BABI NA SHA BAKWAI

1.4K 95 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~69~}

       Washe gari da sassafe suka kama haramar zuwa aiki kamar yanda suka saba,
     Kai tsaya Gobarau academy duka zarce sukayi dropping d'in Hafsa sannan suka wuce nasu aikin.

    Kasantuwar weekend akayi aiki ya taru masu sosai a Office musamman ma Umar, hakan yasa bai shigar da maganar ba sai washe gari,
     Safiyar talata kam babu b'ata lokaci ya shigar da case d'in su Ummimah, aka kuma ce nan da sati d'aya za'a shiga kotu.

   Sosai Sultana taji dad'i ta kuma shirya ta tafi gidan su Ummimah dan ta shaida masu halin da ake ciki.

    Masinjan kotu aka aika gidansu Gentle dan yakai sammaci, saboda koda aka fad'i sunanta da sunan iyayenta  kowa ya ganeta, saboda babanta sananne ne sosai kuma yanzu haka ya fito takarar d'an majalissar tarayya.

   Kai tsaye gidan Alhaji Abu Abu ya dosa,
   Sallamah yayi a tangamemen gate d'in gidan amma shiru ba'a amsa ba,
   Saida yayi sallamah sau uku sannan mai gadin gidan ya fito yana taunar asuwaki,
   Hannu masinjan ya bashi suka gaisa sannan yace
   "Meke tafe dakai bawan Allah?",
    "Sak'o ne daga kotu, sammaci ne akace a kawowa masu gidan nan".

   Cike da mamaki mai gadin ya karb'i takardar,
    "Sammaci?" Ya tambayeshi.

   "Ehh sammaci ne, dan Allah a tabbatar da anbawa masu gidan wannan takardar" masinjan ya fad'a tare da juyawa ya tafi.

     Kai kawai mai gadin ya kad'a sannan ya zarce cikin gidan domin ya basu takardar.

    Bayan yayi sallamah yaga Ladi mai aiki tana mopping, mik'a mata takardar yayi yace 'ta bama yallab'ai' sannan ya tafi.

      Saida suka fito karyawa sannan tace
    "Hajia wai ga wannan mai gadi ya kawo yace a bama yallab'ai",
   Bayan ta karb'a tace
   "Alhajina gashi",
Murmushi ya mata yace
   "Bud'e ki karanto min inji".

   A zahiri kuwa ta karanto cewa 'sammaci ne daga kotu ankai k'arar 'yarsu Salmah bisa laifuka da dama'.

    "What!?sammaci? 'Yata aka kai sammaci?",
    Itama Hajiyar tsaye ta tashi tace
    "Lallai wannan munafurci ne? Salmah dake makaranta abunta hankali kwance shine dan rainin hankali za'a kaita k'ara?",
    "Ko tantama babu wannan cinne ne daga mak'iyana, suna so inji kunya akan takarar da zanyi ne",
      "Kaga wai Aisha Abubkar sukayi k'ararta, ga sunan nan a jiki" Momy'n Gentle ta fad'a bayan ta mik'a takardar cike da mamakin wannan al'amarin.

   Karb'a yayi yace
   "Wacece wannan? Aisha?" Tun bai rufe bakinshi ba momy tayi caraf tace
   "Na gane ko wacece, k'awartar nan d'iyar matsiyata ce, saisa tun farko na hanata k'awance da ita amma ta nace lallai sai tayi ita dai tana sonta, wato duk alkhairan da Salmah ta mata da wannan abun zata saka mata? Lallai d'an adam abun gudu ne".

     Cike da b'acin rai Alhaji yace
   "Kenan ma 'yar matsiyata ce ta kai 'yata k'ara? Lallai kuwa reshe zai kife da mujiya, saboda duk abunda take nufinta dashi gareta zai koma, wallahi na rantse sai na d'auko lawyer wanda duk k'asar nan babu kamarshi, sai na nuna masu nafi k'arfinsu, su d'in banza!" Ya rofar da yawu bisa center carpet yace
    "Sai kun wulak'anta I promised" ya jefar da takardar k'asa.

    Mamaki sosai uwar keyi ta d'auki wayarta ta latsa kiran Gentle, bayan ta d'auka ne ta shaida mata duk abunda ya faru,
   Taji tsoro sosai amma a zahiri ta nuna al'ajabinta akan al'amarin,
  Harda kukan munafurci tace
   "kinga illar talakawa Momy, ba irin maganar da baki fad'a min akan kar inyi k'awance da Ummimah ba amma na nace sai nayi, kinga abunda ta bini dashi ko momy?" Ta k'ara fashewa da kukan munafurci, da haka suka kashe wayar bayan uwar ta shaida mata cewa sati mai zuwa za'a fara zaman kotu, dan haka ta hanzarta dawowa gida saboda babanta yace zai d'auko mata babban lawyer,
   Dukda hankalin gentle ya tashi amma sai ta samu sassauci jin lawyer za'a d'aukar mata.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن