Twenty-five

3.6K 314 37
                                    

Jaɓi Road....

Yau Asabar saboda haka Daddy baije ko'ina ba, suna zaune da Bilki suna karta a falo.
Baka jin komai sai 'pick 3' ko 'General Market' sunayi suna babbaka dariya.
Itako Mermer tana upstairs tana goge goge dasu shara, dama aikinta kenan kullum sai tayi mopping gidan tas.
Bawai Bilki batada mai aiki bane, a'a ta koma mai zuwa cefane ne saboda bata yarda da Mermer akan inta fita zata dawo ba.
Mermer ta gama gyara ɗakin Bilki wanda yake cike da kazanta, duk su wanduna a kasan gado ko gefe an saka an cire ba'a kawar ba.
Sai kuma su abin goge kunne masu datti shake akan mirror da kuma cotton bud. Da kuma ɓawan kankana da abarba wanda tasha jiya bata kawar ba duk kwarin zaki kanana ya fara yawo akai. Haka tabi ta gyara tsab, ɗakin Daddy ta nufa.
Kamar yadda ta saba idan zata shiga cikin ɗaki koda mutum koba mutum sai tayi sallama.
Tana shiga ciki ta soma gyarawa, babu wani datti tunda Daddy yanada tsabta. Tazo wucewa saita hange wani bakar leda an cusa wajen kusurwa ta gefen pillow.
Zuwa tayi ta dauko, abinda ta gani ya girgiza ta, an chukurkuɗa ledojine kuma laya ne kala bakwai a ciki. Wanda aka nade da jan zare da kuma bakake, sai kuma gashin mutum wanda aka soka allura tareda wasu kullin garin magani.
Ita kuma Bilkisu tana cikin karta saita tuna cewa yau bata kawar da kullin da Daddy ke kwana akai ba, da sauri ta ruga sama. Aiko nanta banka cikin ɗakin kamar zata karya kofan, haki takeyi kamar karyar Maguzawa.
Wuf ta kwace ledar daga hannun Mermer, "Yo nifa tsidibi da gulma ne banso ubanwa yace ki buɗe"
"Yi hak'uri nasha datti ne"
"Yo munafuka kin gani ai, sai ki wuce kitchen ɗina yana san gyara"
Haka Mermer ta tafi tana addu'a saboda ganin abin, ita kuma Bilki citsan yatsa tayi.
Dama ya kamata ta koma wajen Tsanani ta kai mashi maintenance fee, haka ta koma wajen Daddy dake jiranta su cigaba.

'Yan Gidan Gwaiba (Completed) Where stories live. Discover now