BABI NA SHA SHIDA

1.3K 95 0
                                    

WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

            Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                  (Jan. 2017)

*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

               
                   {~68~}

    
      Washe gari ta kama ranar lahadi babu aiki,
   Hakan yasa da sassafe Sultana ta gyara gidanta ta bad'e ko'ina da k'amshi,
    D'akin su Hafsa ta shiga ta samu Haydar baya nan sai Hafsa kwance a gadonta, hakan ya tabbatar mata da yana d'akin Safiyya.

   Kai tsaye d'akin Safiyya ta nufa,
   Ta samu Haydar zaune bisa cinyar Safiyya sai zuba mata surutu yake ita kuma tana dariya.
   Ganin Sultana yasa Safiyya ta sauke Haydar daga kan cinyarta ta tsuguna har k'asa tace
   "Ina kwana momy?".

   Da fara'ah Sultana ta amsa da
   "Lafiya k'alau Safiyya, an tashi lafiya?",
   "Lafiya Aunty, ya gajiya?",
   "Ba gajiya, naje d'akin su Haydar ne na samu bayanan, na tabbatarda nan yayo",
    "Ehh kuwa nan yayo kam, cikin magagin barci ma yazo, Haydar" ta miyar da kallonta ga Haydar.

   Hakan yasa ya fahimci inda ta dosa,
   "Good morning momy" ya fad'a bayan ya duk'a har k'asa.

   "Morning my boy, ka tashi lafiya?",
   "Lafiya momyna" ya bata amsa yanayi yana wasa da warwaron hannun Safiyya.

   "My boy anyi sallah kuwa?",
    "Ehh momy Aunty Safiyya tasa nayi",
    "Ok muje ayi wanka" ta d'aukeshi suka tafi d'akinsu.

   Tashin Hafsa tayi tayi sallah kafin ta gama har Sultana ta gama shirya Haydar.

    Bayan ta gama shiryasu duka ta fita parlor, dama kuma ta gama had'a break fast tun tashinta daga bacci,
   Koda ta shiga d'akin Umar ta tayar ya tashi shima har ya shirya,
   Murmushi k'unshe a fuskarta tace
   "Barka da tashi mai gidana na kaina".

   Murmushin ya mata shima yace
   "Yauwa 'yar aljannah, kin tashi lafiya?",
    "Lafiya k'alau honey, break fast is ready, kai kawai muke jira",
    "Alright wifey, idan mun gama akwai maganar da nake so muyi dake",
   "Ok ba damuwa". Suka fita daga d'akin tare da nufar dining area.

    Bayan sunyi nat Umar yace
   "Maganar jiyan nan ce, so inaga kamar ya kamata mu koma gidan tare dake, saboda akwai 'yan tambayoyin da nake so na masu kafin mu shigar da maganar kotu, saboda a tunanina ba zamusha wata wahala ba a wannan shari'ar".

   "Hakane honey, na shirya dama muje kawai, amma kuma jiya nama su Hafsa laifi, ina so muje tare dasu daga can mu wuce yawo dan in kankare laifina" ta fad'a bayan ta kalli Hafsa ta saki murmushi.

     "Ok muje?" Ya tambayeta  
      "Ehh muje" ta shiga d'akin Safiyya,
    Abunda zata dafa na rana ta shaida mata sannan ta fito da sauri saboda su Haydar har sun fita parking area ita kawai suke jira.

     Kai tsaye gidansu Ummimah suka dosa,
  A k'ofar gida Umar ya tsaya bai shiga ba, sai Hafsa da Haydar ma a cikin mota basu fita ba,
    Sallamah tayi tare da jinkirtawa har saida aka amsa sallamar.

   Kamar jiya ta samu Ummimah tayi tagumi saidai kuma yau babu hawaye, amma kuma kallo d'aya za'a mata a fahimci tsantsar tashin hankali a tattare da ita,
   Bayan sun gaisa ne tace
   "Tare nake da mai gidana, Barrister Umar Mohd Bashir",
     "Ki shigo dashi ciki mana Sultana" Mama ta fad'a had'e da d'an guntun murmushi.

   Fita tayi kuwa babu jimawa sai gasu sun taho harda su Hafsa,
    Bayan sun shiga ciki Umar ya gaishe da Mama ta amsa cikin dattako,
   Ummimah ma ta gaisheshi bayan ta saka hijabinta,
    Ruwa ta kawo masu a tasa mai fad'i sannan ta koma mazauninta ta zauna.

    D'aukar ruwan Umar yayi yasha kad'an sannan ya ajiye.

    "Mama na samu bayanin duk halin da kuke ciki kuma mun d'auki alwashi nida matata insha Allahu zamu taimakeku, kuma da yardar Allah zamuyi nasarah, nazo ne saboda akwai bayanin da nake so na samu daga bakin Aishatu, saboda gobr Monday nake son shigar da maganar kotu".

   "To babu damuwa Umar, muna saurarenka" Mama ta fad'a bayan ta sauke hannunta daga tagumin da tayi ta fuskanceshi.

   "Ummimah tambayarki zanyi,
   A lokacin da aka kaiki asibiti karo na biyu, kin saurari wani bayani daga bakun Dr. Rafiq?".

    Ajiyar zuciya ta sauke tare da fad'in
   "Ban saurareshi ba gaskiya, saboda baya da abunda zai fad'a min in yarda dashi duk da insisting da yayi akan lallai sai ya fad'a min amma ban yarda ba".

    "Kinyi kuskure Ummimah, da kin sani ki saurareshi ai kiji abunda zai fad'a miki, kinga ko nan da mun samu eata hujja, amma babu komai, shi Dr. Radiq d'in d'an can Jalingo d'in ne?",
    "Wallahi ban sani ba, na dai san wata private hospital ce yake aiki, kuma da alama tasuce shida abokin aikinshi Dr. Khalid",
    "To yanzu kuna ganin Dr. Rafiq zai iya saurarena idan na sameshi da maganar?",
    "Bazan iya ganewa ba, saboda na kula Dr. Rafiq munafuki ne, yanada canja magana, kaga dai daga farko ga yanda mukayi dashi, daga k'arshe kuma wai daga asibitin takardar shaidar zubarmin da ciki tazo, kaga kuwa ai babu gaskiya".

     Kallon Ummimah yayi a karo na farko tare da sauke ajiyar zuciya,
    "Zan sameshi zamuyi magana dashi, insha Allahu nasan zamuyi nasarah",
    "To shikenan Uncle Allah ya tabbatar da hakan"
     "Ameen" duka suka fad'a.

    Sultana tace
   "To yanzu ya za'ayi asan address na asibitin?",
   "Sunan asibitin KADRAQ CLINIC, ba zatayi wahalar ganewa ba, batada nisa da Talent University",
   "Ok good" Umar ya fad'a bayan ya mik'e tsaye yama su Sultana nuni da su tashi su tafi.

   Bankwana sukayi sannan suka fita cike da tausayin rayuwar su Ummimah.

      Royal bakeries duka zarce daga can, suka kwashi ice cream kala kala da chocolates masu yawan gaske sannan Umar ya biya kud'in suka nufi hanyar fita.
    Suna fita sukaci karo da wasu matasa su biyu a buge da gani sunsha sunyi tatul,
   Kallo Sultana da Umar duka bisu dashi,
    "Waiku ya akayi kuke kallonme ne? Ko kun sanmu ne?" D'aya daga cikin 'yan mayen ya fad'a cikin maganarsu ta 'yan maye.
    D'ayan ma yace
     "Sai kallonku sukeyi hehe, ga katina ka d'aukeni aiki kaji?" Ya mik'awa Umar complimentry card d'inshi.
   Da k'arfi d'ayan yaja hannun abokinshi suka k'arisa cikin restaurant d'in,
    Bin katin da kallo Umar yayi,
   Degree holder ne kyakkyawa dashi a hoton dake jiki,
    Ga phone number a jiki da address d'inshi.

      "Rayuwa kenan, Allah ya shirya mana zuri'ah, kinga wannan matashi dashi da iliminsa amma ya kama sana'ar shaye shaye duk ya wulak:anta rayuwarsa" Umar ya fad'a cike da tausayi yana k'ara kallon katin.

    "wallahi kuwa honey, Allah dai ya shirya, kawo katin in gani" ta mik'a hannunta ta karb'i complimentry card d'in matashin.

     "Sulaiman Usman Saraki" ta furta bayan ta kalli katin,
    "To shi a tunaninshi idan ma d'aukar aikin ne sai a rasa wanda za'a d'auka saishi?  Duk mutanen kirkin nan dake neman aiki saishine za'a bama aiki?",
     "Wallahi kuwa, mu tafi su Hafsa har sun gaji da tsayuwa" suka isa inda suka ajiye motarsu,
   Purse d'inta ta bud'e ta jefa card d'in sannan suka kama hanyar gida.

   Har suka isa gida  basu daina mamakin 'yan shaye shayen nan ba, suna k'ara tausaya masu.

     "To yanzu honey ya kake ganin za'ayi? Zamu fara shigar da maganar kotu ne sannan kaje wurin likitan ko kuwa?"  Sultana ta tambayi Umar.

    "Nafi so mu fara shigar da maganar har sammaci akaima su Salmah sannan in fara duk wani bincike" ya bata amsa.

       Kamar Sultana tana son yin magana sai kuma ta fasa,
    Safiyya ta kawo masu abinci sukaci kafin nan la'asar tayi ta shirya Hafsa domin zuwa islamiyya.

      _Gaisuwa gareku 'yan k'ungiyar *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya k'ara zumunci yabar zaman tare. #onelove#_


°•°AKA°•°Princess Amrah😘

WATA SHARI'AH (COMPLETED✔️)Where stories live. Discover now