Four

5.7K 354 10
                                    


Nawwarah tayi mamakin ganin yadda Nuwairah ke takawa, though tasan ta saba amma yadda taga tayi wani kwalliya harda saka lipgloss batayi expecting ɗinta ta taka ba.
     Har tayi nisa saita tsaya, maganar Momee ke dawo mata. “wanda ya yanke zumunci Allah zai yanke dashi”
    Sam bata san fushin Allah, reverse tayi ta koma domin ta dauko ta, badan ita zatayi ba saidai kuma dan Allah kuma kada Momee tazo wucewa ta ganta saita saɓa mata.   
       Nuwairah ta saka earpiece abinta tana tafiya sai taga motar Nawwarah ya danno kai, watau sabon motar da aka basu last week saboda graduation dinsu.
     Vintage Aston Martin Gualling ne motar, komai iri daya saboda Nawwarah tace baki takeso, ita dama Nuwairah batada problem.
     Kiiiiiii alamar karar mota ya tsaya babu birki, gashi kuma ta nufota kamar zata kadeta, saida ta tsorata taja da baya. “Haba Nawwarah meye haka, so kike ki nakasa ni?”
     Bushewa da dariya tayi sosai tana ɗaga gira, abinda tayi yayi dadi sosai.
   “Nasan yanda ake nakasa mutum kuma ba haka bane, tsorata ki kawai naso yi inji dadi” ta faɗa da smug face.
    Harara Nuwairah ta watsa mata cikin glasses ɗinta saita ce, “Congratulations kinyi abin arziki, oya tafi ki ban waje” saita ratsa gefen motar ta soma tafiya.
    “Ke karki kawo min iskanci, ki shigo mu tafi” ta faɗa a hasalce. Juyowa Nuwairah tayi tana mata kallon mamaki. Washe baki tayi wanda ya nuna silver braces ɗinta, saita soma tafa hannayenta.
     “OMG! Banji da kyau ba, Nawwarah Yusuf Gwaiba aka NYG aka Pinky yarinya yar gidan gwaiba mai ji da kanta ce tace na shiga motarta. Please someone should pinch me saboda mafarki nekeyi”
    “Idan zaki shiga ki shiga, stop acting like the idiot that you are” ta faɗa in a frustrated manner tareda zare ido.
    “Zan shiga tunda Twinny na ta matsa” saita yi hanyar kofar dayan ɓangaren.
     “Karki kara kirana sunar nan, nadai faɗa maki”  ta faɗa a k’ule.
   Three minutes sukayi sai gasu gaban Désolé, “Oya fice min daga cikin mota kafin wani yayi zatan na sanki da gaske ne”
     Ba musu ta sauka atleast an rage mata hanya, shiga ciki ba matsalar ta bane, kuma Department dinsu yana gaba kafin nasu Nawwarah.
     “Thanks siste.....” bata karasa ba Nawwarah ta fige motarta tayi gaba.

11: 26am....

   Lokacin su Nuwairah sun gama exams, kowa ya fito anata daukar hoto. Masu kananan jukebox suka fito dashi anata rawa wasu kuma speaker ne daga mota.
   Wakar tsoffin mawaka watau Style Plus suka saka. Kowa sai rarewa yakeyi kamar haka, “Four years don waka, we still dey carry go nobody waka nobody go solow”🎶
     Sunayi suna watsa ma juna champagne masu ɗankarin tsada da kuma glitters multi colored a jikinsu.
     Kowa na wannan abun banda Nuwairah, babu wanda ya kirata tazo suyi hoto. Tana daga gefe sai burgeta sukeyi. Ta washe baki hangangan baka ganin komai sai karafai shake kamar zata cinye ka.
    Gashi saboda wannan ranar yasa tayi dan kwalliya batayi normal dressing ɗinta ba, yanda suka watsar da ita koda Milan Fashion week ta dauko ta saka a jikinta bazata burge suba.
     Ta tashi zata tafi saboda driver yazo picking ɗinta kuma appointment ɗinta wajen Doctor Deenie karfe sha biyu ne.
      “Zo muyi hoto” wata yar ajin su Nuwairah tace mata, murna fal ranta saita soma tafiya zuwa wajen. Har zata shiga cikin formation ɗinsu sai yarinyar ta dakatar da ita. Kallon raini tayi mata kana tace,“i meant to say, zo kiyi mana hoto”
      la’asar jikin Nuwairah tayi because har ta fara murna atleast zatayi hoto da yan class ɗinsu tunda yaune rana ta karshe.
    “Okay ba damuwa”
   “Hope dai kin iya amfani da camera ɗin” yarinyar ta faɗa cikin isgili.
     “It’s a Cannon!” Nuwairah ta faɗa saita ɗaga gira. Mamaki ya kama yarinyar saita wuce tayi posing tareda sauran friends ɗinta.
Ta kashe masu wajen kala ashirin saita tafi, “MERMER amma bakida dama, ji abinda kikayi mata” wata daga cikin su tace.
    Gaba ɗaya aka bushe da dariya, ita kuma Mermer tace, “Bahaushe yace ina sane, wai karuwa ta taka matar aure. Ba sis din Pinky bace?”
     Sai kowa suka fara weird faces tareda rarraba ido ko zasu kara ganin Nuwairah, “Dama ance Pinky twins ce amma ban taba ganin taba, ashe mai tabarau itace sis ɗinta” wata daga  cikin su tace tana latsa waya tareda taunar chewing gum, kas kas kas.
     “Amma Pinky anji kunya! Wannan ne yar uwanta daman?”wata kuma ta amsa
   “kunyar me? Bayan babanta ne Alhaji Gwaiba” Mermer tace.
    “Eh haka ne fah” sauran suka amsa.
A cikin Désolé, Yan mata biyu ake yayee, da Mermer sai Pinky. Ita Mermer yar sarauta ce. Babanta shine Yarima mai jiran gado a garin zazzau.       Kuma yanzu haka shine GMD din NNPC, su biyun rivals ne basa jituwa. Koda yaushe Pinky take cin awards ɗinsu most beautiful, classy and expensive.
     Last year sai Mermer ta fara zuwa da Lamborghini, toh ta cije kowa dole aka bata awards ɗin Pinky.
      Gasa sukeyi sosai kamar babu gobe, idan yau wannan taje eatery taga ɗayan, to zata siyan ma kowa abinci dake ciki.
     Haka itama ɗayan zata daidaice wani lokaci ta rama, gashi ko gaisuwa basu taɓa yi ba balle magana. Kowa ji da kanshi yake yi.
      Da yar sarauta da kuma yar masu kudi ake fafatawa. Saidai kuma abinda yasa Pinky ta kara tsanar sister ɗinta kenan saboda ba’a cika masu abu ba. Ita Nuwairah idan an tambayeta takan ce albazaraccin yayi yawa.
    Nawwarah bata ɓarin naira yadda ya dace, ita kuma Mermer ita kadai aka haifa, duka kudin gidansu sai yadda tayi. Thou a haka ma Nawwarah ta kece ma Mermer tsaya, kawai dan tazo da Lamborghini ne, amma kowa yasan idan za'a nuna babba sai Dan Gidan Gwaiba.
       Abinda yasa Mermer tayi ma Nuwairah haka baifi yanda jiya Daddynta yace wai zata fara Internship a Gwaiba Investment ba ranar Monday.
       Daga nan yace mata akwai ‘yar Alhaji Yusuf a class dinsu, dama Nuwairah ta daɗe tana mata kamada Pinky amma yadda Pinky keda gayu yasa bata taɓa dangantasu ba saida ta ganta ɗazu.
        Yanzu rivalry ɗinsu zai karu saboda zasu rinka haɗuwa tare tunda waje ɗaya zasu rinka aiki. Saidai Pinky zata shiga uku a wajen Mermer saboda zatayi using sister ɗinta tayita musguna mata.
        
*******

Ita kuma Nawwarah dayake bata wani ci abinci ba jiya, koda safe kadan taci yasa tana exams tana tunanin abinci.
     Koda ta gama ta fige motarta zuwa 9-11 dake Unguwar Rimi domin ta siya Shawarma, tanata sauri sauri jikinta yana ɓari saboda Ulcer ɗinta zai tashi.
       Sauri yakeyi shima zaiyi grabbing burger kafin ya tafi aiki, yanada appointment da patient wajen 12pm. Baima lura da kowa a gabanshi ba yana tafiya wajen motarsa bayan ya siya.
      Kawai bangaje mutum yaji yayi kuma duka burger ɗin ya zuba a jikinta.
     “Innalillahi are you crazy? Baka gani ne?” Nawwarah ta faɗa tana kokarin karkaɗe jikinta. Ko kallon shi batayi ba, gashi jakarta ya tarwatse a kasa komai ya zube.
     Dukawa kasa yayi ya tsince tas, ya mayar da komai saiya mika mata, “Here you go” yace saboda sam zaginsa datayi bai bashi haushi ba. Thou yasan bata kyauta ba amma ya bata mata kaya.
      Balla masa harara tayi saita fisge jakarta ta wuce ciki, da sauri ya bita yana kokarin mata magana. Shi dama irin matan dayake so kenan.
    Yaga mace well dressed da kuma attitude, baya san naive women at all ko masu abu kamar rakumi da akala.
     “Please Kiyi hakuri, im so sorry”
   “Well you should” ta faɗa bata kalleshiba, tana tafe tana swaying jikinta.
     “Im Jalaluddeen by the way, but zaki iya kirana Jalal for short”
     Cak ta tsaya, sai ta juya ta fara kallon sa, sama tayi da idonta saita mayar kasa kuma. Saida ya tsargu amma ya dake.
     “Okay Jalal, sai anjima”
“Wow playing hard to get koh? I like it Sosai”
   Wurga idonta tayi gefe batace komai ba, saidai idan ka kalli bakinta zakaga murmushi kadan kadan.
     “Please bari muyi breakfast tare tunda i was clumsy with mine”
    “okay fine” sai suka wuce ciki, Shawarma sukayi ordering sukaci wanda akayi da kaza, shi double sausage yasa cikin nasa.
     Bayan nan sai Nawwarah tayi karab ta biya, babu yanda baiyi ba amma taki, abin yayi mashi zuwan bazata saboda baisan mata aje wani waje dasu su biya ba, kullum jakarsu kamar kwalta yake baka ɓanɓanran komai daga ciki.
        Sunyi exchanging contacts daga nan sai kowa ya kama gabansa, murna fal ransa saboda ya samu classy babe of his choice.
     
******

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now