa, daga nan Hamza ya fito da chocolate na Twix yana ci, dama shi yansan zaki kamar mace.
    Sai wajen shida da kwata suka mike tsaye suka soma shiryawa. “Xaka iya kuwa? Ko zaka bari naje na dawo” Last Don ya fada cikin damuwa.
   “Dole naje sabida matsala nace” Hamza ya amsa.
    Leather trousers suka saka bakake kirin sai suka saka bakin vest sannan suka saka bakar jacket, na Hamza babu kwalliya amma na Last Don akwai su zip wani anyishi a buɗe dan gayu.
    Takalmin boots suka saka shima baki na alfarma wanda ya wuce k’aurinsu da nesa. Sannan suka saka safar hannu da kuma bakaken helmet.
    Sun sauya kamaninsu sosai koka sansu idan ba magana sukayi ba baka ganewa. Hamza ya dauki wani sledgehammer ya cire plate number ɗin motarsa na gaba dana baya.
   “ka fara kwarewa” last Don yace da wani muryan mace, dama disguise ɗinsa kenan. Yayi magana kamar mace, so da dama idan Yan sanda sun tambaya wanda aka ma sata description sai suce ai shugaban su mace ce.
    Ana mamaki sosai kuma ana fatan a kamata.
   Sun isa Gaskiya daidai layinsu Hunaisa, chan kasan layin suka parking suna jira gari ya sake duhu.
    Shikuma Mudassir sai mugayen mafarki yaketa yi kwana biyun nan, ko yau dayayi barcin rana saida yayi.
    Buga motarsa yayi ya tafi gidan matarsa watau Hunaisa, a ciki yayi parking kuma su Hamza sunga shigan mota cikin gidan.
    Bayan su Hunaisa sun gama zantawa kuma ta jaddada mashi lafianta lau, vedio call yace zasuyi anjima saita ce masa batada kati.
     “Muje bakin titi na siyan maki koh daga nan na sake ganinki da kyauYaMudassir yace.
   Babu musu ta ɗauki hijabinta, kuma coincidence blue ɗin da Hamza ya santa dashi kwanaki shi ta maimaita.
    Suna fitowa Hamza ya ganta, kuma ga wutan lantarki a bakin gate, babu tantama itace.
    “Gata chan” ya faɗa
   “Ah toh ai ta rage ma kanta wahala kuwa data fito” Last ya chapke. Dama zasu shiga cikin gidan ne ya dauketa da karfin tsiya, kuma shi LD baya wasa kana kawo mashi wargi zai bindige banza.
     “Stick to the plan” LD yace saiya tada mota, su YaMudassir ana tafe ana raha sai sukaga bakar mota ta dunfare su.
    Motar na isa su Hamza suka fito da sauri, bindiga LD ya kwada ma YaMudassir sai Hamza ya dauki Hunaisa.
   Cikin seconds suke kokarin aiwatar da abin, nan Hunaisa ta soma shure shure tana ihu tareda bige bige amma ya turata seat ɗin baya ya kulle.
   YaMudassir ne ya mike da sauri ya kama Hamza da dambe tareda shakeshi ta baya, kuma ya danne shi yanata duka.
    Abinka da anguwar masu dashi kowa abin gabansa yake lura da, babu ma wanda yasan anayi.
   Da kyar Hamza ya samu ya tureshi amma YaMudassir ya dawo tareda hamɓarinsa a cikinsa. LD yana daga cikin mota Shikuma yana kokarin saisaita Hunaisa dake shure shure.
   Yaga mata hijab ɗin yayi saiya wanka mata mari, sannan ya dauko masking tape ash masu kwarin gaske ya danne tareda kulle mata hannu, kafa da kuma baki.
    Yana fitowa anata fafatawa da YaMudassir kuma suna dukan juna babu tantama.
   “Dam” karar bindiga ya tashi, LD ne ya harbe YaMudassir a cikinsa, a razane Hamza ya matsa saboda shima ya tsorata.
    “Karka bata min lokaci, zo mu tafiyace tareda komawa wajen driver.
    Haka ya shiga suka tafi suka bar YaMudassir a kwance, jini ke fitowa daga bakinsa, ga kuma na cikinsa. Idonsa ya firfito baya ma iya ihu, kawai numfashi sama sama yakeyi idanun sa suna kokarin rufewa.
    Hunaisa suma tayi daga razanar bindigar, dama tun ba yauba takejin mugun abun kamar zai faru da ita.... Wannan kenan!



#YGG


DIMPLΣS ce


   Please don't forget to like, comments and share with your friends 👌

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now