BABI NA ASHIRIN DA UKU

1.3K 116 2
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~75~}

    _Wannan shafin naku ne masu tausayin halin da Ummimah take ciki, baki d'aya masoyan littafin *Wata shari'ah* ina k'aunarku, Allah yabar so da k'auna. #onelove#_

     ******

      Saurin mik'ewa Umar yayi ya tari gabansu babu haufin komai haka kuma babu ko alamar tsoro a tattare dashi,
    Kallonshi d'aya daga cikin matan tayi tare da k'ara b'ata fuskarta.

    "How dare you malam!? Ka barmu akan aikinmu muke" ta fad'a cikin hausaeta da bata k'ware ba kasantuwar ba bahausa bace, mini skirt d'in dake bisa makeken k'ugunta kawai ya isa ya tabbatar da cewa ba musulma bace.

     "Hukunci bai yanku ha saboda zamuyi apeal, idan baki yarda ba zaki iya zuwa ki samu alk'ali kuyi magana dashi, bakida hurumin da zaki wabi kwaso jiki domin kama Ummimah ku kaita prison, so you better to leave this place because you are just wasting your time, babu inda zaku tafi da ita" Umar ya fad'a cike da zafin rai.

     Jin maganar da Umar yayi yasa ta sauke hannun dake rik'e da handcuff d'in,
    Juyawa baya tayi hakan yasa suma sauran suka juya, tunda suka tafi basu sake dawowa ba.

   Ummimah kuwa har yanzu bata farfad'o ba,
    Mamah baki d'aya hankalinta ya tashi, bata fatan ta rasa 'yarta kamar yanda ta rasa mijinta da sauran 'ya'yanta guda biyu.

   Zarah da Rabiatu kuwa idonsu har ya kumbure tsavar kukan da suka sha, gasu ga Ummimah inda take kwance sai k'ara allawadai da wannan al'amarin sukeyi.

    Saida Sultana ta gama kwasar kukanta sannan ta taso,
   Inda suke ta nufa ta tsuguna tana fad'in
    "Dukkan tsanani yana tare da sauk'i, haka zalika komai yayu zafi maganinsa Allah,
   Ya kamata duk koke koken nan mu ajiyesu,
    Muyi k'ok'arin sama mata lafiyarta dan sam bai kamata mu barta anan ba,
    Gobe Tuesday insha Allahu zamu d'aukaka k'ara,
     Sai mu dage da addu'ah insha Allahu zamuyi nasarah,
    Saboda Allah yana tare da mai gaskiya".

    "Hakane Sultana, Allah yayi mana jagora, Allah kuma ya tashi kafad'un Ummimah" Mama ta fad'a tare da share hawayen fuskarta.

   Zarah da Rabiatu ne suka kinkimi Ummimah,
  Kai tsaye bakin motar Umar suka kaita,
   Tun daga nesa ya bud'e masu kasantuwar mai amfani da remote ce,
   Bayan sun sakata ya bama Sultana key d'in yace 'ta tafi dasu gida, saboda shi zaije wurin justice suyi magana dashi akan d'aukaka k'arar da suke so suyi'.

    Har Sultana ta tada mota tabar wurin su Gentle suna tsaye suna kallonsu,
   Mamaki had'e da haushi ne ya mamayesu ganin Ummimah zata tafi ba tare da an tafi da ita prison ba.
    

     A ranar daida Umar ya gama komai daga kotunsu ya miyar da maganar court of apeal,
    An yankar masu rana talatin ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai zasu fara zaman kotu.

    Umar yaji dad'in yankar masa kwanakin da akayi da yawa, saboda yana tunanin hakan zai bashi damar yin bincike cikin natsuwa har ya samo manyan hujjojin da zai gabatarwa kotu wanda zasu gamsar da kotu cewa lallai Gentle itace tasa akayiwa Ummimah fyad'e.

*****

      "Dan Allah ku sakarmin uwata hakanan, wallahi ita kad'ai gareni, dagani sai kannena biyu ta haifa, babanmu ya mutu tun muna yara, itace tasha wahala damu tun daga bokonmu har islamiyyarmu,
     Batak'i ta rasa farin cikinta amma ta faranta mana ba,
    Ta rasa komai nata a dalilin karatuna na likitanci,
    Ba zanso na rasata ta dalilin aikin likitancina ba, dan Allah ku saketa ni na yarda kuyi min duk abunda kukaga dama na amince". Dr. Rafiq ne ke wannan maganar fuskarshi share share da hawaye.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now