BABI NA ASHIRIN DA TARA

1.3K 108 1
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~81~}

    *KOTU*

  Kotu ta cika mak'il dan zan iya cewa duk zaman da sukeyi babu wanda al'ummah suka halarta sosai kamarshi,
   Saboda sosai Alhaji Abu Abu ya gayyato mutane dan ya tabbatar da su zasuyi nasarah, tunda dai yasan su Barr. Umar basuda wata shaida saisa suka canja salon shari'ar, kuma ma canjin salon da sukayi bai amfana masu komai ba saboda gashi sunyi takarda wacce taci uwar original one d'in.

   Mai gabatar da k'ara ne ya tashi ya gabatar sannan alk'ali yace
    "Kotu na jiran Barr. Sultana domin taci gaba daga inda ta tsaya".

   Tasowa tayi bayan ta gyara daidaituwar rigarta ta iso inda Ummimah da Gentle suke,
     "Kotu na son ganin Dr. Khalid idan yana kusa, ya fito da takardar asibitinshi kamar yanda yayima kotu alk'awarin zai kawota yau".

   Tasowa yayi cike da confidence, takardar ya mik'ama Sultana ta duba sosai, saida gabanta ya fad'i saboda babu wanda zai ganta yace ba ta kirki bace,
    Ganin reaction d'in fuskarta yasa Barr. Sa'eed sakin murmushin mugunta sannan ya kalli Barr. Umar daya tsurawa Sultana ido dan shima ya fahimci yanayinta.

   Mik'a takardar tayi har ta isa ga alk'ali,
   Bayan ya dudduba sosai yayi rubutu sannan ya miyar da ita ga Sultana,
    "A bisa duba da kotu tayi ga wannan takardar, kotu ta gamsu da cewa asibiti dai ta Dr. Khalod ce shi kad'ai, dan haka batun wannan maganar ta kau".

   Dukda gabansu ya fad'i amma basu ji komai ba dan sun san duk wannan ba wani abu bane saboda babbar hujjar da garesu ta isa tasa a yanke hukunci yanzu yanzu.

       Wata takarda Sultana ta sake zarowa tace
    "Wannan takarda ce wadda ta nunar da cewa anyiwa Aishatu Abubakar fyad'e har sanadiyyar haka ta kamu da cutar hawan jini,
    Sannan kuma gashi nan k'asa signing d'inka ne farko sai na Dr. Rafiq a k'asa,
     Kenan kaima kasan fyad'e ne aka mata tunda har kayi signing?".

   Gabanshi ne ya hau dukan uku uku ya hau rarraba ido,
    "Ni wannan signing d'in ba nawa bane, akwai dai yanda akayi amma ni bansan da wannan maganar ba, abunda na sani d'aya ne kawai ta zubar da ciki ne, wannan takardar kawai nasan nayi signing amma fa ni ban ma tab'a ganin wannan d'in ba".

   Murmushi Sultana tayi tare da d'aga d'ayar takardar asibitin da yace itace tashi,
    "Dr. Khalid ka duba da kyau ka gani mana, waye zaiga wannan signing d'in kuma har ya banbantasu? Ko makaho ya laluba yasan iri d'aya ne kuma mutum d'aya yayisu, kadai canja magana".

     "Objection my lord! Barr. Sultana tana k'ok'arin forcing d'in Dr. Khalid akan ya amsa abunda bashi yayi ba, ya fad'a mata cewa wannan sugning d'in ba nashi bane amma kuma ita tayi insisting akan nashi ne bayan kuma batada wata hujjar data tabbatar fa hakan" Barr. Sa'eed ya fad'a jin ana neman k'ure Dr. Khalid.

     "Barr. Sultana a kiyaye" alk'alin ya fad'a tare da miyar da kallonshi ga Sultana.

     "Iyakar tambayar da zan masa kenan ya mai shari'ah" ta furta had'e da komawa mazauninta ta zauna.

     "Ko akwai mai magana a cikin sauran lawyers d'in" alk'ali ya tambaya.

   Tasowa Umar yayi ya gyara zama hularsa yace
    "Sulaiman Usman Saraki, Yusuf Bilal Mohd, kotu zata so ganinsu idan suna kusa".

    Daga k'ofar shigowa sarki Manu ya shigo, a bayanshi kuma gado ne irin wanda ake d'ora marasa lafiya d'in nan,
   YB ne kwance cikin gadon duk yabi ya lalace kamar bashi ba.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now