SHARHI

1.3K 61 5
                                    

*MATA TUBALIN AL'UMMA*

_FRIDAY,  21 SEPTEMBER 2018._

*SHIRIN DAGA MARUBUTAN MU, A YAU SHIRIN NAMU YANA D'AUKE DA SHARHI NE AKAN LITTAFIN WATA SHARI'A, WANDA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN AMRAH AUWAL MASHI TA RUBUTA A SHEKARAR 2017.*

_Gaisuwa tare da fatan alk'airi ga masoya ma'abota karatun littafan  mu a koda yaushe, barkanmu da saduwa da ku a filin namu na sharhi._

_A tak'aice labarin *WATA SHARI'A*  yana magana ne akan wata matashiyar yarinya wacce ta had'u da k'aluballan rayuwa kala-kala, wacce duka k'awarta ce sila, ta had'u da muguwar k'awa mara tsoron Allah, wacce tasa akai mata fyad'e dan rashin imani, hakan bai ishe taba tasa aka kureta a makaranta, hakan bai mata ba tasa a ka kashe k'anwar ta aka kawo masu gawar, wanda ya yi silar zuciyar mahaifinta ya buga harma ya rasa nashi rayuwar, hakan bai mata ba taci gaba da bibiyarta, tasa aka k'ona gidansu, kai dama abubuwa kala-kala na takaicin rayuwa._

_A dunk'ule zamu so mu ji meyasa marubuciyar ta zabi wannan jigon, kuma wani darasi littafin ya ke d'auke da shi Amrah?_


[9/21, 5:40 PM] Amrah:

Babban dalilin da ya sa na dauki wannan jigon saboda abubuwan ne da suka yawaita a wannan zamanin. Fyade ya yi yawa sosai ga mutanen yanzu.

Sannan kuma babban abun haushi, irin wannan jigon ne ya kamata marubuta su rinka amfani da shi wurin isar da sakunansu. To sai dai an samu karancin hakan, an fi karkata ga jigo daya tal (Soyayya).

Littafin WATA SHARIA na da manyan darussa a cikinsa. Daga ciki akwai illar amince wa kawa, da sauransu.

[9/21, 5:41 PM] FIDDAUSI SODANGI:

_Da farko dai zan fara ne da yiwa marubuciyar jinjina a bisa namijin kok'arin da ta yi wajan rubuta wannan shahararran littafi nata, hak'ik'a marubuciyar ta taka rawar gani kwarai da gaske, labarin ya tsaru iya tsaruwa, marubuciyar ta yi amfani da kaifin masirar da Allah ya yi mata wajan rubuta labarin, madallah da samun NAGARTACCIYA kamar ki a cikin marubuta, Hak'ika muna alfahari dake Amrah, dole ne ni Fiddausi in jinjina maki Allah ya k'ara basira Ameen._

[9/21, 5:42 PM] Amrah: Na gode kwarai
Firdausi. Allah ya kara mana basira baki daya.

[9/21, 5:43 PM] FIDDAUSI SODANGI:

_Akwai K'orafe-korafe da gyararraki, tare da tambayoyi, da nake buk'atar in gabatar maki dasu, idan kin shirya?_


[9/21, 5:43 PM] Amrah:

A shirye nake. Insha Allah.

[9/21, 5:44 PM] FIDDAUSI SODANGI:

_Typing errors, anci karo da errors masu d'unbin yawa a kusan kowani shafi na littafin, ban sani ba ko saurin son isar da sakon da marubuciyar ke son yi ne ya kawo hakan ko kuwa ya abin yake ne Amrah?_

[9/21, 5:46 PM] Amrah:

To a gaskiya ba wai saurin isar da sakon ba ne sila. Na yi typing din littafin ne da computer ba tare da na yi editing dinsa ba na kawo watsapp. Amma daga cikin wanda na yi a watsapp na yi editing din su.

[9/21, 5:48 PM] FIDDAUSI SODANGI:

_Marubuciyar ta gaya mana cewa Aisha ba tada k'awa ko d'aya, sai k'annanta, Afrah da Amrah, bata boye masu, komi nata, suma hakan ta ke a garesu, har takan tambayi kanta, shin watafi so ne a cikin su,  takan bawa kanta amsa dacewar matsayinsu d'aya ne, sai kuma kwatsam a wani waje mukaji marubuciyar tace, tafi shakuwa da Amrah, dan ko damuwa gareta sai Amrah ta riga kowa sani kafin kowa ya sani a cikin gidan, shin Amrah ya abin yake ne?_


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 27, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now