BABI NA SHA TARA

1.4K 98 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~71~}

    Zama tayi a kusa dashi jin wayar da yakeyi, hakan yasa ya kalleta ya mata murmushi kafin yaci gaba da wayarsa,
   Ganin wayar bata k'arewa bace yasa Sultana ta mik'e ta bud'e wardrobe d'inta,
    Ta samu kaya wanda zasuma Mama daidai harda supopinta da lasuka masu tsada.

     Har ta fita ta kaima Mama kayan ta dawo Umar bai gama wayar ba,
  Kwanciya tayi akan k'irjinsa tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana k'ara tuno da gobe ne fa zasu shiga kotu.

   Tashi daga jikin Umar tayi jin ya gama wayar,
    "Ya kukayi dashi honey?" Ta tambayeshi.

   Tashi zaune shina d'in yayi yace
    "Munyi magana dashi yanada kirki sosai,
    Ya shaida min cewa sai nextweek Friday zai dawo,
   Ya min bayani cewa wallahi shi kanshi baki d'aya kanshi ya d'aure da wannan maganar,
   Saboda yasan ya ajiye takardar asibitin Ummimah wadda ta nunar da cewa fyad'e aka mata sannan kuma tana d'auke da cutar hawan jini,
    Amma kuma wai daga baya ya nemi takardar ya rasa,
    Saidai wai yaji magana ta fito cewa ciki aka zubar mata,
   Baki d'aya ya rasa yanda akayi hakan ta faru kuma yaso ya mata bayani tun a lokacin tak'i saurarshi, ya rantse ya kuma rantsewa da Allah akan baisan yanda akaui hakan ta faru ba,
    Yadai san daga shi sai abokin aikinshi ne suka san da maganar, kuma abokin aikin nashi shi yasan yanda komai ta kasance,
      Kuma da zarar ya nufi abokin aikin nashi da maganar sai ya nok'e akan baya son maganar,
   Shidai wai yana zargin Dr. Khalid d'in akan yasan komai ko kuma da had'in hannunshi a wannan maganar,
    Amma yamin alk'awarin cewa idan ya dawo zai sake tuhumar abokin nashi da maganar ko za'a dace,
     ya nunar min da farin cikinshi sosai akan tsaya masun da mukayi domin k'watar masu hak'k'insu, kuma shima ya tabbatar min da zai bada gudummawa d'ari bisa d'ari dan ganin mun samu nasarah".

    Cikin farin ciki Sultana tace
    "Allah sarki ashe mutumin kirki ne, saisa akeso idan mutum yace ka saurareshi to ka saurareshi d'in, gashi kuwa gaskiya ta fito,
   Ni kaina ina zargin wancan likitan, to idan bashi ba waye zayyi haka? Su biyu ne kawai suka san halinda ake ciki",
    "Hakane wifey, dare nayi mu kwanta kinga gobe sammakon fita zamuyi",
     "Ok dear" ta fad'a tare da mik'ewa ta kashe wutar d'akin.

                     *KOTU*

     Kotu ta cika mak'il wasu na k'ara shigowa wasu kuwa fita sukeyi savoda rashin halartar alk'ali,
     Tsabar cika da kotun tayi yasa har wasu basu samu wurin zama ba saidai a tsaye suke.

     Shigowar alk'ali ne yasa kowa ya natsu akayi shiru har lokacin daya isa mazauninsa ya zauna.

     Daga can gefe na hangi Mama da Ummimah sunyi zuru zuru hankalinsu ya k'ara tashi dan suna matuk'ar jin tsoron ganin idon mutane ace wai duk yawansu sai sun tashi sunyi magana cikinsu.

    Mai gabatar da k'ara ne ya tashi yace
     "A yau d'aya  ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai ne kotu zata fara sauraron k'arar da Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar akan wai tasa an mata fyad'e wanda hakan yayi silar korarta daga makaranta" ya mik'a file d'in ga alk'ali tare da rusunawa sannan ya dawo mazauninsa.

     Alk'ali ya gyara zaman gilashinsa tare da yin gyaran murya yace
     "Idan akwai lauyoyi ko zasu gabatar da kansu?".

    Tashi Umar yayi bayan ya gyara rigarsa yace
    "Sunana Barrister Umar Mohd Bashir, a tare dani akwai",
     Sultana tayi saurin mik'ewa tsaye tace
     "Barrister Sultana Saddam Bakori"
     "Mune masu kare wadda take k'ara" Umar ya fad'a sannan suka koma suka zauna.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now