BABI NA ASHIRIN DA DAYA

1.3K 98 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~73~}

    Bayan sun koma gida sukaci gaba da tattaunawa inda Rabiatu da Zarah suka ringa tsinewa Gentle bayan Ummimah ta basu kaf labarin abubuwan daya samesu har mutuwar Baba, da kuma ta Afrah, ga Amrah maras lafiya bama asan inda take ba.

   Sunji haushi sosai kuma suma sukayi fatan samun nasara a wannan shari'ar da ake, saidai kuma a yanda sukaji labarin dukiyar mahaifin Gentle, da kuma babban Barrister d'in daya d'aukar mata, sun shiga kokonton samun nasararsu, saidai kuma sunyi fatan Allah yasa dukiyarsu kar ta amfanesu.

    Da wannan firar har yamma tayi Sultana da Umar suka dawo gida cike da gajiya,
   Su kansu a mota firar shari'ar kawai yakeyi, amma shi yana ji a jikinshi next zaman da za'ayi insha Allahu zasuyi nasara bama sai ansha wahala ba.

     Koda suka shigo gida Hafsa ta taresu, murna fal a ranta ta gaishe da iyayen nata sannan suka k'arisa daga ciki inda suka samu har yanzu su Zarah basu daina firar abunda ya samu su Gentle ba.

    Bayan sun natsu sosai Umar ya kira Dr. Rafiq, ya k'ara tabbatar masa da cewa fa ranar Monday next week anada buk'atarshi a kotu, ya amsa da 'insha Allahu zayyi k'ok'ari ko zuwa ranar Sunday ya shigo Katsina, saboda ranar Friday zai koma Jalingo',
   Sallama sukayi Umar ya kashe kiran,
   Sultana tace
    "To ya maganar wancan ma'aikatan na makarantarsu?",
    "wannan kuma ai bamuda case dasu, kotu zata aika da sammacinta" Umar ya bata amsa yana k'ok'arin cire suite daga jikinshi.

   Taimaka masa tayi ya k'arisa cirewar, itama ta cire nata sannan suka shiga wanka.

   Fitowarsu suka samu abinci jere a dining, murmushi Sultana tayi saboda tasan babu tantama wannan aikin Ummimah ne, tunda suka dawo gidan da zama ta hana Safiyya yin aiki sosai, komai ita takeyi bata gajiyawa.

      *Ranar lahadi 10:45pm*
  A daidai wannan lokacin ne Umar ya latsa kiran Dr. Rafiq domin yaji ko ya iso Katsinar amma shiru bata shiga ba,
   Sake latsa kiran yayi still dai 'not reachable',
   Hakan yasa ya fuskanci Sultana da itama shi take kallo yace
    "Ban san mesa ba number'n Dr. Bata shiga, kinga tun yamma naketa fama kiranshi amma duk maganar guda ce",
    "Ina tunanin ko yana hanya ne, wata k'ila kuma hanyar babu network mai kyau" Sultana ta bashi amsa tana kallonshi cikin soyayya.

    Basu kawo komai a ransu ba a haka suka bar maganar su a tunaninsu ko yana hanya, dan haka cikin kwanciyar hankali bacci ya d'aukesu mai cike da walwala da nishad'i saboda yanda suke jin dad'in zasu shiga kotu da hujjarsu babba, wadda suke ganin da ita wannan shari'ar zata kawo k'arshe.

          *KOTU*

   Yau ta kama ranar Monday bakwai ga watan d'aya, shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai,
    Kotu ta cika kamar zaman farko, harma zan iya cewa a wannan lokacin ma tafi cika sosai,
   Kowa burinsa yaga yanda k'arshen shari'ar zata kaya.

    Bayan mai gabatar da k'ara ya tashi yace
    "Yau  7-1-2017 kotu zataci gaba da sauraron shari'ar data fara a makon daya wuce, wadda Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar k'ara akan zargin da take na sakawa an mata fyad'e wanda yayi silar dakatar da ita daga karatunta".

     Alk'ali yace
    "Barr. Umar da Barr. Sultana ku muke saurare, kotu na fatan kun kawo mata shaidun data buk'ata a zaman farko",
    Shiru ya biyo baya kasantuwar daga Umar d'in har Sultana basu tattare da natsuwarsu,
   Tun shigowarsu kotu suke baza ido dan ganin Dr. Rafiq amma shiru har yanzu baizo ba,
    Kuma gashi idan sun kira lambarsa bata shiga,
    Baki d'aya hankalinsu a tashe yake,
   Ita kanta Ummumah nata hankalin a tashe yake, barin k'awayenta Rabiatu da Zarah da suma basu tattare da tasu natsuwar.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Kde žijí příběhy. Začni objevovat