BABI NA HUDU

1.9K 128 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)
               
                   {~11-20~}

Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun k'arfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki,
   Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka d'auko Hafsa sannan suka wuce gida.
    A cikin motar Hafsa tace "Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kad'ai ba dan kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin Head Master's Office,
   Na gaisheshi ya dafa kaina yace min "kece Hafsa ko?",
    "Ehh nice Hafsat Umar Muhammad" na bashi amsa,
    Shine yace min wai dama sak'one zai bani wurinku,
    "Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matuk'ar muhimmanci, idan Allah ya baka damar taimako to kayi k'ok'arin aikatashi tun kafin damar ta kufce maka" ya kuma ce min "karki manta ki fad'a masu wannan sak'on".
   Yana gama fad'in haka English Teacher d'inmu yazo harda bulala a hannunshi
   "Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!" Naji tsoro sosai Abbah dan nasan sai ya bani kashi idan na koma class,
   Abbah abun mamaki ashe wannan mutumin wanda ya bani sak'o wurinku ya iya turanci sosai,
   Aikuwa ya taimakeni ya fad'awa Teacher'nmu cewa ba Hausa nakeyi ba turancine, harda cewa yayi wai yaji dad'in yanda ya jini ina speaking kamar ba 'yar Nigeria ba, kuma sak'o yake bani wurin parents d'ina, daga nan kuma sai ya tafi" ta gama basu labarin hankalinta kwance tana bud'e dash board dake side d'inta.

     Juyowa Umar yayi ya kalleta taci gaba da wasanta,
     Bai tanka mata ba, haka Sultana ma batace mata komai ba,
    "Abbah da Momy kunyi shiru, nidai babu ruwana idan ya tambayeni nasan na fad'a maku sak'onshi".

    Shiru sukayi har suka isa gida,
    Bayan Umar ya shiga d'aki ne Sultana ta juyo ga Hafsa tace "mutumin da yayi miki maganar ya yake?",
    "Momy nifa ban sanshi ba, kawai dai nasan ya iya turanci kuma yanada fara'ah" ta bata amsa.

*****

    Washe gari.

Da sassafe Sultana ta tashi, ita dama  haka tsarinta yake kullum ita ke rigar Umar tashi, sai ta gama ayyukanta kaf ta bad'e gidan da k'amshi sannan ta tasheshi yayi wanja, idan yayi wanka sai su karya tare lokacin itama ta shirya kuma ta gyara Hafsa da Haydar.

    Bayan sun zauna kalaci ne Sultana tace "Abbah yau kuwa ina son fita ko zuwa da yamma ne insha Allahu".

    Gyaran murya yayi yace "dama kinga nima inason fita, ina zakuje ne sai mu fita tare?".
    Ido ta ringa zarowa dan batasan kalar k'aryar da zata masa ba,
    "Gudan Hauwa nake son zuwa, kwana biyu bamu gaisa ba",
    "Ehh kuma dama jiya ta kirani ni nama manta, tace ince miki Zarah batada lafiya saima yanzu na tuna wallahi, afuwan".

    "Amma dai honey ka cika mantuwa da yawa, yanzu inda ace bance zanje ba kenan da bazaka fad'a min ba, saidai ta ringa kallona da abun ko? Ai babu dad'i ace yarinya batada lafiya banje na ganota ba",
    "Nidai kiyi min hak'uri tunda gashi na fad'a miki, anjima d'in kinga sai mu tafi tare nima in dubata da jikin".

   Damm! Gaban Sultana ya fad'i sai raba idanuwa take saboda bata son ya bita,
    "A'a kafa san dama ba tare dakai nake zuwa gidan Hauwa ba, bana son inje ka azalzaleni sai na tashi mun tafi gida, ni kuma ina son in zauna muyi fira sosai barin yanzu mun dad'e bamu had'u ba".

    "To naji uwar son fira, kije yau ni kuma gobe sai inje, kuma inji kince zaki bini yawon gobe in kurta miki rashin mutunci" cike da soyayya yakeyin maganar.

    "Ehh naji dai babu komai, nima kuma daga can sai mu wuce yawonmu ko Hafsa?"
    "Ehh Momy, har ki kaini Royal Bakeries ki siya min shawarma da ice cream" Hafsa ta fad'a tana murmushi.
    "Karki damu ai yawo zamusha sosai cikin garin nan, harda inda wani bai tab'a zuwa bama sai munje ko?"
    "Ehh momy zanje, shi kuma Abbah sai mu barshi da Haydar ko?"
    Kwakkwab'e baki Haydar yayi alamar zayyi kuka,
    "Ni ba jakuje daniba ko? Appa kaji wai bajacu tafi dani loyal ba nima insha ayish kilim",
    "Woiii Haydar bai iya magana ba, wai ayish kilim, yaro kazo in koya maka magana" Hafsa ta fad'a tana mishi gwalo.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now