Season Finale, Episode 43

7.2K 437 69
                                    

Bayan kwana biyu....

    Shaƙuwa ne mara misaltuwa tsakanin Mermer da Nawaz, koda yaushe suna cikin chatting, walau whatsapp kokuma text msg. Inba shiba to suna tareda juna cikin nishaɗi.
    Cikin kwana biyun nan Nawaz ya kasance cikin wani jin dadi da kwanciyar hankali, itama kanta Mermer ɗin. Ama kam abin ya bala'in baƙanta mata rai.
   Duk wani hanya datake bi ta takalo shi ta rasa, baya bata dama ta ɓata mashi rai kwata kwata.
   Shikam kowane yamma idan ya tashi aiki kafin Maghrib yana biyawa gidansu Mermer, tarba mai kyau take masa cikin mutunci da arziki.

   Nan zata kawo masa abinci da ruwan sha, kuma zata tursasa shi koda kaɗan ne yaci. Shikam yana nuna baya so yace bawai dan baya jin yunwa ba. A'a kawai dan ya girmama Ama a idon Mermer kafin ta raina mashi mata.
   Itama ta san cewa kila tana takura masa ne tunda yanada mata, amma kawai taga abinda ya dace kenan. Tarairayan sa take kamar ba ita ba.
   Abin yana bashi mamaki sosai saidai kuma ya burgeshi. Haka yauma ya tafi wajenta, dayake sunyi waya kuma tasan da zuwanshi.

    Kwalliya tayi sosai ta fito a sunarta. Atamfa ta saka mai furannin sannan kuma kalar hoda da ganye. Ya bala'in fito da ita saboda ɗinkin fitted riga da skirt ne
     Gyale na kalar hoda ta saka da takalmi, sannan ta sheƙa kwalliya a fuskanta. Nan taje wajensa tana rausaya, shi kuma ya tsaya kallonta ya shafa'a cikin tunani baima san ta isa wajen ba, saida ta snapping yatsunta a iska sannan yayi firgit ya dawo.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now