01 Soyayya

5.3K 260 6
                                    

WATA SHARI'AH😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

   Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jink'ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, tsira da aminci su k'ara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammadu (SAW) tare da Alayensa, na godewa Allah mai kowa mai komai da ya ba ni damar sake kawo muku wannan labarin nawa.

    Wannan labari mai taken wata shari'a fiye da rabinsa ya faru da gaske, na yi ne domin fad'akar da masu hali irin na jarumar cikin littafin, ina fatan za a amfana da abin da za a karanta a cikinsa, ina kuma fatan za ku ji dad'inshi.

     Jinjina, godiya, bangirma ga uwa mabada mama, k'ungiya mai albarka Nagarta Writers Association, fatana a kullum Allah ya k'ara d'aukaka mana ku, Allah ya k'ara baseerah, hikima, ilimi, hazak'a da kuma zak'in hannu.

    RAZ da ku nake tak'ama da tink'aho a kodayaushe, da bazarku nake taka rawa, bani da kamarku a duk online writers, Allah ya bar zumunci ya barmu tare.

     Sauran masoyana na duk fad'in duniyarnan ina k'aunarku kuma ina alfahari daku, inama ace baki zai iya lissafoku baki d'aya? Aikuwa dana zage damtse wurin jera suyenku tare da sanar daku kaf sak'unanku suna isowa gareni, saidai kuma kash! Ba abune mai sauk'i ba saboda yawanku, saidai ince nima ina k'aunarku kuma ina alfahari daku.

    RAZ NOVELLA one and two ina godiya gareku, Allah yabar minku da soyayya da k'auna.

********************************
                  {~1~}

    Yammaci ne mai cike da ni'ima,
    iska na kad'awa ta ko'ina, ganyaye sunyi tsanwa shar abun gwanin ban sha'awa, sama tayi luf da hadari kwance a cikinta, ko'ina yayi tsit babu ko kukan tsuntsaye, kowa ya ladaftu a gidansa dan gudun saukowar ruwan sama.

      Tuk'i yake da k'arfin gaske kamar mai shirin tashi sama,
     Daga gefenshi (kujerar zaman banza) wata mace ce ta hakimce fuskarta sanye da dark glasses, kyakkyawace ajin k'arshe, tanata taunar chewing gum cikin natsuwa take kallon yanda namijin yake sharara gudu abunshi.

    "Dan Allah Honey ka rage gudun nan da kake, ka bimu a hankali mana" ta fad'a bayan ta zare glasses d'in dake idonta.

    "Ai dolece tasa kikaga ina gudun nan Sultana, bakiga yanda saman take bane? Ina gudun kar ruwan sama ya saukone, kinsan watan August ruwan sama baya alerting kafin yazo saidai kawai aganshi yazo, kuma da k'arfi yake zuwa yanda dole sai munyi parking har sai lokacin daya tsaya sannan mu tafi" ya bata amsa still yana shararar gudunsa.

    Shiru tayi bata kuma fad'in komai ba, ganin ya k'ara yawan gudun da yake yasa ta sake maimaitwa,
    "Abban Hafsa dan Allah ka rage gudun da kake, kasan fa bana son gudu da mota saisa kakeyi".

   Bai ko kalleta ba yaci gaba da tuk'inshi.

    "Nikam wai kodai duk cikin fushin nayi winning d'inka a shari'ar yaune yasakaka wannan gudun tsiyar? Nikam karka zubar damu garin fushinka".

   A fusace ya rage gudun motar ya koma tuk'ata slowly,
    "Sultana an fad'a miki wai naji haushine dan kinyi winning d'ina shari'ar yau? Kika sani ma ko da gangan na barki kikayi winning d'in nawa dan na ganki sabuwar lawyer ne?"

    "Kaidai fad'i gaskiya Honey" ta fad'a cikin zaulaya tana masa dariya.
    "Kaga ai gashi yanzu nasa ka rage gudun ko? Inda ace ban maka hakaba da yanzu kana nan kana sharara gudu damu".

    "Au! Haka kika fad'a? Zakija inci gaba daga inda na tsaya kuwa" ya fad'a yana k'ok'arin cigaba da gudunshi.

    "A'a nidai dan Allah kayi hak'uri tunda ai mun kusa isa gidan ma".
   Tana gama fad'in haka kuwa ruwan sama ya sauko da k'arfin gaske mai had'e da iska sosai,
   "Kinga abunda nake fad'a miki ko? Inda kin bari baci gaba da gudun aida tuni mun isa",
    "Ehh nidai na yarda kabi a hankali d'in koma dai yaushe ne zamu isa babu matsala".

    Saida ruwan sama ya yawaita sosai sannan suka iso gida,
   Saida yayi horn sau uku kafin maigadi ya fito hannunshi rik'e da lema ya wage gate d'in gidan,
    D'aga ma maigadin hannu yayi alamar gaisuwa tareda tsaida motarshi a daidai inda aka tanada domin ajiye motoci.

     A hankali ta bud'e motar ta fito, irin rigar nan ta barristers ce sanye a jikinta da hular kayan, shima namijin irinsu ne a jikinshi, a bayanshi ta bo'ye bayan ya rufe motar dan bata son ruwan sama ya tab'ata ko kad'an sannan suka shiga cikin gidan.

    Da shigarsu kuwa saiga wata yarinya 'yar kimanin shekara bakwai, sanye take da doguwar riga armless baby pink in colour,  da sauri kuwa ta taso
   "Oyoyo Momy" ta fad'a bayan ta rungumi mamarta,
    "Oyoyo my Hafsa" itama ta fad'a tana mata murmushi,
    "Au! Momy'nki kawai kika sani ko?  Nima barinje wurin nawa baby'n yanzu" namijin ya fad'a bayan ya d'auke kanshi daga garesu.

    "Am sorry Abbana, yanzu zanzo wurinka kaima" Hafsa ta fad'a bayan ta saki momy'nta ta koma ta rungumi Abbanta.

    "Ina Haydar ne?" Ya tambayeta bayan ya cire hular kanshi.

    "Haydar yana wurin Nany, suna upstairs" ta bashi amsa,
    "Ok kije kice ta kawo minshi, nayi missing nashi tun safe rabona dashi"
   Da sauri kuwa ta haye sama don ta kira Nany d'in da Haydar k'aninta.

    "Ammafa Abbah nayi mamakin yanda nayi winning shari'ar nan ta yau, ni kaina nasan ka sakar min itane kawai",
    "Thank God da kika fahimci hakan da kanki, yunwa nakeji wallahi",
    "Ok am sorrie, barin shiga yanzu in dafa maka favorite naka" ta cire rigar jikinta da hular ta shiga d'akinta ta ajiyesu sannan ta fito domin nufar kitchen.

     K'arar shigowar text message taji a wayarta, da saurinta ta ciro wayar daga cikin jakarta ta bud'e sak'on.

     Ido bud'e take karantashi cikin mamaki, bayan ta gama karantawa ta kalli mijinta tace "Abbah! Kalli sak:onda aka aikomin yanzu".
    Karb'ar wayar yayi ya fara karantowa a bayyane.

Princess Amrah😘
NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now