BABI NA TALATIN DA DAYA

1.8K 100 14
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~83~}

                  *K'ARSHE*

   "A bisa shaidu da hujjoji da suka gabata, kowa yaji yanda mai laifi ta amsa laifinta da bakinta, sannan kuma..." shiru alk'ali yayi kasantuwar tari da yaci k'arfin YB,
    Sosai yake tarin harda jini ke fita daga bakinshi,
    Cike sa tausayi kowa ke kallonshi,
   Baifi minti goma a wannan halin ba rai yayi halinshi,
   Da k'arfi iyayenshi suka d'auki salati had'e da kuka, dama sun san haka na zuwa saboda yanayin ciwonshi babu alamar zai tashi ko kad'an.

   An d'auki kusan awa d'aya da mutuwar YB harma an tafi da gawarshi Jalingo sannan kotu ta sake zama.

    "Kotu ta tabbatar da cewa Salmah ita ce ta saka akayima Aishatu fyad'e, bayan nan kuma tasa an kashe mata 'yar uwa wadda a dalilin haka babanta ya yanki jiki ya fad'i ya mutu,
    Indiyawa sunzo zasu duba lafiyar d'umbin al'ummah wanda a cikinsu harda Amrah k'anwar Aishatu, dalilin saceta da Salmah tasa akayi yasa har likitocin suka k'araci zamansu suka koma k'asarsu,
   Salmah tasa an sakawa gidansu Aishatu wuta har ya k'one k'urmus, tayi hakan ne da nufin  Aisha da mamanta su k'one dan bata san basu ciki ba.
   Dan haka kotu ta yankewa Salmah Abubakar hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari,
   Sannan kuma iyayen Salmah wato Alhaji Abu Abu da mahaifiyarta zasu bada tarar naira miliyan goma, wanda a cikin miliyan goma d'in za'a ware kud'in da za'a fitar da Amrah zuwa k'asar Indiya, za'a fidda wanda Aishatu zata koma makaranta saboda Salmah ita tayi silar da aka koreta, sannan kuma za'a fitar dana gidansu da Salmah tasa aka k'ona.
     Abdul k'adir kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda shi da kanshi ya furta cewa da hannunshi ya kashe Afrah, sannan kuma a gaban kowa yazo ya watsawa Salmah acid a fuska wanda fuskarta tayi dameji harma abun ya shafi idanuwanta.
    Sauran matasan nan kuwa wanda suka kasance kisa itace aikinsu kamar yanda kotu ta tabbatar,
  An yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga su dukansu.
     Sarki manu kuwa bashida laifi saboda kotu bata sameshi da laifi ko d'aya ba saima taimako da yayi, dan haka kotu ta wankeshi daga laifi.
     Idan Alhaji Abu Abu bayada kud'in tarar da aka yanka masa, kotu zata d'aureshi na tsawon shekaru uku, ko kuma za'aci gaba da tsaronshi har sai lokacin daya kawo kud'in.
     A k'arshe kotu na bama Aishatu Abubakar hak'uri akan abubuwa da dama, mahaifinta da 'yar uwarta da suka mutu Allah yaji k'ansu, 'yar uwarta maras lafiya kuma Allah ya bata lafiya yasa ayi aiki cikin nasarah".

   Kabbara kotun aka d'auka baki d'aya mutanen dake ciki,
    Kuka Gentle ta sake b'arkewa dashi da taji hukuncin da aka yanke mata,
   Ta tabbatar da zata fuskanci tsangwama sosai a kurkuku saboda damejin da fuskarta tayi, ta zama abun tsoro kamar *dodon Jatau.*

    "Zan biya, ko miliyan d'ari ne Allah na amince zan bayar akan a d'aureni" Alhaji Abu Abu ne yayi wannan maganar had'e da share guminsa.

   Murmushin dattako alk'ali yayi dan dama abunda yake jira kenan, da gangan yayi maganar yasan Alhaji Abu Abu ba zai yarda a d'aureshi ba saboda shi d'an siyasa ne, sannan kuma yanada mak'udan kud'in da ko fin haka aka nema sai ya bayar.

     Ummimah, Amrah, mama, Zarah da Rabiatu kukan farin ciki kawai suke,
    Barr. Sultana da Barr. Umar kuwa sai farin ciki baki har kunne,
   Har inda Barr. Sa'eed yake zaune yana had'a gumi Umar yaje,
  Bayan ya mik'a masa hannu yace
    "Kamar yanda kayi fatan Allah ya had'amu a *WATA SHARI'AH* gashi kuwa ya had'amu,
   Yau gashi d'an k'aramin Barr. Ya kayar da babban Barr."
   Murmushin k'arfin hali Barr. Sa'eed yayi tare da fad'in
    "Bana fatan Allah ya sake had'amu a *WATA SHARI'AH.* A yau kam na tabbatar da kai ba k'aramin Barr. Bane kai babba ne, dan zan iya cewa kama fini girma daga kai har matarka, tashi tsaye ma mu gwada tsawo inga ni da kai wa yafi wani girma?." Ya kwashe da dariya tare da mik'awa Umar hannunshi sukayi musabaha. Haka suka rabu Barr. Sa'eed na k'ara girmama Umar da Sultana dan ya tabbatar da su ba k'anana bane.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now