BABI NA ASHIRIN DA HUDU

1.1K 88 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~76~}

     _Jinjinar ban girma gareki k'awar arzik'i *Ayusha Iliasu* hak'ik'a ke jarumace, ki godewa Allah da irin d'umbin baseerar daya baki, kin cancanci yabo akan littafinki mai taken *Hak'k'i* Allah ya k'ara miki baseerah da zak'in hannu, Allah ya k'ara d'aukakaki yasa kifi haka. #onelove#_

      *****

           A Katsina kuwa Umar ya gama maganar komai yanzu suna jiran ranar shuga kotu ne kawai,
       Ummimah yanzu ta d'an samu kwanciyar hankali amma ba sosai ba,
   Saboda gani take yanzu wannan itace damarsu ta k'arshe idan har basuyi nasarah ba tofa shikenan,
   Addu'ah ta rik'a sosai sannan kuma mamanta ma tana tayata.

      Ana gobe za'a shiga kotu ne Haydar ya fara zazzab'i,
   Sosai jikinshi yayi zafi sai rawar sanyi yakeyi,
    Matuk'ar tashin hankali Sultana ta shiga saboda tunda take da Haydar bai tab'a yin zazzab'i mai zafin wannan ba,
     Ya mak'alewa Safiyya da ita kawai yake yarda,
   Hatta da ita Sultana d'in baya yarda da ita ko Umar babanshi.

      Hakan yasa daren ranae ya nacewa Safiyya yace lallai sai tare da ita zai kwana,
    Babu yanda Sultana batayi dashi ba akan ya kwana tare da ita amma sam yak'i yarda harda su hawaye,
   Ganin yana neman ya fasa mata kuka yasa ta mik'awa Safiyya shi tace ya kwaba tare da ita.

    Har sun kwanta Sultana taje d'akin Hafsa ta d'auketa saboda bai kamata Hafsa ta kwana ita kad'ai a d'aki ba,
   Sannan kuma a musulunce ma babu kyau su kwana tare da Hafsa saboda shekarunta sun wuce na ma'aurata su kwana tare da ita,
     D'akin Safiyya ta kaita ta kwantar,
   Ta samu Haydar ya mak'alk'ale Safiyya tsam kamar ance za'a k'wace masa ita,
    Cike da tausayi ta kwantar da Hafsa daga can gefe sannan ta tofesu da addu'ah ta koma d'akinta,
   Haka kawai take jin wani irin yanayi maras dad'i,
    Kawar da duk wani tunani tayi tare da barin d'akin ta nufi inda Umar.

   Ta sameshi ya tasa takardu gaba yana rubuce rubuce,
   Cike da soyayya tace
    "Sannu da aiki honey",
    "Yauwa wifey kema sannu" ya fad'a yana mata murmushi.

     "Bakaga yanda Haydar ya mannewa Safiyya ba, kamar wanda akace za'a k'wacewa ita,
   Nikam bansan wace irin soyayya Haydar yakewa Safiyya ba,
    Bansan ya zayyi idan zatayi aure ba,
   Saboda dai macece dole wata rana zatayi aure, koni bana mata fatan tayita zama a k'ark'ashinmu ba tare da tayi aure ba",
     "Insha Allahu kafin tayi aure ma yayi wayo, kinga babu maganar wahalar rabuwarsu kenan" Umar ya jefo mata amsa bayan ya rufe takardar da yake rubutu akai d'in.

     "Hakane honey, har ka gama aikin ne?" Ta tambayeshi bayan ta haye bisa gado saboda bacci takeji sosai yau.

    "Ko ban gama ba ai dole in daina in kula da iyalina" ya bata amsa had'e da hauewa gadon shima.

     "Nikam dama kaci gaba da aikinka, saboda bacci nakeji sosai yau, harda wani irin ciwon kai nake tsabar baccin dake idona" ta k'arisa maganar cikin hammar bacci harda d'an guntun hawayen hamma.

     "Nima dai baccin nakeji sosai, kiyi baccinki to barin k'arisa saura kad'an sai nima in kwanta, bana son in fita gobe ban gama wannan aikin ba",
   "Ok good night dear" ta fad'a bayan taja blanket ta rufa.

_3:30am_

      Wasu mutane uku ne fuskokinsu sanye da mask k'wayar idonsu kawai ake iya gani,
   Hannayensu rik'e da bindigogi k'anana ba masu girma ba,
     Kayan jikinsu kuwa complete black ne.

   A hankali had'e da sand'o suke tafiya har suka iso bakin gate,
    Kasantuwar a rufe yake yasa d'aya daga cikinsu ya zaro wani k'aramin abu daga aljihunsa,
     A daidai inda sakatar take ta ciki ya zira siririn abun babu b'ata lokaci kuwa k'ofar ta bud'u.

    Shiga ciki sukayi har yanzu sand'a sukeyi,
   K'ofar da zata sadasu da cikin gidan ma a rufe take,
   Yanda yayima gate haka yayi yanzu ma,
   Aikuwa suka shige cikin gidan a hankali d'aya daga cikinsi ya kunna 'yar fitila maras haske sosai.

   Tsaye sukayi cak kasantuwar sun rasa d'akin da zasu dosa,
    Sundai san an basu tabbacin Sultana akeso su kashe amma kuma ga jerun d'akuna nan basu san ta inda zasu nufa ba.

     D'akin dake fuskantarsu suka taka a hankali suka shiga,
   Ummimah da Mama ce kwance suna bacci, hakan ya tabbatar masu da babu Sultana a ciki.

   Fita sukayi daga nan suka doshi d'ayan d'akin,
   Zarah da Rabiatu ne suma sunata kwasar baccinsu.

    D'an guntun tsaki daya daga cikinsu yayi sannan suka juya suka fita daga d'akin.

       Na can nesa da parlor'n suka shiga inda suka samu Safiyya da Haydar kwnace, sai Hafsaacan daga gefensu suna bacci,
    Wannan ya basu tabbacin Sultana ce saboda sukam ba'a lissafa masu da akwai mai rainon yara a gidan ba.

      Murmushi sukama junansu sannan wani ya nemi inda ake kunna hasken d'akin ya kunna.
    Ya kunnawa kuwa Hafsa tayi saurin tashi zaune saboda ita dama indai akwai haske to ba zata iya yin bacci ba,
     Zaune ta tashi sai rarraba ido take hankalinta tashe take kallonsu,
   Ita a zatonta ma ko a d'akinta take dan bata san sanda Sultana ta dawi da ita d'akim Safiyya ba.

       Matsawa tayi inda Safiyya ta bubbugata da k'arfi kuwa ta tashi zaune,
    D'aya daga cikinsu wanda da alamar shine oga ya zare mask d'inshi had'e da yin wani shu'umini murmushi yana kallon Safiyya,
     "Barr. Sultana ko? Karki damu saboda damuwarki zata iya sakawa kiyi ihu, ihunki kuwa zai iya kawo

k'arshen rayuwarki".

    Cike da tsoro Safiyya ta dad'e bakinta ta samu kanta da kasa fad'aasu ha ita bace Sultana.

        Hafs ata bud'e baku zatayi magana kenan ogan yayima wani signal ya fesa wata powder a daidai fuskar Hafsa, take kuwa ta fad'i sumammiya a bisa gadon.

   Hankalin Safiyya ya k'ara tashi,
   Tana so tayi kuka amma tana tsoron karsu mata wani abu,
   Karkad'a kai kawai take alamar kar suyi mata wani abu,
    Wani bak'in k'yalle suka fiddo tare da fesa garin powder d'in nan a jikinshi sannan suka k'ulle mata bakinta dashi.

    Kan bindiga wani ya k'wala mata aikuwa itama ta sume sai jini ke fita daga kanta kamar anyi yankan wata dabba,
   Tun daga nan bata kuma sanin abunda ya faru ba.

    'Daukarta sukayi suka nufi waje da ita a hankali dan kar a jisu, saida suka fita suka sakata a mota sannan Haladu mai gadi yaji k'arar motar,
     Da sauri ya taso a rikice, ganin k'ofar gate a bud'e ne ya k'ara rikita rayuwarshi,
    D'akinshi ya koma ya d'auko makamai sannan ya fita waje,
     Hasken motar kad'an kad'an yake hange har suka b'ule,
    Sosai yaji haushi ya koma d'akinshi yayi tagumi,
    Baccin da bai koma ba kenan saboda yana tunanin abunda yasa ya iske k'ofa bud'e bayan kuma shi ya tabbatar da ya rufeta kafin ya kwanta,
    Sannan kuma ga k'arar mota da yaji wadda asukwane suka bar area'n unguwar.




_kudai k'ara hak'uri da gajerun shafi, bamu gama hidimar bikin bane, amma daga gobe insha Allahu zamu gama zakuci gaba da samuna kamar ko yaushe._




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                 NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now