BABI NA SHA HUDU

1.2K 107 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~66~}

    Duk kukan da mukeyi baisa mutanen sunji tausayinmu ko d'aya ba,
   Cike da rashin imani suka ringa watsi da baki d'aya kayakinmu,
    Ga gawar Afrah cikin buhu ga kuma Baba da yake kwance baya ko alamar numfashi,
    Kukanma nemanshi nayi na rasa, sai mama daketa ambatar sunan baba amma har yanzu ko alamar motsi bayayi.

    "Ku tashuwa min daga k'ofar gida bana son ganinku, idan ba haka ba kuma a wulak'antaku cikin unguwar nan" mutumin mai gidan hayar ya fad'a cike da izgili da gadara.

     Mutanen da suka kawo gawar Afrah d'aya daga cikinsu yace
    "Kai kuwa bawan Allah ka tausaya masu mana, bakaga hakinda suke ciki ba? Ka barsu suji da d'aya mana, tunda dai kasa an fitar masu da kaya ai sai ka shafa masu lafiya haka, tunda mai gidan nasu ma gashi nan kwance bama asan halin da yake ciki ba".

     A wulak'ance yace
    "Babu ruwana da halinda suke ciki, gidana  kawai na sani kuma na basu minti goma subar harabar nan, idan kuma basu bari ba duk abunda na masu su suka ja".

    Cikin rashin tsoro na tashi tsaye,
   Ko alamar kuka babu a idona na dubeshi ido cikin ido nace
    "Kaga malam ka kama kanka, na kula kai baka da tunani kuma baka san darajar d'an adam ba,
      Munfi k'arfin ka wulak'antamu wallahi,
   Sannan kuma duk halinda ka tayar damu daga Allah ne, bawai dan Allah baya sonmu bane kaga ya barmu a haka,
    Jarabtace kuma babu wanda yafi k'arfinta,
   Kaima bakafi k'arfin Allah ya jarabceka ba".

    Dariya ya k'yalk'yale da ita tare da fad'in
    "'Yan mata Kenan, dama an bani labarinki tun kafin inzo, wallahi kinji na rantse, idan na tafi na dawo na sameku anan zakiyi mamakin abunda zan maku, ni nafi k'arfin ki fad'a min wannan maganganun marasa dad'i" yana gama fad'in haka ya juya ya tafi,
    Gardawansa ma suka mara masa baya.

    Sai a lokacin na sake jin wani irin kuka maras control yazo min,
   Wannan mutanen su suka ringa rarrashinmu tare da kwashe mana kaya suna kaiwa gidan d'aya daga cikinsu,
     A gidanshi aka sallaci Afrah, a lokacin har ankai Baba asibiti domin duba lafiyarsa.

     Bayan ankai Afrah ne muka tafi asibiti,
   Mukayi sa'a kuwa Baba ya farfad'o,
    Farin ciki mukayi sosai Mama ta matsa kan gadon ta rik'e hannunshi,
    Da k'yar yake iya bud'e idonshi sai hawaye ke fita daga idonshi,
   A hankali ya iya bud'e bakinshi tare da furta
    "Ku yafemin nasan tawa ta k'are,
    Wanda suka zalunceku ku barsu da Allah shi zai maku sakayya,
    Ku rik'e addu'ah a ranku kamar yanda Baffa da Hassu suka rik'i addu'ah kuma tayi masu jagora a cikin *Dodon Jatau,* duk wanda ya rik'i addu'ah baya tab'ewa,
    Sannan duk wanda yazo neman aurenki Aishatu karki b'oye masa abunda aka miki, bana son zalunci ya shigo ciki,
   Idan kika fad'a masa yaji zai iya aurenki shikenan, idan ba zai iyaba kuma sai kici gaba da neman zab'in na gari".

   Kuka muke sosai nida Mama har babu mai rarrasar wani,
    Da k'yar baba yaci gaba da fad'in
    "Ku kuka da rayuwarku, kuyi k'ok'arin rik'e babunku, kar ku jefa kanku a wani hali saboda abun duniya" tari sosai yaci k'arfinshi,
    Jini ne yabi bayan tarin saigashi gullama gullama yake fita abun tausayi,
   Salati muka d'auka nida mama, hakan yasa shima baba ya d'auka yanayi,
    Muna direwa shima yana direwa, bai iya furta komai ba sai ajiyar zuciya da yayi wanda shine fitar ranshi.

     "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai muke fad'i nida Mama.

    "Bai mutuba wallahi da ranshi, likita! Likita kazo ka tabbatar mana da Abubakar bai mutu ba, nasan bazai tab'a tafiya ya barmu ba" Mama ta k'ara fashewa da kuka.

        Bayan likita ya shigo ya tabbatar mana da Baba ya mutu, hakan yasa muka k'arfafa kukan namu,
   Da k'yar muka fita daga d'akin saboda gadon da gawar baba take mama ta rik'e da k'arfin gaske tana kuka.

   Sai washe gari aka kai Baba, kasantuwar yamma tayi lokacin da ya rasu d'in, ko kafin akai gawar a shiryata ma duhu ya fara.

      A gidan mutumin daya jagoranci gawar Afrah da Baba muka zauna,
   Bayan munyi sati biyu zuwa uku a gidanshi a lokacin har mun fara dayayewa ya samar mana wannan gidan da muke ciki anan unguwar Tudun wada,
     Anan muke rayuwa nida Mamana, sosai kawu Nasiru (wanda ya taimakemu) yake kula damu tamkar 'yan uwanshi na jini,
     Duk lokacinda nama mama maganar mu tafi wurin danginta kona Babana sai tace a'a, saboda lokacinda zasuyi aure duka danginsu basu soba,
   Iyayenta sukace inhar ta auri babana to babusu babu ita har abada,
   A gidansu babama haka akace masa,
    Sun aminta da hakan sukayi aure sannan suka bari Kaita suka dawo cikin Katsina.
    Wannan shine labarina, ina fatan zaki taimakemu inhar kinada halin yin hakan, ki k'watomin 'yar uwata inhar tana raye". Ummimah na gama fad'in haka ta fashe da kuka.

   Mama ta share hawayenta tace
    "Tabbas duk abunda Aishatu ta fad'a miki gaskiya ne, cutarmu akayi amma an nuna anfi k'arfinmu ta hanyar dukiya, bamuda galihu ko kad'an".

    Cike da tausayi Sultana tace
    "Ki daina fad'in bakuda galihu Mama, Allah yana sonku ai, kuma insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe tunda har Allah ya jefoni a rayuwarku".

     "To waima waye ya fad'a miki muna cikin wani hali?" Mama ta tambaya saboda abun ya bata mamaki.

    "Ni kaina ban saniba Mama, ya b'oye kanshi koma waye,
   Amma kuma yanzu duk ba lokacin wannan bane,
    Na d'aukar maku alk'awarin zan taimakeku bakin k'arfina, sannan kuma mijina babban Lawyer ne am sure shima zai taimaka min dan ganin mun gurfanar da Salmah a gaban alk'ali".

    Koda duka duba har dare yayi duk basu sani ba,
   Da hanzari ta duba wayarta tayi kicib'us da 21 missed calls,
    Tashi tayi ta masu bankwana sannan ta fita ta shiga motarta tana k'ok'arin dialing number'n Umar mijinta.

   _gasuwa tare da godiya ga masoya labarin *WATA SHARI'AH* aduk inda suka, nagode da yanda kuke nuna kulawarku gareni musamman 'yar uwata ko ince Aunty'nmu *Ashnur Pyar,* Allah yabar zumunci da zaman tare._



°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                 NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now