BABI NA SHA UKU

1.3K 102 4
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~65~}

     Ganin kallonda ake bina dashi yasa duk na tsargu, nayu tsaye a k'ofae gida kasantuwar babu hanyar shiga,
   Ganin nayi tsaye yasa wanda ke baki k'ofar duk suka daddare kowa yana kallona,
    Saurin shigewa gidan nayi gabana sai fad'uwa yake hankalina ya matuk'ar tashi,
    Da sauri na shige naci karo da Baba yana kuka sosai kamar k'aramin yaro,
  Hakan ya k'ara tasar min da hankali matuk'a,
   Wurin Baba na isa tare da gurfanawa k'asa ina kuka,
   "Baba mefaru? mesa k'ofar gidanmu yake a cike? Mesa kake kuka?" Duka a tare na jefa masa wannan tambayoyin.

     Bakinshi na rawa yace
    "Aishatu 'yan fashine sun..." ya kasa k'arisa maganar kasantuwar kuka da yaci k'arfinsa.

    "Baba me 'yan fashi sukayi? Dan Allah kamin bayani ka daina kukan nan" na fad'a hankalina a tashe.

     Hannunshi ya d'aga ya gwada min inda aka harbeshi, sai kuma raunuka dake bisa kanshi wanda ban kula dasuba tun shigowata tsabar tashin hankali sai yanzu.
    "Na rasa mesa sukazo wurinmu, ni nayi zaton ko saa masu kud'i 'yan fashi ke zuwa inda suke, sai gasu nan gidan sunzo mana" Baba ya fad'a bayan ya dafe kanshi saboda wani irin sara masa da yayi,
    "Sannu Baba, inma a haka abun ya tsaya ai angode Allah" na fad'a cike da tausayin Babana.

    "Ba anan ya tsayaba Aishatu, akwai matsala babba, sun d'aure Afrah da Amrah sun tafi dasu..." tun bai rufe bakiba na mik'e tsaye ina kallon Baba,
    "Sun tafi dasu Baba? Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba wannan cinne ne, turo manasu akayi wallahi Baba" na k'ara fashewa da wani kukan ina tunanin furucin Gentle na k'arshe,
    "Lallai babu wanda zayyi wannan aikin sai ita, ko tantama babu itace" na fad'a a bayyane dukda a zuci naso maganar ta tsaya.

    "Wacece ita? Me kike fad'a ne waima?" Baba ya tambayeni a rikice,
    Samun kaina nayi da kasa fad'a masa sai wani irin kuka da nakeyi zuciyata sai tafarfasa take.

    "Ki fad'a min abunda yake ranki Aishatu, bai kamata kiyi shiru ba, waima meya dawo dake daga makaranta bayan kuma jiya kika tafi? Ko kin samu labarin abunda ya faru yau d'in ne?".

    Shiru nayi k'irjina saa dukan uku uku kawai yake,
   Hankalina ya k'ara tashi,
  "Baba zan maku bayani amma ka bari sai mutanen  nan sun lafa, sirrine tsakanina daku iyayena".

      Da gudu na k'arisa d'akin mama, na samu d'akin cike da mata sai jaje ake masu, hakan yasa na j'ara fashew ada kuka bayan na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya,
    Itakam babu abunda ya sameta alamar basu tab'ata ba kenan,
   A kid'ime ta janyo fuskata ta kalleni dan a tunaninta ko Amrah ce, saboda bata tab'a zaton zata ganni a wannan lokacin ba.

    "Mama ashe abunda aka mana kenan, sun tafi mana da Amrah da Afrah, shikenan mama sun gama damu" na sake fashewa da wani kukan.

    Sosai mutanen d'akin suka tausaya mana, wasu na hawaye wasu kuwa tagumi sukayi kowa da kalar tunaninsa, babban abun mamakin bai wuce yanda kowa yasanmu mabuk'atane amma kuma wai bama b'arayi masu yawi da sanda ba, 'yan fashi masu amfani da binduga sune sukazo gidanmu.

    Sau wuraren sha biyun dare sannan mutane suka gama watsewa, hakan yasa Baba ya dawo d'akin mama ya samemu kowa da abunda yake sak'awa, kuka kuwa babu mai rarrasar wani.

    Inda muke ya zauna ya dafa min kafad'ata,
    "Komai yayi zafi maganinshi Allah, sannan kuma dukkanin tsanani yana tare da sauk'i haka Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin littafinsa mai tsarki, dan haka dan Allah ku daina kukan nan, bana son wata cuta ta sameku a dalilin haka, insha Allahu Afrah da Amrah zasu dawo garemu".

     "To muna fatan haka Babansu, Allah ya tabbatar" mama ta fad'a tare da share hawayenta.

     Jikina na rawa na fara labarta masu duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe babu abunda na b'oye masu,
    Hankalinsu ya k'ara tashi sosai, sun tausaya min kuma suma sun tabbatarda Gentle ce tayi wannan aiken,
    Babbar matsalar yanda take d'iyar masu kud'i, mun tabbatarda ko munkai maganar ga hukuma babu abunda za'ayi masu.

    Yanda mukaga rana haka mukaga dare, ko rintsawa babu wanda yayi a cikinmu, sai koke koke dake tashi wanda har Baba kukan yake yana k'ara tausayawa rayuwata, saboda yanzu shikenan an rabani da martabata.

      Washe gari da sassafe Baba yaje yayi reporting maganar ga 'yan sanda,
   A tak'aice dai saida akayi sati biyu babu ko labarin su Amrah, gashi kuma yanzu har indiyawanda zasu duba Amrah sunzo, likitanta yayi waya yace a kaita za'a nata aiki dan yayi masu bayanin komai, hakan ya k'ara  tayar da hankalinmu, muka rasa duk wata natsuwarmu,
   Gashi kuma hukuma ta kas ayin komai akai,
   Har tadin maganarma basu sakeyi ba dukda cikakken bayani da Baba ya masu tun daga abunda Gentle tasa akamin har 'yan fashinda suka tafi da k'annena biyu.

   A ranarda suka cike sati biyun ne aka tsinci gawar Afrah a daidai kwanarda zata shigarda mutum layinmu,
    Mutanenda suka tsinci gawar natane suka kawota nad'e cikin buhu jina jina,
    Bayan sunyi sallamah  da Baba ya fitane suka shaida masa avunda suka gani,
    Amma kuma basu tabbatarda cikin 'ya'yan Baba bane kawai dai sunyi hasashen hakan ne, kasantuwar fuskar duk jinice kallo d'aya ba za'a iya gane ko waye ba.

    A rikice Baba ya k'wala mana kira nida Mama,
   Koda jin kiran muka tabbatarda ba lafiya ba,
   Dan haka muka fito k'ofar gida hankalinmu tashe ko d'an kwali ban nema ba.

    Bayan ya bud'e buhun ne ya janye yalwataccen gashin Afrah da duk ya b'aci da jini daga bisa fuskarta,
     Baki d'aya fuskar tayi dameji,
   Kayan jikintane ya k'ara tabbatar mana da d'aya daga cikinsu ne, *Afrah ko Amrah* saboda mun kasa banbancesu,
    Jiki na rawa Mama tace
   "Ko tantama babu Afrah ce, wallahi Afrahta ce wannan, saboda wannan kayan sune a jikinta, Amrah kuma blue shaddace ta saka ba wannan atamfarba".

   Bansan lokacinda na fasa wani irin ihu mai k'arfi ba, inda buhun yake na tsuguna ina kuka sosai ina k'ara kallon yanda fuskar Afrah ta koma,
   Tam! Na rik'e buhun ina sauke ajiyar zuciya bayan na nemi hawayenda nake na rasa,
   Duk abunda ke faruwa har yanzu Baba ya kasa furta komai,
   Saidai kuma kallo d'aya za'a masa aga tashin hankali k'arara a fuskarshi.

   Muna cikin haka ne wani mutumi yazo, a biye dashi wasu gardawa ne majiya k'arfi,
    Cike da izgili mutumin yace
    "Na gaji da hak'uri nikam hak'urina ya k'are,
    Dan haka yauyau d'in nan zaku barmin gidana,
    Shekara biyu kenan ana kan ta uku rabonka da biyan kud'in haya,
    Dan haka dole ku nemi wurin zama kubarmin nawa yanzu",
   Kallon gardawan yayi yace
   "Hame ku shiga ku firfito masu da kayakinsu".

    Da hanzari kuwa suka shiga, mu kuwa kallon mamaki kawaa muka bisu dashi,
    Rashin imaninsu ya matuk'ar d'aure mana kai,
   Basu ko dubi halinda muke ciki ba amma suka ringa jifa da kayanmu,
   Hakan ya tabbatar min da cewa wannan ma aikene daga Gentle.

     K'ara mukaji da k'arfi Baba ya fad'i k'asa,
    Da sauri Mama ta matsa inda ya fad'i d'in tana kiran sunanshi,
    "Abubakar, Abu dan Allah ka tashi, karka tafi ka barmu a daidai lokacinda muke buk'atar taimakonka, dan Allah ka tashi.." kuka yaci k'arfinta.

     

°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                  NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now