BABI NA BAKWAI

1.5K 119 1
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪
  

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~41-50~}

      A gigice ta farka cike da azabtuwar ciwo, ganin ina kuka yasata k'ara k'ank'ameni itama tana kukan,
    "Aunty Ummimah ki daina kuka ai naji sauk'i, tunda Baba ya saimin panadol nasha zazzab'in ya sauka, ki kwantar da hankalinki, idan kuna kuka nima sai kisani in ringayi".

   Wani kukan maras control ya sake fito min da k'arfi, kenan Amrah bata san cutar da take tare da ita ba? Allah sarki baiwar Allah, Allah ya bata lafiya. Fatan da nayi mata a raina kenan bayan na saketa nace,
    "Barin kawo miki abinci nasan bakici komai ba".
    Da hanzari Baba ya share hawayensa dan baya so mu fahimci cewa shima kukan yayi,
    "Ki duba booth d'in mashin d'ina akwai yoghurt na nan ki kawo mata, nasan zata fi buk'atar abu mai ruwa ruwa".

   Tashi nayi kuwa na nufi inda mashin d'in yake,
   Bayan na bud'e booth d'in na fiddo yoghurt kai tsaye na wuce palor,
    Bud'eshi nayi na juye a kofi na fara bama Amrah,
   Saida tasha kamar rabin kofin sannan na sauke shi k'asa,
   Kamar tana jirana kuwa sai amai ta fara kwarawa babu sassauci, saida ta harar da komai dake cikinta sannan cike da azabar ciwo ta koma ta kwanta,
   Hawaye naji sosai suna fita daga idona,
    Cikin natsuwa na dangwali ruwa a hanky na goge mata bakinta sannan na fara gyara jikina,
   Har a lokacin Mama da Afrah basu daina kuka ba, kowansu tana tausayin halinda muka tsinci kanmu a wannan yanayi.

     Bayan na gama gyaran wurin duka na koma kan kujerar na d'ira fuskar Amrah akan cinyata, baki d'aya zazzab'i mai zafi ya taso mata,
   Kuka nake sosai amma maras k'ara, hawayena ne ya sauka bisa kumatun Amrah,
    K'ok'arin tashi zaune tayi amma ta kasa,
   Ganin haka yasa na tasar da ita zaunen ta fuskance ni,
    "Dan Allah ki daina kuka Aunty Ummimah, na fad'a miki naji sauk'i fa, yanzu ma aman da nayi ne yasa zazzab'in ya sake dawowa".
   Goge hawayen nayi tare da yi mata murmushin yak'e, itama murmushin tayi sannan ta koma ta kwanta a bisa cinyata,
   Mama da Afrah kuwa barin d'akin sukayi dan basa so ta fahimci kuka sukeyi.

    Bayan sati biyu.

Zaune muke ina bama Amrah abinci a baki,
    Kwatsam naji sallamah da muryar mace babba sai kuma d'ayar muryar kamar ta budurwa,
   A lokacin Afrah ta tafi islamiya Baba kuma bai dawo daga wurin aiki ba,
    Mama kuma tana d'akinta tana fitar da kayan wanki.

   Amsa sallamar nayi tare da ajiye abincin a k'asa,
    "Maraba daku, ku shigo daga ciki".

       Babbar macen ta fara yi gaba sannan budurwaw ta shigo,
    Murmushi na saki a lokacin dana Gentle, itama murmushin ta miyar min dashi,
    Kamarsu d'aya ita da babbar matar hakan ya tabbatar min da mahaifiyarta ce,
    Sauke Amrah  nayi daga bisa jikina na gaishe da matar,
    "Ahh Salmah kune a gidan namu?,
   "Wallahi kuwa mune Aisha, na jiki kwana biyu bakizo School ba, shine naje har Principal's Office ya duba min address d'inki,
   Nayima Momy na bayaninki sai tace zata biyoni mu duba ko lafiya kike, shine fa kika gammu da yammacin nan".

   Murmushi na mata sannan nace "Amrah baki iya gaisuwa bane?",
   Jiki babu k'wari ta duk'a har k:asa ta gaishesu,
   Bayan sun amsa ne Mama ta shigo saboda muryoyin da taji,
   Fuskarta d'auke da fara'a suka gaisa da Momy,
   Nayi ma Mama bayaninsu da kuma dalilin zuwansu,
   Sannan kuma nayima su Gentle d'in bayanin rashin zuwana makaranta,
   Sun tausaya mana sosai sun kuma tausayawa Amrah,
    Sai yamma lik'is sannan Momy ta bama Amrah 10k cike da tausayi suka bar gidan.

    Sosai Momy ta yaba da kirkinsu, hakan yasa ta amince min da yin k'awance da Gentle, koba komai tanada hankali, sannan kuma tanada kula itada mahaifiyarta.

   Tun daga wannan lokacin kusan kullum sai Gentle ta ziyarce mu, hakan ba k'aramin  dad'i yake min ba,
   Wannan kular da take mana ita ta siye min zuciya baki d'aya, naji Gentle ta kwanta min a rai.

     Saida mukayi wata d'aya a haka, lokacin har na gama rubutama Amrah jarabawa, hakan yasa na koma makarantata, ammafa rabin karatun da nakeyi hankalina yana gida, ina matuk'ar tausayin 'yar uwata, saboda yanzu ciwon k'ara yawaita kawai yake, kuma gashi babu ko maganar *kud'in aiki* (Raheem and Basmah err lele) barin kud'in magani, saisa a kullum na zauna banida aiki sai kuka.

   Wata rana cike da murna Baba ya dawo daga wurin aiki, kallo d'aya na masa na gano farin ciki a tattare dashi,
    Da sauri na karb'i ledar hannunshi,
    "Balango ne na gani a hanya na siyowa maras lafiya, idan taci sai ta baku sauran",
   Murmushi nayi na fara bata a baki,
   Bayan Mama ta shigo d'akin tayima Baba sannu da zuwa,
   "Nazo maku da albishir mai girma, amma fa sai kun bani goron albishir",
   Murmushi d'auke a fuskata nace "ka fad'a mana koma menene Baba, zan baka goro babba".

    "Yanzu na dawo daga wurin likitan da yake duba Amrah, ya tabbatar min da cewa gwamnati ta kawo manya manyan likitoci daga India, wanda zasu duba narasa lafiya wanda suke d'auke da ko wace irin cuta kuma kyauta bada ko sisi ba, zasuyi wata uku sannan su koma k'asarsu,
   Dan haka ya bani form d'aya na cike da sunan Amrah, nan da sati d'aya zasu fara aiki".

   Hamdaka muka saki mu duka dake d'akin, harda Afrah da yanzu ta shigo ta tsinci zance, Amrah kam dama bata san ciwon da yake damunya ba, tayi zaton zasu dubata ne kawai akan yawan ciwon da takeyi.

   Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanina da Gentle, ta kaiga bani b'oye mata ko wace irin damuwa haka itama bata b'oye min tata damuwar,
    Saidai a iya zamana da ita na fahimci sam ibada bata dameta ba, amma dai ina k'ok'arin nunar mata da muhimmancin ibada,
     Saidai kuma a duk lokacin da zan mata maganar ibada sai ta b'ata rai, wani lokacin ma ba zata sake min magana ba har a tashi daga makarantar.
    Sam hakan baya sa indaina fad'a mata gaskiya.

    Yanzu kam mun d'an samu kwanciyar hankali har sati ya zagawo,
  Baba da Mama da kansu suka kaita FMCK saboda acan ne za'a gudanar da taron likitocin.

       Likitici biyar suka hau kan Amrah, da manya manyan na'urori suke amfani wanda suke haska mata baki d'ayan k'walwarta,
   Sun tabbatar da brain tumor ce take d'auke da ita, saidai kuma bata tsananta ba,
   Dan haka akwai wani gashi da za'a ringa kaita na tsawon wata uku, duk bayan sati za'a ringa gasa mata k'walwarta sannan kuma akwai wani ruwan allura da za'a ringa duba mata a hanci shima dai duk satin ne,
   Sannan kuma sunma baba bayanin ba lallai bane idan akayi haka cutar ta rabu da ita har abada, amma kuma zata samu sauk'intana wasu shekaru.

   Duk da hakan Baba yaji dad'i yayi masu godiya sannan suka kama hanyar dawowa gida,
   Lokacin da Baba yaimana bayani ba k'aramin dad'i mukaji ba, har da sadaka saida Baba yayi duk da shima mabuk'aci ne.

Bayan shekara uku

*******
    Pls kuyi hak'uri da wannan page d'in yayu gajerta, bana jin dad'in jikina ne, luv you all.



°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now