BABI NA SHA BIYU

1.3K 99 1
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~64~}

  _Na tayaki murnar kammala wannan littafin naki wanda ya ilimantar gamida fad'akarwa, lallai littafin *HARAMTACCEN ZAMA* ya kawo darussa da dama, fatana a kullum Allah ya k'ara miki baseera 'yar uwata ko ince aminiyata *(Rabiatu sk msh AKA Babymsh)* #onelove#_

*****

     Tun daga nan ban k'ara sanin abunda yake faruwa ba, sai farkawa nayi na ganni kwance kan gadon asibiti, gefena Zarah da Rabiatu ne sunyi tagumi suna jiran tsammani.

    Kallo d'aya na masu suka bala'in bani tausayi, domin kuwa na k'ara tabbatarda sune k'awayena na gaskiya wanda suke k'aunata.
    
     Basu ankara da farkawata ba saidai shesshek'ar kukana sukaji,
   Da hanzari kuwa suka mik'e tsaye, Rabuatu ta furta
    "Alhamdulillah tunda kun tashi, sannu Aisha",
   Kai kawai na d'aga mata ina hawaye sosai saboda k'ara tunowar da nayi wai yau nice aka kora daga makaranta, an cuceni kuma an hanani kuka.
   
    Zarah ta zaro d'an kwalinta daga kanta dake cikin hijabi ta mik'o min
     "Bana son kina kukan nan Aisha, ya kamata ki d'auki k'addara saboda *KOWA DA K'ADDARARSA,* ba wai Allah baya sonki bane yayi miki hakan, kawai dai *JARRABTARKI KENAN* kuma ina fatan zakiyi k'ok'arin ki cinye wannan jarabawar,
    Wanda suka cuceki kuma ki barsu da Allah shi zai miki sakayya, kiyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareki, ungo wannan ki share hawaye" ta mik'o min d'an kwalin nata.

     K'arba nayi na fara share hawaye saidai kuma da zarar na share sai wani ya fito,
   Da k'yar na iya furta
  "Babu komai k'awayena, na yarda na kuma d'auka cewa *K'ADDARATA CE* banida hanyar maganceta, na barwa Allah komai saboda shine zai saka min, dan Allah wace asibiti nake?"
  Zarah tace "inda aka kawoki ne last time, munje School clinic ank'i karb'arki sunce saboda wai ke yanzu ba student bace".

      Saurin mik'ewa nayi dukda ciwonda duk gab'ob'in jikina suke min,
     "Na gwammaci in mutu akan in zauna a asibitin nan, Zarah mesa kuka kawoni nan? Kunsan kuma irin sharrinda suka k'ullamin, su da kansu suka rubuta takardar k'arya cewa an zubarmin da ciki, basu fidda takardar gaskiya ta cewa fyad'e akamin ba" na k'ara fashewa da kuka bayan Rabiatu ta rungumeni a jikinta itama kukan take sosai tana k'ara jin tsanar Gentle a ranta, saboda tasan duk sharrintane da makircinta.

     Duk maganganunda mukeyi ashe a kunnen Dr. Rafiq ne, shigowa yayi jiki babu k'wari ya nufo inda muke tsaye har yanzu ban saki Rabiatu ba,
    "Ka fita daga nan bana son ganinka, kai mugune kuma munafuki, ka munafurceni ka gwadamin kai mutumin kirkine ashe ba haka bane sai naga sab'anin haka, ka fita kafin in fasa maka kai da kwalbarcan" na nuna kwalbar malt dasu Zarah suka kawo min.

         "Nasan zayyi wahala ki yarda dani, amma dan Allah inaso ki ajiye hankalinki ki saurari bayaninda zan miki" ya fad'a bayan ya k'ariso inda muke,
    "Ki koma ki zauna har yanzu jikinki bayyi k'wari ba".
    Cikin zafin rai na saki Rabiatu, a tsiwace nace
    "Bazan saurarekaba Dr. Saboda bakada abunda zaka fad'a min in yarda dakai, wallahi ka bani kunya, ka shirya k'arya kanaji kana gani bayan kuma ga gaskiya, to an koreni kun samu abunda kuke so, sai kuji dad'inku da kyau kaida wanda suka sakaka" ina gama fad'in haka na jawo hijabina na saka,
    Hanyar fita na kama ina kallon yanda Dr. Rafiq yayi shiru alamar yaso in saurareshi amma sam nak'i bashi damar yin magana saboda babu abunda zai fad'a min in yarda dashi.

     Bin bayana Zarah da Rabiatu sukayi,
    Purse d'ita Rabiatu ta bani tace
    "Anata kiranki daga gida, ban d'aukaba saboda bansan abunda zan fad'a masu ba, bana son tayar masu da hankali".

    Karb'a nayi na zaro wayar daga ciki na danna kiran Baba,
    Bugu d'aya ya d'auka hankalinshi tashe yace
    "Aishatu ince dai lafiya kike, tun jiya nake kiranki inji ko kin sauka lafiya",
    Gabana ya fad'i sosai na k'irk'iro murmushi,
    "Na sauka lafiya Babana, wayar na jefa a cikin jakata can k'asa, sai yanzu na ganota",
     "To masha Allahu, dama sauka lafiyar ake fata ai, ina Salmah kun had'u ko?",
    Har wayar da Baba ma ji nayi bana so, tsinke wayar nayi kawaa naci gaba da kukana tare da kashe wayar baki d'aya.

     Bayan mun bar asibitin kai tsaye makaranta muka wuce,
   A bakin gate na tsaya su kuma suka shiga ciki domin su kwaso min kayakina,
    Ina nan tsaye saiga wata mota tayi parking a daidai bakin gate d'in kasantuwar ba'a barin mota mai tint shiga cikin harabar makaranta,
      Gentle ce ta fito sanye da irin skirt d'in nan bak'i mai b'arka doguwa daga gabanshi, sanye take da riga 'yar k'arama orange bakin hannu da kwalar rigar anyi ado da burberry bak'i, sai tad'an yafa d'an kwalin after dress k'arami,
     Babu wanda zaice ita bahaushiyace sai idan dama ya santa,
    Dariya had'e da shewa ta d'auka a lokacinda taga ina kallonsu,
   Cike da b'acin rai na kawar da kaina daga garesu itada saurayinta.

    A cikin hakane su Zarah suka iso, kallo sukabi Gentle dashi Rabiatu ta watsa mata harara,
    Wata dariyar ta saka bayan sun matso inda muke ita da saurayin nata.
    "Tunda an koreki ai saiki tattara tsimmokaranki kibar makarantar saboda ba anan aka haifi uwarki da ubanki ba, sai a koma aci gaba da cin k'anzo da tuwon dawa,
   Ai dama na fad'a miki nafi k'arfinki, wanda ya fikima nafi k'arfinsa,
    Talent University tamuce mu keda ita, saboda malaman cikinta namune kaf mun gama dasu, tun daga junior har senior lecturers d'in, ke har senate mun gama da 'yan cikinta saboda damu suke damawa".

     D'aga hannu nayi na d'auketa da kyakkyawan nari saboda maganganun da sukemin sun isa haka,
     Kanta ta d'ago ta kalleni cike da mamaki tace
    "Ni kika mara Ummimah?",
     "An mareki d'in wacece ke da ba za'a marekiba? Ki sani yanzu ni ba d'aliba bace a makarantar nan, inada damar yi miki komai ba tare da naji haufin wani abuba, idan kikaci gaba da fad'a min magana kuma in k'ara miki wani".

    Saurayin natane ya d'aga hannu da nufin rama mata,
    Dakatar dashi tayi tareda fad'in
     "K'yaleta Bash, nasan maganinta",
    Ta juyo gareni
   "Ke kuma sai kinyi regreting d'in marina da kikayi, ba gida zakije ba? Ki tafi" tana gama fad'in haka ta wuce cikun School abunta, shima saurayin nata yabi bayanta.
     "Karki damu k'awata, babu abunda zaki gani a gida sai alkhairi, kar kiji komai ki rabu da ita Allah ya fisu" Zarah ta fad'a cikin sigar rarrashi.
       Hak'uri sukaci gaba da bani har lokacinda keke napep tazo ta sauke wasu, tsayarmin da ita  Rabiatu tayi,
    Da kuka muka rabu dasu, har mukabar wurin suna d'aga min hannu,
    Saida sukaga tafiyarmu sannan na hangesu sun shiga cikin makaranta.

    Wani sabon kukan ne naji yana saukomin,
   Mai napep d'in yace
    "Baiwar Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, tunda na d'aukoki kike kuka kar wani ciwon ya kamaki",
    "Karka damu bawan Allah, kaidai kayi aikinka" na fad'a cikin muryar kuka.
      Tashar mota ya kaini babu b'ata lokaci kuwa na samu motar Katsina,
     Mun jima bata cikaba kasantuwar yamma tayi babu matafiya sosai,
    Sai wurin k'arfe biyar sannan motar ta tashi.
     K'arfe tara da rabi na dare muka shiga Katsina,
   Nice banje gidaba sai kusan goma da rabi kasantuwar abun hawa da yake wahala idan dare yayi,
    A bakin gidanmu napep ta saukeni,
   Saidai kuma mutane dana gani mak'il k'ofar gidan,
   Har shiga kanta da k'yar na sameta,
   Duk wanda ya kalleni saiya gyad'a kai wasu suna hawaye.


   _Alhamdulillah! Nagode sosai da addu'o'inku masoyana, yanzu kam nagode Allah na samu sauk'i, idona ya fara warkewa, da wanda suka kirani a waya da wanda suka min addu'ah ta chart duk ina godiya musamman aminiyata *ZARAH BB,* nagode once again._



°•°AKA°•°Princess Amrah😘
                   NWA

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now