BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

1.2K 98 5
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~77~}

_Wannan shafin naki ne masoyiyata *Ummu Nawal,* nagode k'warai da yanda kike kula tare da bibiyar wannan labarin, Amrah luvs youh much #onelove#_

****

     Washe gari.

Tunda sassafe Haydar ya tashi daga barci, ido ya bud'e bayan ya lalaubi Safiyya bai jita ba,
    Daga can gefe ya hangi Hafsa tanata sharar bacci abunda cikin kwanciyar hankali.

   Zaune ya tashi jikinshi zafi rau yana fad'in
   "Aunt Shafiyya" amma shiru baijita ba dan a tunaninshi ko tana toilet ne,
    Sauka yayi daga kan gadon ya fara knocking toilet amma har yanzu baiji alamarta ba.

   Kuka ya fasa da k'arfi tare da barin d'akin ya doshi kitchen ko tana can amma saa b'uruntun Sultana daya jiyo tana had'a break fast saboda sammako zasuyi a kotu.

    K'arar kukanshi data jiyo yasa tayi saurin fitowa ta tareshi dan dama a tsarinta bata barin yaro ya shiga kitchen saboda tana amfani da gas da electric,
    "Haydar wats your problem?" Ta tambayeshi bayan ta rungumeshi.

    "Momy banga Aunty shafiyya ba tunda na tashi" ya fad'a cikin kuka.

    "Kajika Haydar da wata magana, yo ina zataje kuwa? May be ko ta shiga toilet ne yasa baka ganta ba, kayi shiru ka daina kukan nan ba nisa tayi ba" Sultana ta fad'a cikin sigar rarrashi tana rarrasar d'anta Haydar.

     Da haka har ta samu yayi shiru ta kwantar dashi parlor kan three seater wani baccin ya d'aukeshi,
   Murmushi tayi tare da nufar komawa kitchen saiga Ummimah ta fito,
     "Ina kwana Aunty?" Ta fad'a bayan ta duk'a har k'asa.

    "Lafiya k'alau Ummimah, ya jiki ya warware ko?",
    "Alhamdulillah ya warware sosai Aunty, yaune zamu fara zama ko?",
    "Ehh yau ne kuma yanzu ma bada dad'ewa ba, ance k'arfe takwas ta mana can, saisa na tashi na fara had'a break fast dan karmu makara",
    "Ok Allah ya taimaka ya bamu nasarah Aunty, baki ba zai iya gode maku ba saboda duk wata hanya da zamubi domin gode maku kun wuceta, addu'ah kawai itace ta dace daku, Allah ya saka maku da alkhairi ya rabaku daga sharrin shaid'an daku da zuriyarku",
    "Ameen Ummimah, muci gaba dai da addu'ah insha Allahu zamu dace".

   Murmushi tayi sannan tace
   "Muje in tayaki aikin Aunty".

   Tare suka shiga kitchen d'in sukaci gaba da aiki sunayi suna fira,
    Jin har yanzu Safiyya bata fito ba kuma abunda ba halinta bane yasa Sultana bin sawunta,
    A hanyar fita kitchen Zarah da Rabiatu ma suka biyosu,
   Bayan sun gaisa Zarah tace
   "Munzo mu tayaki aikin ne Aunty".

   Murmushi fal a fuskarta tace
   "Ai dama kunyi zamanku wallahi har mun kusa k'arisawa, nasan 'yan mata da son barcin safe",
    "Babu komai Aunty aima mun tashi tun d'azu har mun shirya" Rabiatu ta fad'a tare da shigewa kitchen d'in Zarah tabi bayanta.

     D'akin Safiyya ta shiga da nufin taga ta shirya Hafsa amma da mamaki sai taga sab'anin haka,
    Hafsa kwance har yanzu bata tashi ba sannan kuma babu Safiyya,
    Mamaki taji sosai sannan tace
    "Safiyya" amma shiru babu amsa,
    Bakin toilet d'in ta nufa tace
    "Wai lafiyanki kuwa Safiyya?" Nan ma dai shiru.
   Bankad'a k'ofar tayi taga wayam babu kowa a ciki,
   Dawo da kallonta tayi a gado saima yanzu ta kuka da jini dake kwance bisa zanin gadon,
    Hankali tashe ta matsa inda jinin yake ta tabbatar da jinin gaske ne.

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now