BABI NA ASHIRIN

1.4K 102 1
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~72~}

    Cikin izzah da tak'ama Barr. Sa'eed yace
    "Aishatu shin a cikin kalaman da Salmah tayi ko akwai maganar data fad'a wadda kike da ja akanta?",
    Da hannunta ta share hawaye jikinta ya fara rawa saboda yanda taga an tsura mata ido,
    "Ehh...ehh a..akwai" ta fad'a cikin rawar murya.

   Murmushi Barr. Sa'eed yayi yace
    "Ki kwantar da hankalinki ki daina rawae murya indai da gaske kinada gaskiya ba k'arya zaki fad'a ba".

     "Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a k'ufule,
     "Bai kamata Barr. Sa'eed yana fad'in wannan kalaman ga Aishatu ba, ya kamata yayi la'akari da yanayin yawan mutanen wurin nan ne yasa take rawar jiki da rawar murya",
     "Barr. Sa'eed a kiyaye" alk'ali ya fad'a yaci gaba da kallonsu.

    "uhm, kr nake sauraro" ya fad'a a hankali.

    "Kusan duk maganganun data fad'a k'arya ne, nasan dai tana yimin wasu abubuwan idan taga inada buk'ata, amma maganar da tace ita ke d'aukar nauyinmu wallahi k'aryane, babana bai rageni da komai ba, kusan duk wata ko baya da kud'i sai ya ranta ya turo min, sannan kuma da tace na canja hali wannan duk halayenta ne, babu inda nake zuwa, idan ma na fita daga room d'inmu to bazan wuce room na kusa da namu ba inda k'awayena Zarag da Rabiatu suke ba".

     "Ina su k'awayen naki suke a halin yanzu? In da gaskene ai ya kamata ace sunzo nam kodan su bada wannan shaidar ga k'awarsu".
    Jikin Ummimah ya hau rawa saboda rashin halartar su Rabiatu kotun, tasan ba lallai bane a yarda da maganarta.

    "Gamu" Zarah da Rabiatu suke fad'a daidai lokacin da suka shigo cikin kotun.

    Ajiyar zuciya ta sauke farin ciki bayyane a fuskarta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da suka iso inda ake son ganinsu.

     Qur'ani aka basu sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya sannan cikin rashin jin dad'in zuwansu Barr. Sa'eed yace
    "Kune k'awayen nata?",
    "Ehh mune"  suka had'a baki wurin fad'i.

     Baki d'aya yama rasa tambayar da zayyi masu, saboda sam bayyi tunanin zasuzo ba, dan saida ya tabbatar da babu su a cikin kotun sannan ya nemi yana son ganinsu.
    Sai daga baya wata fasaha ta fad'o masa yace
    "Wai da gaske wurinku Aishatu take zuwa wani lokaci?",
    "Ehh da gaske wurinmu take zuwa duk lokacin da Gentle ta fita tayi dare, wani lokacin ma a d'akinmu take kwana saboda tace ba zata iya kwana ita kad'ai ba" Rabiatu ta bashi amsa.

    Shiru ya d'anyi kafin yace
    "To idan da gaske ne mesa wani lokacin idan bata d'akinku kuke zuwa ku tambayi Salmah inda Aishatu taje? Kenan hakan ya tabbatarda ba kowane lokaci kuma d'in kuka san inda take ba".

    Zarah tayi caraf tace
    "So d'aya ne tak hakan ta kasance, kuma ranar ma ta fita neman Gentle ne akan tazo suyo karatu dan exam d'in da zamuyia washe gari mai wahala ce, tun fitar da tayi shine vata dawo ba har mukaje nemanta room d'insu".

     Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace
    "Ya mai girma mai shari'ah, da wannan bayanin da k'awayenta sukayi ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa ba kowane lokaci ne take tare da k'awayentan da take cewa suna tare always ba, kenan akwai gyara a maganar Aishatu saboda gashi k'awayenta sun fad'a da bakinsu, ta masu k'aryar zataje ta nemi Salmah domin suyi karatu, amma kuma Salmah ta dawo tace ita batama ga Aishatun ba, wannan ya tabbatar da cewa ta tafi yawo kenan"
   Ya juya gasu Zarah yace
    "Zaku iya tafiya ku zauna".

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now