BABI NA SHA DAYA

1.3K 101 3
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~63~}

    Bayan sati d'aya na fara jin sauk'i, har zama na farayi sab'anin da da ko zaman ma bana iyawa,
   Sosai Dr. Rafiq yake bani kulawa, komai shi yakeyi min, hatta da magani da kanshi yake siyamin ya bani ruwa insha,
   K'awayena Zarah da Rabuatu kuwa tamkar 'yan uwana na jini, duk wani abu daya dace suna yiminshi,
    Abun haushi kuwa har yanzu Gentle batazo da dubani ba.

   Kwatsam ina zaune Rabiatu da Zarah na gefena, labari muke sosai suna bani dariya, hakan yasa hankalina yad'an kwanta, a gidanmu kuwa har yanzu basu sani ba, saboda Dr. Rafiq yace kar in fad'a masu abunda ya sameni harsai idan na koma gida dan kar in tayar  masu da hankali.

    Securities ne suka shigo roon d'in har mutum hud'u, bayansu kuwa wani babban mutum ne sanye da babbar riga,
  Bayan shigowarshi saiga wasu securities d'in guda hud'u a bayanshi.

    Cike da girmamawa muka gaishesu,
   Mutumin kawai ya amsa sallamar, tun bai rufe baki ba saiga wasu manyan mutanen sun shigo masu yawan gaske, har room d'inma bai iya d'aukarsu ba wasunsu a bakin k'ifa suka tsaya.

   Hankalina ya tashi sosai ganin manya manyan lecturers d'inmu ne,
   Kallo suka bini dashi baki d'aya kafin sukayi min ya jiki,
   Wancan mutumin wanda ya fara shigowa ya gyara zamansa a plastic chair d'inda yake zaune yace
    "Aisha Abubakar ko?"

   Cike da mamaki na d'aga kaina alamar ehh,
    "Good" ya fad'a tare da zaro wata 'yar takarda daga aljihunshi na gaba.

    D'an rubutu yayi sannan ya mik'ata ga wani yace
   "PA a ajiye min wannan" sannan ya juyo gareni yace
    "Ya jikinki?"
  Alhamdulillah na furta cike da alamar tambaya.

    "Karki damu ba wata matsaka bace kinji, sunana Khalil MA Khalil" ya furta tare da mik'ewa tsaye yabar d'akin,
  Securities d'inshi ne suka nara masa baya sannan sauran malamn ma suka fita.

   "Ya Salam" na fad'a sabida jin sunanshi,
   Da fitarsu Zarah tayi ajiyar zuciya tace
   "VC nefa da kanshi yazo dubaki Ummimah, lallai kin ciri tuta, wata k'ila sun samu labarin abunda aka mikine sukazo dubaki",
   Rabiatu tace
   "To a ina zasuji labarin? Ke VC fa, wa zai fad'a masa? Kiga gayyar da sukayi fa".

   Nidai saurarensu kawai nake amma fa sam hankalina bai kwanta da zuwansu ba.
   Bayan kwana biyu aka gama exam aka rufe School baki d'aya,
  A ranar nima na nemi sallamah, saboda Zarah da Rabiatu bana son na shiga hakkinsu, sunce wai ba zasy tafi su barni ba.

   Babu yanda Dr. Rafiq bayyiba akan inyi hak'uri in k'ara samun sauk'i amma kuma na nace sai ya sallameni, hakan yasa ya bani takardar sallamah tare da kud'i masu yawa yace inyi kud'in mota.

*****

   K'arfe hud'u na rana na sauka Katsina,
   Akwatina naja tare da tsayar da mai napep nace ya kaini Saulawa,
   Babu b'ata lokaci kuwa muka isa gida.

   Cike da farin ciki Afrah ta tareni, jakata ta karb'a tare da kaita d'aki,
    "Afrah ina sauran 'yan gidan ne?" Na tambayeta bayan ta zauna tana min saanu da zuwa.

    "Sun tafi sukai Amrah asibiti, booking zasuyi mata, insan ance wai nanda wata biyu ko uku indiyawan nan zasy dawo".

   Harda tsalle nayi dan murna, hakan yasa na fama ciwona sabida har yanzu raunukana basu gama warkewa ba.

   Saurin duk'ewa nayi ina matse matse,
   Da tausayi Afrah tace min
"Bakida lafiya ne Aunty?"
   Kai kawai na d'aga mata alamar ehh,
    "Ayyah! Sannu gashi kuma kun gaji, kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci, nasan su Baba ma yanzu suna hanya saboda tun safe suka tafi".

   Haka na tashi jiki babu k'wari na nufi toilet,
   Har ga Allah naji dad'in bayanin Afrah,
   Bayan nayi wanka na jiyo muryar su Mama,
  Aikuwa da sauri na saka kayana na nufi parlor ko mai ban shafa ba.

    Har k'asa na gaishe dasu Baba,
  Sunji dad'in ganina sosai Baba yace
   "Wannan zuwa na bazata, baku fad'a mana zaki dawo ba ai",
    "Ehh Baba, nafison nayi surprising nakune dama",
    "Gashi kuwa kinyi ai hankalinki ya kwanta" mama ta fad'a tana kallona.
    Baba ya k'ara yimin bayanin komai,
   Naji dad'i sosai na matsa inda Amrah take,
    "Sannu k'anwata, ya jikin naki?",
    "Jiki da sauk'i Aunty Ummimah, ya karatu?",
    "Alhamdulillah, Allah ya baki lafiya".

   Bayan naci abinci nayi tunanin in fad'a masu abunda ya sameni amma kuma na fasa,
   Da zarar nayi k'ok'arin fad'i sai wata zuciyar ta haneni,
   Hakan yasa nayi shiru nabar maganar a cikina dukda cimin rai da takeyi.

    Idan ma zaune nake na tuno da wannan abu sai hankalina ya tashi, kuka sosai nakeyi ni kad'ai ba tare da kowa ya sani ba,
  Wata rana ina cikin yin kukan Mama ta shigi ta sameni a haka,
   Sallamah uku tayi amma duk bansan tayi ba,
    K'arisowa ciki tayi ta ganni inata sharar kuka,
   Hankalinta tashe ta tsuguna kusa dani tace
    "Ummimah lafiya? Me sameki kike kuka?".

   Zabura nayi tare da share hawaye ina fad'in
    "Babu komai mama",
   "Kamarya babu komai? Babu komai shine kike kuka?"
    Gyara zama tayi sannan tace
    "Nasan babbar matsakarki itace ciwon 'yar uwarki, dan Allah ki cire wannan damuwar, insha Allahu k'arshen cutarta ya kusa zuwa, saboda muna sa ran nanda wata uku indiyawan nan zasu dawo, kuma wannan karen ance zasu iya tafiya da marasa  lafiya a k'asarsu, kinga kuwa insha Allahu Amrah ta kusa rabuwa da cutarta har abada".
  
    Goge hawaye nayi nace
   "Shikenan Mama, Allah ya bata lafiya" na fad'a kamar da gaske abunda  ya sakani kukan kenan.

        Murmushi tamin nima na miyar mata dana k'arfin hali,
    "Kizo Afrah ta gama girki, nasan kina jin yunwa",
    Tashi nayi nabi bayan Mama har parlor.

     Satina biyu a gida Mama tamin maganar Gentle, gar saida gabana ya fad'i data ambata min sunanta,
    "Naji Salmah shiru kema kuma bakije inda takeba, Allah yasa dai lafiya",
      Gabana ya fad'i na rasa abunda zan fad'a mata, sai daga baya nace
    "Ta fad'a min cewa ba'a garin nan zatayi hutu ba, wai Kaduna zata tafi" nama Mama k'arya,
     "Ahh to babu komai ai, Allah ya dawo da ita lafiya"
   "Ameen" na amsa mata dashi cikin raina kuwa wata irin k'unar rai nakeji, saboda yanzu babu wadda na tsana a doron k'asa kamar Salmah".

   Sannu sannu har hutunmu ya k'are na fara haramar yin registration,
   Da k'yar da wahala Baba ya samo min kud'inda zanyi,
     Koda naje banki zan saka kud'in abun mamaki da zarar an saka password d'ina baya bud'uwa,
  An gwada kusan so biyar amma portal d'ina yak'i ya bud'u,
   Zarah na kira a waya na fad'a mata abunda ke faruwa,
    "Wannan ba matsaka bace, akwai sauran lokaci kuma kinsan akwai table payment, ki bari a koma School sannan kawai ki biya acan, kinsan dama bank payment d'in nan matsalace dashi".

    "Hakane k'awata, to nagode sosai".

    Da haka na kashe wayata tare da ajiyeta k'asa.

    Sati d'aya daya zagayo na fara shirin komawa,
    Su Mama sunyi mamaki da sukaji nace masu ni kad'ai zan tafi,
   Sallamah nayi dasu na nufu tashar mota,
   Babu b'ata lokaci muka sauka cikin garin Jalingo.

   Wurin biyan kud'in naje,
Abun mamaki ki acan d'inma babu sunana,
   Abu wasa ba wasa ba har maganar taje sama,
   Anan ne aka tabbatar mun da anyi expeling d'ina from the University, saboda kamani da akayi da zubar da cikin shege,
   An samu takardar asibiti wadda ta tabbatar da hakan, sannan kuma likitan daya dubani da kanshi shi ya tabbatar daa hakan.

    Take jikina ya d'auki rawa, bakina ya kasa furta komai, kaina ya ringa jujjuya min,
   lummm na fad'i k'asa sumammiya.

_ayi hak'uri da wannan, ina fama da ciwon idone fitinanne, ina buk'atar addu'arku._


°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now