02 Boyayyen al'amari

2.6K 154 1
                                    

WATA SHARI'AH😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                   (Jan. 2017)
               
                       {~2~}

    "Kamar yanda Allah ya yi ku masu taimako ke da mijinki, nake amfani da wannan damar domin rok'onku wata alfarma,
    An cuceta kuma an hanata kuka, ku taimaka ku taimaketa, ku fiddata daga mawuyancin halinda take ciki".

    "Subhanallah! To waye yayi wannan rubutun? Kuma da alama koma waye ya sanmu, kuma gashi babu wani cikakken bayani" Barrister Umar ya fad'a yana kallon matarshi Barrsiter Sultana.

    "Kaima kenan Honey, nikam banma fahimci komai dake ciki ba, bansan inda maganar ta dosa ba".

     "Barin kira number'n inji, dan wannan ba abune wanda za'ace wrong number ba, dama da niyyar mu d'in aka turomawa" kafin ya gama rufe bakinshi shima wayarshi tahau ruri alamar shigowar text message, exactly irin wanda aka turoma Sultana shima shi aka turo mashi,
    Bayan ya gama karantawa yace "akwai matsala kam, kinga" ya mik'a mata wayar, "nima irinshi aka turo min yanzu babu ko banbanci, barin kira dai".

    Kiran lambar ya latsa amma da mamaki sai yaji ana fad'in "the number you are tyring to call does not exist, please check the number and try again",
    "A'ah" ya fad'a bayan ya sake gwada lambar, still dai abunda aka fad'a ne aka maimaita.

    "Ya akayi? baka samu bane?" Sultana ta tambayeshi tana kallonshi.
    "Wallahi kuwa babu itama wai sukace kiji tsiyar MTN, k'iri k'iri yanzu aka turo min text da number amma wai ace babu ita, wannan k'aryane" ya sake kiran layin.

     Saida ya kira sau goma amma babu ita, hakan yasa kawai ya hak'ura ya ajiye wayar idonshi lumshe yana tunanin wanda ya masu wannan text d'in.

    "Barinje in dafa maka abincin yanzu honey" ta fad'a bayan ta tashi ta nufi kitchen.

    Hafsa da  Nany ne suka sauko daga upstairs Haydar na goye bayan Nany,
   Har k'asa ta duk'a tace "sannu da dawowa Alhaji" shiru yayi kasantuwar zurfi da yayi da tunanin wanda ya turo masu wannan text d'in,
     "Ina yini Alhaji" ta sake maimaitawa dan tasan baijita ba daya amsata.

    "Lafiya Safiyya ina gajiya?",
    "Ba gajiya, Momy fa?",
     "Gata can a kitchen, kawo Haydar d'in"
   Mik'oshi tayi, bayan ya karb'eshi tace "Alhaji an kawo wata takarda d'azu da bakunan, Haladu ya mik'o yace wani yaro ya kawo wai a aje maku kaida momy".

    "Ikon Allah! Ina takardar take?" Ya tambayeta bayan ya tashi zaune daga kishingid'awar da yayi.

    "Gata" ta mik'a mashi tare da nufar kitchen domin ta taya Sultana aiki.

     Bud'e takardar yayi yaga ab rubuta "nine dai wanda ya rubuto maku sak'on waya, yarinyar tana cikin matsanancin hali, an cuceta kuma an hanata kuka dan anga halinda suke ciki itada mahaifiyarta
    Kada ku wahar da kanku wurin kiran lambar tawa saboda ba zaku sameni ba, nasan kunada halin taimakon nata, kuyi bakin k'ok'arinku na rok'eku karku bari wanaan damar ta taimakon musulmai ta kufce maku, Allah kad'ai yasan ladar da zaku samu".

     "Sultana!" Ya fad'a bayan ya gama karantawa.

     "Na'am honey" ta fito da sauri saboda yanda ya kirata ta tabbatar da akwai matsala.
    Gabanshi ta gurfana tace "lafiya dai honey?",
  "Karanta kiga wannan",
        Goge ruwan hannunta tayi a zanin jikinta sannan ta karb'i takardar a hankali ta fara karantawa.

    "Towai waye yake aikoda wannan sak'on? Waya kawo takardar?" Ta tambayeshi tana kallonshi,
    "Safiyya ta bani ita, wai Haladu ya kawo yace ta ajiye mana idan mun dawo ta bamu",
     "Safiyya!" Ta kira sunan mai aikin tata.
      Bayan tazota tace "jeki kiramin Haladu kice yazoshi da sauri yabar duk abunda yakey, kar kuma ki biye masa kuita shirmen fad'an nan naku, dan nasan ku bakwa had'uwa wuri bakuyi fad'a ba",
     "To momy" Safiyya ta fad'a tare da fita da sauri harda gudu gudu takeyi.

      A waje ta sameshi yana ban ruwan flowers,
    Murmushi yayi daya ganta yace "ahh! 'Yan matana kece da kanki?",
   B'ata fuska tayi tace "nifa bana son shashanci waye 'yan matan taka?",
     "Kece mana Safiyya, ai banida wata budurwa wadda tafiki",
      "Kai ni ba shirme ya kawoni ba, kajeka momy na kiranka, kuma tace kayi sauri yanzu take son ganinka",
     "To kije gani nan zuwa" ya fad'a yana mata wani murmushin,
     "Tace mujemu tare, dan haka kazo mu tafi kana b'atamin lokaci",
     "Ahh lallai 'yan matana ta fara sona tunda har takeson mujera tare, mu tafi to".

   Bata kuma ce masa komai ba har suka isa, bayan sun zauna Sultana tace "Haladu waye ya baka takarda d'azu yace ka kawo mana?",
     Shiru yayi yana tunanin wace takardace take nufi? Sai daga baya ya tuna yace "wani yarone ya kawota nima dai bansan yaron ba, yace min wai an bashine ance ya tabbatarda ya kawota gidan nan".

    "Oh my God! To waye wannan wai?  Ai ya kamata koma waye ya bayyana mana kanshi mu taimaki baiwar Allah'n tare dashi, b'oyon ai bashuda amfani" Sultana ta fad'a.

    "Wama yasan ko k'aryar banza yake? Irin mutanen nan ne dai masu son su shiga sha'aninmu, dan haka ki fita batun wannan maganar nima na fita, ku tashi ku tafi Haladu" ya sallamesu.

      Tashi kuwa sukayi, Haladu ya kalli Safiyya yayi mata murmshin soyayya sannan ya tafi, ita kuwa hararshi tayi sannan ta koma kitchen Sultana ma tabi bayanta har yanzu batace komai ba sai tunane tunane da take,
    Ta tabbatarda akwai magana, bazai yiwu ace koma waye ya k'irk'iri maganar nan ba kawai dan yaji dad'i, zataci gaba da bincike har sanda Allah zai bayyana wannan b'oyayyen al'amarin.

Princess Amrah😘
NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now