BABI NA SHA BIYAR

1.3K 97 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~67~}

     Bugu d'aya kuwa Umar ya d'auki kiran cike da zak'uwa yace
    "Hello wifey"
    "Honey kamin uzuri dan Allah sai yanzu na kula da kiranka",
    "Ehh tunanin da nayi kenan dama, ina fatan dai lafiya",
    "Lafiya k'alau wallahi, ka jini shiru wallahi na jima a inda naje d'in ne, kuma akwai magana sosai sai na dawo, barin d'auko su Hafsa sannan mu wuto gidan da sauri",
    "Ai su Hafsa tun d'azu suna gida wifey, kuka tayima Hauwa'u wai tunda ba zaki dawo ba ita gida take so, a dole saida naje na d'aukosu",
    "Oh ni Hafsa ba hak'uri, bari to indawo yanzu gani a hanya",
    "Ok sai kin dawo" Umar ya fad'a tare da tsinke wayar.

   Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kasantuwar jin matarshi tana lafiya, dama jinta shiru da yayi yasa hankalinshi ya matuk'ar tashi.

     A jerin missed calls d'inda ta tayar harda na Hauwa,
   Hakan yasa ta katsa kiranta,
   Babu b'ata lokaci itama ta d'auka.
    "Maman Hafsa lafiya dai ko?" Ta tambayeta cikin tashin hankali.

    "Lafiya k'alau Maman Zarah, na saka wayar a jaka ne ashe a silent take ban sani ba, kin sanmu lawyers da yawon bincike, saisa kukaji shiru ban dawo ba",
    "To masha Allahu Aunty, Hafsa dai basu yarda sun tsaya ba",
    "Ehh haka Abbansu ya fad'a min yanzu, bansan mesa ba Hafsa batada yarda, waini gani nayi ga Zarah nasan zasuyi wasa tare ashe bata yarda ba",
    "Wallahi kuwa, bakiga kukanda tasha ba kamar wacce zan cirewa kai".

      Dariya Sultana tayi tace
   "Ai dama dai ku kuka zab'arwa kanku rigimammiya, ga Haydar d'ina d'an albarka yaro shiru shiru babu hayaniya sai natsuwa",
   Itama Hauwa dariyar tayi
   "Ai sai shiru shiru d'in, wannan yaron ai saike, yaro sai b'arna da rashin ji? Yau saida ya fasa min kaf k'waina dake cikin fridge, tumaturina kuwa saiya fasa ya fara sha sai ya yar ya sake fasa wani, duk ya gama wulak'anta min kayan fridge, Haydar saike kad'ai Aunty Sultana".

   Wata dariyar Sultana tayi saboda Haydar ya bata dariya sosai, itama kanta haka take fama da b'arnarshi kullum cikin dukanshi take amma kamar tana tunzurashi.
    "Aunty Hauwa ai d'an albarkar kenan, danma kun samu ya saka miki albarka a kayan fridge? D'ana yaron kirkine",
     "Wallahi Aunty Sultana zan kashe wayar nan indai maganar d'ankin nan zakina yimin",
    "Naji dai Aunty, dama na k'ariso gida yanzu nima, ki gaisarmin da 'yata Zarah, saida safe",
    "To saida safe, ki shafamin kan Hafsa 'yar albarka",
    "To Aunty Hauwa zan shafa miki kan Haydar d'an albarka".

   Murmushi tayi tare da hanginp up na kiran ta miyar da hankalinta ga kwanar gidansu da zata shiga.

***

     Parking tayi bayan ta shuga gidan, da hanzari Haladu ya iso gareta, hand bag d'inta ya karb'a bayan ya gaisheta,
     Ciki ta shiga yana biye da ita har suka isa parlor,
    Bayan ta k'arb'i jakar tayi godiya ta kalli inda Hafsa take kwance  tayi bacci hawaye duk sun bushe a idonta,
   Murmushi tayi tare da furta
   "Hafsa kayan rigima" ta shiga d'akin mijinta.

     D'an kishingid'awa yayi yana 'yan rubuce rubuce a wata takarda dake k'ark'ashin wani file,
    "Assalamu alaika ya Habeebee" ta fad'a cike da soyayya.

   Kanshi ya d'ago fuska d'auke da murmushi yace
   "Wa'alaikissalamu ya Habibty",
    "Sannu honey, ka jini shiru afwan",
    "Babu komai wifey, ina kika shiga ne kika d'auki wannan tsawon lokacin?" Ya tambayeta bayan ya harhad'a takardun a cikin file, saboda baya had'a aikinshi da kuma kula iyalinshi.

    "Ka gafarceni Uncle Umar da bayanin da zan maka",
   Saurin tashi zaune yayi saboda yasan akwai matsala, duk lokacin da Sultana zata kirashi da Uncle Umar to tabbas akwai matsala ne.

    "Me farune wifey? Allah yasa lafiya" ya furta idonshi kyam a kanta.

    "Uncle Umar na sab'a maka, ka hanani kula wanda yake turo mana text messages d'in nan amma na kasa hak'uri dole saida na kula,
    Wadda yake fad'a mana d'in tana cikin wani hali tabbasa tana cikin matsanancin halin, kuma tanada tsananin buk'atar taimakonmu, dan Alkah inaso ka taimaka min mu had'a k'arfi da k'arfi domin k'watar mata fansa".

    Kallonta ya sakeyi bayan ya rik'e mata hannu cike da soyayya
    "Anything for you wifey".

    "Yauwa honey na, sunanta Aisha Abubakar..." ta labarta masa komai tun daga farko har k'arshe bata b'oye masa ba.

    Ba k'aramin tausayawa Ummimah yayi ba shima,
    "Lallai ke jaruma ce wifey, kin cika 'yar aljannah, Allah ya bamu ikon taimakonsu",
     "Ameen mijina na kaina, Allah kar ya kawo ranar rabuwarmu".

   Murmushi Umar ya mata tare da cewa
   "Aikuwa dole zamu rabu wifey, akwai ranar da mutuwa zata rabamu".

    Wata 'yar k'wallah ta d'igo mata take tace
    "How I wish mutuwar ta d'aukemu tare honeyna, ko kuma ta fara d'aukata, bana fatan ka mutu ka barni saboda bansan yanda zan iya rayuwa idan babu kai ba".

    Dod'e mata baki yayi yace
   "ki daina wannan maganar Wifey, lets close the chapter, kije Hafsa na can kwance a parlor ki kaita d'akinsu, Haydar ma yana d'akin Safiyya".

    "Ok honey" ta fad'a tare da share hawayen daya fara fito mata.

    Bayan ta d'auki Hafsa ta kai d'aki ta koma d'akin Safiyya ta samu Haydar ya mak'alk'ale Safiyya yana bacci,
   Ita kuma sai d'an bubbuga bayanshi take itama baccin yana shirin d'aukarta.

   Kallonsu tayi cike da so, a bayyane ta furta
     "Allah sarki Safiyya! Akwai soyayya tsakaninki da Haydar, ban san ya zakuyiba idan zakiyi aure".

   Bud'e idonta tayi tayi murmushi ba tare data furta komai ba.

    "Yau bacci tunda wuri haka Safiyya? Ko dan bana nan ne?",
    "Momy kenan, ai idan bakya gidan nan jinshi nake kamar babu kowa a ciki, mun saba kullum wannan lokacin muna tare parlor mun fira, amma kuma yau bakya nan, gashi Hafsa ma k'awar firar tayi bacci tun d'azu".

    "Hmm! Wallahi Safiyya wata 'yar matsalace ta tsayar dani",
    "Ayyah Momy, Allah ya warware matsalar",
    "Ameen Safiyya, kawoshi" ta mik'a hannunta ta karb'i Haydar da jikinshi yayi kace kace da ruwan tumatur duk ya bushe yayi dabbura dabbura.

      D'akinsu ta kaishi ta saka mishi pyjamas d'inshi sannan ta d'orashi akan baby bed d'inshi blue, Hafsa kuma tana kan nata pink.
    Bayan ta tofesu da addu'ah ta fita,
   Kai tsaye alwala ta d'auro ta gabatar da sallolin da ake binta na magrib da isha, tayi shafa'i da wutri sannan tayi addu'ah sosai ta koma d'akin mijinta.

    Ta sameshi yana kwance yana jiranta,
   Murmushi ta masa sannan ta isa gareshi tana fad'in
    "Na gaji wallahi honey" tayi hamma tana kallonshi
    "Wallahi honey ba zakaji tausayinsu ba sai idan ka gansu, kaga gidan da suke, kaga halinda suke ciki, mamanta fa tace tun daga lokacin da abun ya faru yarinyar bata kuma samun walwala ba, kullum cikin kuka take".

    "Allah sarki bayin Allah, insha Allahi komai ya kusa zuwa k'arshe, zamu taimakesu sosai bakin k'arfinmu, har School ma zata koma da yardar Allah".

    "Allah ya yarda mai gidana na kaina" ta kama hannunsa ta bashi peck sannan ta mik'e domin canza kayan jikinta tana mai k'ara son mijinta, tana kuma k'ara jin dad'in yanda yake da taimakon mutane.

_Gaisuwa da godiya gareki maman Taslim, ina jin dad'in yanda kike nuna kulawa tare da bibiyar wannan labarin, Allah yabar zumunci da zaman tare, ya raya mana Taslim d'inmu bisa tafarkin sunnah, ameen._




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                 NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now