BABI DA ASHIRIN DA SHIDA

1.2K 93 2
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

                

                   {~78~}

_wannan shafin tukuici ne gareki my dear *Ummu Shureym,* hak'ik'a ke masoyiya ce ta gaske, Allah yabar soyayya da k'auna ya raya mana Shureym bisa tafarkin sunnah. Amrah LYSM #Onelove#_

*****

      Mamaki fal a fuskar Umar yake kallon mutanen dake cikin matrix d'in,
   A hankali mutumin ya fito bayan ya kashe motar,
   Murmushi yayi tare da mik'a masa hannu yace
    "Assalamu alaikum",
   Shima hannun ya mik'a masa amma kuma bai amsa sallamar ba saidai kallo kawai da yake binsa dashi.

     "Ka daina mamaki Barr. Umar, nine d'in dai Dr. Rafiq wanda kukayi dashi zaije kotu ya bayar da shaida sai kuma wani dalili ya hana, amma yau a shirye yake daya bayarda shaidar duk abunda ya sani kuma tsakaninshi da Allah".

    Murmushi Umar yayi yace
   "ina ka shiga Dr. Rafiq? Aimu munyi zaton ko kaima sun siyeka da kud'i ne, tuni aka yanke hukunci amma mun d'aukaka k'ara, yanzu haka shirin tafiya kotun muke saboda yaune zamu fara zama".

   Muryar mace ya jiyo tace
   "Ba za'a tab'a siye Rafiqu da kud'i ba d'an nan, shari'ar nan tana ransa kawai dai an nuna anfi k'arfinsa ne..." Umman Rafiq ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'awa Umar,
   Sultana ma tana tsaye tana saurarensu wani irin dad'i taji a ranta,
   Itakam dama tayi mamakin rashin zuwansa kotun, ta tabbatar da akwai wani babban dalili daya hanashi zuwa lokacin da ake buk'atar ganinshi.

   Har k'asa ta duk'a ta gaishe da Umman Rafiq sannan ta gaishe da Rafiq d'in ma,
      Motarsu suka koma Sultana ma ta koma ta shiga tata wadda su Ummimah ke ciki suna hangen  duk abunda yake faruwa amma kuma basu san kome ake fad'i ba.

   Bayan ta shiga ta labarta masu duk abunda ya faru, hamdala Mama tayi sannan tace
    "Allah majik'an bawa, dama shaidarshi ake nema kuma gashi Allah ya kawoshi, Allah dai ya kawo mana k'arshen wannan shari'ah ya bawa mai gaskiya nasarah",
    "Ameen" su duka suka amsa dashi sannan Sultana ta tayar da motar,
   Umar ne gaba sai Dr. Rafiq a bayanshi,
  Sultana kuma a bayan Rafiq, a hankali suke tafiya har suka isa court of apeal.

     Sun samu motoci da yawan gaske a pake, hakan ya tabbatar ma Umar da cewa su kad'ai ake jira,
   Savoda tun k'arfe takwas akace suzo za'a fara shari'ar yanzu kuma gashi har takwas da rabi ta wuce.

   A hanzarce suka zira rigunansu sannan suka shiga,
    Wuri d'aya su Sultana suka zauna da Umman Rafiq da k'annenshi biyu,
   Sultana da Umar kuma suka tafi inda aka tanada domin zaman lauyoyi.

    Bayan sun zauna baifi da minti biyar ba alk'ali ya iso,
   Mazauninsa ya zauna sannan mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar.

     "Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar wadda ta kawo k'ara da kuma Salmah Abubakar wadda ake k'ara" alk'ali ya fad'a tare da yin d'an rubutu a takarda.

   A hankali Ummimah ta taso ta tsaya cikin akwatin tuhuma,
   Salmah ma tasowar tayi ta tsaya itama a cikin akwatin tuhuma wanda ke kusa dana Ummimah.

    "ba sai an tsaya wani dogon bayani ba, kamar yanda kowa ya sani cewa wannan k'ara ce aka d'aukaka, dan haka zamu so wanda suka kawo k'arar su tashi suyi bayanin dalilinsu na d'aukaka k'arar sannan su bamu hujjarsu ta farko".

     Cike da natsuwa da kamun kai Sultana ta tashi tsaye,
   "Sunana Barr. Sultana Saddam Bakori, a tare dani akwai Barr. Umar Mohd Bashir, mune wanda muka d'aukaka k'ara,
   Dalilinmu na d'aukaka k'ara kuwa shine; an yanke hukunci a zamanmu na kotun daya gabata wanda kuma hukuncin bai mana ba,
   Shine muka d'aukaka k'ara a wannan kotu mai adalci tare da hujjojinmu wanda muke fatan kotu zatayi masu duba ta yanke hukunci ga mai laifi".

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now